ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Tana nan zaune a bakin gadonta, tana jiran angon wanda ke can yana ganawa da bakinshi, tare da duba agogon hannunta.
Rabin awa kenan da fitar Dina, ta fada bayi ta sake sheko wanka mai suna wanka, tunda kuwa ba ta taba yin irinshi a rayuwarta ba. Ta feshe jikinta da ‘fehrenheit’ da ‘cerruti’ dinta kamar yadda ya ke a al’adarta.
Tana kokarin sanya kayan barci ya turo kofar ya shigo cikin bulalen ‘pyjamas’ yana rike da wani dan fulas mai tsananin kyau. Kunya ta kama Mairo, kamar bata taba sanin Amirun nata ba, wanda hakan ya janyo ta sanya rigar a bai-bai.
Amir ya yi murmushi, ya rausayar da kai ya iso gare ta, ya ajiye filas din hannunshi a gefe, ya dora kanshi a dogon wuyanta. At last! Sa’ar tashi ce a karo na biyu. Gashi ga Maironsa, bayan gushewar shekaru uku kwarara, cikin duniyar kuntatacciyar soyayya. Shikuwa me zai yiwa Uncle Junaidu, ya biya shi a wannan duniyar? Babu, sai adduar Alheri.
Kyawawan fuskokinsu suka zahhara cikin mudubin. Dukkansu suka saki sassanyar ajiyar zuciya mai nauyi. Wadda ke cike da godiya ga Allah!
Cancarakas! Ya dagata ita da filas din da ya shigo da shi sai ‘bed-room’ dinsu. Ya zaunar da ita a bakin gado, ya mika mata filas din, ya ce.
“Sako ne daga Nabilah, ta ce hannu-da-hannu na baki. Ya zama shi ne cimarmu a wannan daren, sai dai ban san ko mene ne a ciki ba”.
Ta soma kicin-kicin bude filas din, da kyar ta samu ta bude. Suka bi cikin filas din da kallo dukkanninsu.

“Kwadon Rama” ne wanda ya ji kuli-kuli, tumatur da albasa sai kamshi ya ke. Dariya ta kama Mairo, don ta lura Nabilah dai na son a TUNA BAYA…….. ne.
Mairo ta soma cin kwadon ramarta sosai, kunnenta kamar ya tsinke don dadi. Ta kusa cinyewa ya rike fulas din, ya rausayar da ido yana yi mata kallon nan nasa da shanyayyun idanun nan nasa, wanda ya kassara kuzarin jikinta. Ya tada wani tsohon al’amari, wanda ya riga ya shude a tsammaninta. Amir da Mairo, suka ce “Takori kauce a nan, yau bama bukatarki”.


Washegari Daddy yayi kiransu, ya danka musu ‘passport’ dinsu, mai dauke da visar kasashen duniya guda uku; Athens, Amsterdam da Pretoria. Yace da Amir yayi amfani da hutun sa na karshen shekara suje su huta tsayin watanni uku.

Mairo bata tashi dawowa ba, sai da guzurin ciki watanni biyu dan Pretoria. Bayan sun dawo ta nemi chanjin wajen aiki zuwa jami’ar Abuja, ba da son ranta ba, sai don ta samu kasancewa full-time da mijin ta. Abin son ta. Uban ‘ya’yanta kuma abin kaunarta; Dan Abdurrahman Gaya.
A shekarar ne kuma akayi bikin kaddamar da Amiru Abdurrahman matsayin gwamnan CBN, bayan gwamna mai ci a lokacin yayi ritaya. Ba don shekarun shi sun kai ba, sai don kwarewa da sanin makamar aiki da dimbin tagomashin cigaba da ya kawowa Central Bank of Nigeria a matsayinsa na tsohon ma’aikacin World Bank. Shima Uncle Junaidu ya samu ‘promotion’ zuwa ‘chancellor’ na jami’ar Bayero bakidaya. Zumunci da aminci bai taba yankewa tsakanin su ba.
Shekara na zagayowa Mairo ta direwa Hajiyar Amiru wani saitin ‘twins’ din data zabi a bawa sunan (Ilham da Sagir) kannen Uncle, don bazata taba mantawa da kaunar da Ilham ta nuna mata ba. Uncle yaji dadi kwarai kuma ya kawo Ilham daga Wales don kawai taga takwararta. Farin cikin Hajiya Aisha abin ba a cewa komai. Dina ma ta sake samun Hurairah (Hure) bayan fidda rai. Amina ta samu Atiku, Ikhlas ma matar Uncle ta sake haihuwa. To haka Nabilah duka hayayyafa suke kamar kaji, sai mu ce Allah Ya raya, kuma Allah Ya kara dankon zumunci.
MASHA ALLAHU LA-KUWWATA ILLA BILLAH…
Maman Safah da Marwah ce….ke cewa.
Sai mun hadu a sabon littafin YAKANAH cikin yardar Maiduka.
Dandano Daga Yakanah
Karfe goma sha dayan dare garin kano yayi tsit, sai iskar hunturu dake kadawa. Malam Ja’afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida. Zai gitta ta dakin Fati ya jiyo sheshshekar kukanta. Ya dakata, ya dago labulen yana kallonta.
Tana zaune akan darduma ta kunshe fuskarta cikin hijabi sai kuka take. ya karashe shigowa cikin dakin yace “Fadimatu kukan me kike yi?

A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur sun yi luhu-luhu alamar tayi kuka har ta gode Allah. 
Malam Ja’afar ya zauna a wata ‘yar kujera dake dakin yana fuskantar diyarsa. Ta share idonta da hankici, ta ja shashsheka kafin tace “Baba babu komai” ya jima yana kallonta sannan yayi murmushi yace “kina tuhumar mu dayi miki auren da baki so, auren mijin ‘yar uwar ki. Ki yi hakuri, alheri muke nufin ku da shi, ba zaki gane ba sai nan gaba. Idan kun gano gatan da muka yiwa rayuwarku” 
Fati tayi shiru tana sauraron babansu. Taga wannan itace damarta ta karshe. Daga gobe za’a zarga mata igiyoyin wanda baya sonta. Ta kai kanta kasa tana kuka sosai tace “ku yi min alfarma Baba. Baba baka taba sa ni in yi wani abu na shallake maganarka ba.

Amma a wannan karon ina so ka dubi hujjoji na. Baba. Dr Sulaiman baya so na, baba Dr. Sulaiman yafi karfi na. bani da ilimin da zan jera da shi a matsayin matarsa. Baba sulaiman bazai taba son wata ba bayan son da yake yiwa yaya Hadiza. Baba kune baku sani ba, amma Dr. sulaiman ya tsaneni ban san laifin da nayi masa ba. Ban taba gaishe shi ya amsa ba, haka bai taba kallona a matsayini jinin Hadiza ba balle yayi la’akari da wannan ya kaunace ni. In dai don ‘ya’yanshi ne, ai nima ‘ya’yana ne…zan cigaba da rike su ba sai na zama matarsa ba……”
Ya ce “Amma zaki zama matar wani ko? Kuma babu wanda zai aureki da zugar ‘ya’yan yayar ki. naji hujjojin ki Fati, amma nima ina so in tambayeki “wane abu ne Hadiza take da shi wanda ya kaita ga matakin zama matar Babban likita irin Sulaiman???? Tana ‘yar talakawa kamar ki???
Mu biyo Fati da Babanta a littafin YAKANAH yana zuwa bada jimawa ba!!!! __-_TAKORI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47

Leave a Reply

Back to top button