ABARI YA HUCE BOOK 1, 2, 3, & 4 COMPLETE HAUSA NOVEL

Nan da nan farin cikin da ke makale a fuskar Inna Hure ya yaye, Mairo ta lura da hakan, ta ce “Haba Inna, wannan ba wani abu ba ne. Zan dinga zuwa hutu kuma ana zuwa ziyara. Kin san Lanto ma ta gidan Kado tana makarantar kwana a Kwa. Duk bayan watanni uku dawowa ta ke. Sannan bayan kowanne wata ana zuwa ziyara”.
Inna ta ce “To ni wa zai kai ni birni? Har in gano ki a kowanne wata?”
Ta ce “Allah Shi zai kai ki, ga iyalin Baba Abbas za su iya raka ki”.
Nan da nan Hure ta yi kicin-kicin da fuska ta ce “Ke, raba ni da wadannan mutanen. Ni dai na yi hakuri har ki zo hutun”.
Mairo ta yi murmushi ta ce “Shi ke nan Inna”.
Malam dai jinsu yake a zuciyarshi yana mamakin dalilin Hure na kin son yin zumunci da iyalin dan uwansa. Bai sani ba ita a ra’ayinta shi ne, idan har zata ke shiga shirginsu wata rana za su sake yin yunkurin rabata da Maironta don taje tayi masu bauta amma ba don Allah ba.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, su Mairo aka kammala zana common entrace, aka zauna gida zaman jiran sakamako. Ba jimawa ya fito, shugaban makarantarsu ya mikawa Chairman. Cikin sati uku sai ga takardar daukar Maryam Bedi, cikin sabbin daliban FGGC Minjibir na shekarar.
A na so kuma ta isa makaranta cikin sati biyu, hedimasta ya kira Malam Bedi ya damka masa ya kuma gaya masa ya hadawa Mairo kayan abinci da ake hadawa dan makarantar kwana, ya kuma ba shi katifar Mairo da filo, domin makarantar ba sa bukatar akwatun karfe.
Malam Bedi ya dawo gida shi da Hure aka hau shawarar abin da za a hadawa Mairo, Hure ta daka mata kuli-kuli ta kuma shanya mata Rama mai yawan gaske, da zata dinga jikawa idan ta yi sha’awa ta kwada ta ci, kwaki kwano biyar, kanzo kwano uku, yaji rabin kwano, omon wanki da sabulun wanka. Man shafawa da man kitso, man kuli da manja. Mairo ta ce, su sayo mata brush da maclean, aka siyo a Fanshekara. Shi ke nan kaya sun hadu sai tafiya.
A daren Inna Hure ta kwaba lalle ta yaba mata a kafafunta aka daure aka kuma zura hannun dama cikin dumar lalle, shi ma kan safe ya yi jawur kamar jini, duk adon tafiya makaranta ne.
Aka tsefe kai aka yi mata kitson doka guda takwas. Babanta da Hedimasta su za su kai ta Minjibir, don haka tun karfe bakwai hedimasta ya ke buga musu zaure da yake shi ma Chairman ya cika shi da abin arziki duk don ya kula da karatun Mairo.
Mairo na kuka Innarta na yi, a haka suka rabu. Hedimasta dauke da katifar kwanan Mairo, malam Bedi rike da dindimemiyar (Ghana Must Go), a haka suka doshi tasha. Hedimasta na ce da Bedi daga wannan zuwan da zamu yi da kai, duk hutu kai kadai zaka dinga kawota, don haka ka dinga kula da duk abin da na yi”.
Malam Bedi ya ce “To, angode dai”.
Suka samu bayan motar rake suka dane, ta fito da su Fanshekara, daga nan suka hawo motar Bata/Kuroda. A nan suka hau motar Minjibir, Mairo a maleji su kuma a kujerun gaban motar. Tafiyar awanni biyu ta kawo su Minjibir, aka sauke su a tasha. Daga nan suka hau tasi aka kai su har kofar FGGC. Suka gaisa da maigadi, suka ba shi ajiyar kayan su suka karasa cikin makarantar. Jikin Mairo ya yi sanyi matuka ganin irin tsaleliyar makarantar da aka kawo ta.
Ta daga ido tana hangen dalibai cikin kayan makaranta iri daya, cikin tsari da nutsuwa. Kowacce a nutsenta ta ke tsaf, tana tafe cikin kamala. Ba ka jin hayaniyar komi sai sautin malamai suna koyarwa cikin azuzuwa, shi ma din a tausashe.
Mairo ta kalli kanta sama zuwa kasa, ta hango bambanci a farrake tsakaninta da irin jefi-jefin daliban da ta ke ganin suna wulgawa.
Gabadaya sai ta ga kanta kamar wata almajira, duk da kuwa ta kure adaka, ta sha lalle. Ga jambaki jawur ta rambada ta yi kuma jagira da digo a tsakiyar goshinta. Duk da hakan ba ta ji ko dar na zama a wannan makarantar ta yi karatu ba. Ta yi tunanin cewa, ba wannan ne abinda ya kawota ba, darasin da za a koya mata ne, Yaya Habibu ya dawo ya yi alfahari da ita.
Suka tambayi ofishin shugaba aka nuna musu. Kai tsaye can suka dosa, Mairo na kallon yadda daliban wani aji da babu malami a ciki suka yi cincirodo a taga suna kallonta. Sai hankalinta ya tashi matuka, don haka har ta riga Hedimasta tura kai ofishin shugaba, don dai ta tsira daga kallon wadannan yara.
Shugaban makarantar Halima Dukku, ta yi tsai da ranta ta cikin gilashinta tana kallon harbatsatstsiyar dalibar da aka kawo mata. Ta jinjina kai ba tare da ta tofa ba, ta karbi takardun hannun Hedimasta ta sa hannu bayan ta duba ta kuma shigar da sunan Maryam Bedi cikin jerin daliban da makarantar ta karba a wannan shekarar. Ta sa aka ba ta uniform, house-wear da sauransu. Ta kalli takalmin da ke kafar Mairo ta ga silifa ne, wani bakikkirin da shi, ya kuma hadu da wata kafa jawur kamar gauta. Ta ce ba sa ba da takalmi don haka aje a sayo mata sandal ko cambus.
Hedimasta ya ce su yi masa alfarma ya bada kudin a siya mata, su baki ne a garin ba su san ko ina ba. Ta kira leburanta, ta hadasu dashi, ya gaya masa sandal dari takwas ne, kambas dubu daya da dari biyar mai saukin kudin kenan. Gabadayan su shi da Malam Bedi suka hada baki suka ce, “Mai ka ce?”
Ya sake maimaitawa. Malam Bedi ya hau salati amma shi Hedimasta da yake da dan karatunsa na yaki da jahilci sai ya ce”Au to, ba mu sani ba ne, domin yanzu a aljihuna kwata-kwata naira dari hudu ne, ga shi a ciki zamu hau mota. Amma ga wannan”. Ya mika masa dari biyu, ya ce, “Ko irin na dankon nan ne mai igiya a saya mata idan zata dawo sai a nemo”.
Haushi ya ishi leburan ya juya zai fita abinsa, shugaba ta yi gyaran murya ta dauko gudar naira dari biyar guda hudu ta mika masa, ba tare da ta ce komi ba.
Malam Bedi ya dinga zuba mata godiya, ta ce, “Babu komi, ai da na kowa ne”. Ta sa aka kira mata wata prefect ta hadata da Mairo da kayanta gami da littattafai wadanda suke cikin kudin makarantarta, amma babu jaka, ta ce su sayo mata daga baya, ta ce ta kai ta hostel.
Sai a lokacin ne kuka ya zo wa Mairo, shi ma Malam Bedi duk da dauriyarsa sai da ya sa habar babbar rigarsa yana share hawaye. Suna dagawa juna hannu har su Mairo suka kule cikin hostel.
Bayan prefect din nan ta damka Mairo a hannun house-captain dinsu sai ta koma aji. House-captain ta nunawa Mairo dakinsu ta ba ta gado ta shimfida katifarta ta ce, to ta sanya uniform ta tafi aji don kowa yana aji. Sai dai fa a ranta tana mamakin yadda aka yi wannan bakauya ta zo makarantarsu.
Mairo ta tube kayanta ta sanya na makaranta ta bi bayan captain har ajin da aka ba ta, wato JSS 1A. Ta je staff room ta nemo class master dinsu ta hada shi da Mairo, ta koma nasu ajin.
Mairo ta yi tsuru a gaban allo, a lokacin da Uncle ke gabatar da ita a matsayin sabuwar daliba a ajin. Abin da Mairo ta lura da shi shine, gabadaya ‘yan ajin wani irin kallo suke mata na raini da kyama, suna kyabe baki duk sai ta ji ta muzanta.
Uncle ya nuna mata kujerar zama gefen wasu fararen yara ‘yan gayu guda biyu, da ba su fice tsaranta ba. Ai kuwa suka soma matsawa jikin junansu suka takure suka ba ta katon fili.
Malamin ya lura da irin karbar da Mairo ta samu a ajinsa, duk sai ya ji tausayinta ya kama shi. Ya dube ta ya ce, “Sake gaya min sunanki, ban gane abin da principal ta rubuta sosai ba”.
A hankali ta bude dan kankanin bakinta ta ce
“Maryam Bedi”.
Ya ce “What a nice name, maryama, saki jikinki ki zauna a inda na umarce ki. Ba ruwanki da kowa sai abin da ya kawo ki, kina ji na?”
Ta gyada kai, amma ba ta amsa ba.
Ta karasa inda ya nuna mata ta zauna a darare. Yarinyar kusa da ita ta ja tsaki, tsuuu! Ta murguda baki ta juya mata keya. Ta dauki tulin littattafanta ta zura su cikin lokar kujerarta tunda ba ta da jaka.
Uncle ya fita cike da tunanin wannan yarinya. Yana daga cikin malaman da ba sa son ganin rashin walwala ko yaya daga dalibansu. Abin da ya lura shi ne, Maryama ta shigo makarantar da ta fi karfinta. Ya fi kowa sanin girman kai da ji da kai na daliban FGGC don haka ya samu kansa da tausayin ‘yar yarinya, Maryama.
Ya alkawarta wa ransa taimaka mata iyakar iyawarsa, har sai ya ga ta saki jikinta tamkar sauran dalibai ‘yan uwanta.
Da aka tashi daga aji Mairo ba ta san dawar garin ba. Ta dai ga kowa na fita da littattafansa babu wanda ya kulata, kai ba ta ma ishi kowa a ajin kallo ba. Sai ta kwaikwayi yadda suka yi, wato ta kwaso littattafanta masu yawa da matukar nauyi ta nufi hostel kamar yadda ta ga sun yi.
Tana shiga dakin sai ta ga wadannan fararen yaran sun rigata isa har sun tube uniform sun sa na hostel, ashe su ma a dakin suke. Suna ganinta ta shigo suka kara yin kicin-kicin da fuska kamar an aiko musu da sakon mutuwa, musamman da suka fahimci a kusa da gadonsu ta ke.
Dayar ta yi tsaki ta canza harshe tana cewa da kawarta, “See this girl, i donno what she is looking for here…”(kalli wannan yarinyar bansan me take nema a nan ba).
Kawar ta ce, “Kaddararmu ke nan, daki daya, aji daya, mts!”