BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsaki tasaki tace “tun yaushe wani tsinanne yata6a? Ai bazan taba yafe wa Aryan ba, inda ace Babban Yaya yaji, nasan kasheni kawai zaiyi”
Zulaihat tace “wani term din kawai kibar Dakin kidawo namu, qaro mana abincin Dan nikam ban qoshi ba, banaso yunwa ta kamani narame”
Waheeda tace “to waye yace miki cin abinci ne takesa mutum qiba? Ai kwanciyar Hankali ne”
Zulaihat tace “to idan bancin ba tayaya Hankali na zai kwanta?”
Haka suka gama firarsu da yamma sukai class
Washe gari suna aji babu malami a ajin, ta hango wata malamar hausa, yar Gayu ce malamar tanata taku daidai, Waheeda ta daga murya tace “Wanka yabi jiki malama”
Cikin sauri malamar tajuyo tace “me kikace?”
Waheeda tace “wanka yabi jiki”
Bulala ce a hannun malamar aikuwa ta Juyo tashiga ajin saida tayiwa Waheeda Bulala shida, Ana gama mata Bulalar takade hannunta tace “aibaki birgeni ba tunda baki kasheni kinkaiwa su Babban Yaya gawata ba”
Malamar ta kalleta tayi qwafa tafice daga ajin
Ita Kuma Waheeda Takoma ta zauna,6acin rai ne yasa malamar tatafi staff room ta fadawa sauran malamai, anan kowanne malami yake fadar irin rashin jin datake masa, malamin Qur’an ne kawai bata masa ba
Shima period dinsa tana shiga, yazo ajin yafara biya musu Qur’an suna karanta wa, Waheeda tafara surutu ahankali yana ganin ta ya shareta, dataga bai dauki mataki akan ta ba kawai saitaci gaba da surutun ta, saboda already tariga ta’iya wajan tun a islamiya, tsayawa yayi da karatun yace “inada wani uzuri yanzu, next week zan dawo muci gaba” yana fadar haka yafita daga ajin, yaga alama yarinyar bataji, idan yayi mata magana Kuma zata Iya masa rashin kunya agaban sauran Yara, Kuma hakan babu dadi, danhaka ya haqura dabiya musu karatun yafita ☹ï¸
Da yamma suna hostel yau labour day ne, kowa share share yake makarantar tayi tsaf
wata yarinya ce yar js1 ta kawo mata wasiqa, tana dubawa taga qawar Rabi’at ce ta aiko mata wasiqa tana sonta, yaga wasiqar tayi a wajan, tayi wani irin tsaki
Haka Nan taji gaba daya makarantar tafita daga ranta, kullum addu’arta daya Allah yasa su Babban Yaya sudena cin qwallo,😅 Jira take gari ya waye ta kira Ummah a wayar wani malamin ta fada mata abinda yake damunta
Da daddare tana bacci cikin dare taji kamar Ana shafa mata wuya, tayi juyi tasake shigewa cikin Bargo, taci gaba da bacci can taji anriqe mata nipples dinta Ana murzawa, gabantane yafadi tabige hannun tatashi cikin sauri tana dube dube, Dakin duhu qirin babu abinda take Gani, jikinta tafara ta6awa sannan tayi addu’ah Takoma ta kwanta, bacci me dadi yafara daukarta taji an toshe mata hanci da baki andanneta Ana matsa mata qirjinta, kokawa tafara Amma babu riba saboda mutum biyu ne, tanajin yanda aka cire mata Riga Sai murza mata nipples dinta ake kamar za’a cire mata su,kuka tasa tana motsi tana so ta qwace jikinta Amma takasa, Sai hawaye take babu damar numfashi babu damar magana, jitayi kwata kwata bata numfashi kamar zata mutu, ba tasan lokacin da tasa qafarta tahauri wata aciki ba, anan tayi nasarar qwace Boobs dinta daga hannun su, tana jin ansaki bakinta takurma wani uban ihu, aikuwa Yan dakinsu suka tashi, masu a’uziyya nayi masu kunna torch light nayi, daki ya dauki hayaniya, kowa yazo kanta yana tambaya menene, kasa magana tayi Sai zare idonta take tana Kalle Kalle, tahade jikinta waje daya, bata samu damar rera kuka Bama saide hawaye 😥
A Daren, kasa komawa tayi ta kwanta, takuma sa a ranta tabar wannan Dakin daga yau, dakinsu Neenah zata koma, da safe kasa saka brezia tayi, saboda gaba daya kan nonon ciwo suke mata, jitake kamar ta ciresu ta jefar, gashi babu Ummah akusa, babu yanbiyu bare ta fada musu ko zataji dadi, haka tafita aji babu brezia Amma tasaka hannunta acikin hijabi babu Wanda zai gane
Period din farko malamin qur’an yashigo ajin, yana ganin Waheeda gabansa yafadi, fatansa daya Allah yasa su wanye lafiya, yana biya musu, Bayan kowa ya karanta saiyace “akaranta mutum d’aid’ai”
Layin farko sun fara biyawa, Waheeda takasa nutsuwa saida tafara yiwa Neenah magana akan abinda aka mata daran yau, tace “Neenah, yau dakinku zan dawo, jiya bakiji yanda akamin ba, aka kama kan Nono na aka riqe kamar za’a cire, har yanzu zafi nakeji yanda kikasan namutu wallahi, Kuma Ina tunanin su Rabi’at ne itada qawarta, saboda jiya da yamma qawartata har wasiqa ta aikomin tana sona, Kuma….”
Kafin ta qarasa magana,ya mu’allim yace “ke…”
Wata daga cikin yaran tajuyo ta kalli su Waheeda tace “Virus Ana magana”
Waheeda tace “au Dani yake? Bansani Bama saboda ba daidai nakeba yau”
Kallan ta yayi yace “ke futo Nan”
Babu musu tafuto, ya dauki dorinar dake gefensa yafara tsula mata ajikinta, gashi jiki babu vest bare taji sauqin saukar bulala🤣, tun tana mazewa harta dawo tana kuka,haquri tafara bashi Amma ya mu’allim Sai dukanta yake, data gaji da shan azaba kawai saita tashi tayi masa ta Babban Yaya, ta cacimeshi ta rungume shi,🙆ðŸ»â€â™€ï¸?
Aji aka dauki ihu, wasu daga cikin su suna cewa “Virus mu’allim ne”
Sai ihu suke, mu’allim yayi azama yacireta daga jikinsa yatafi staff room ransa abace, yana zuwa yasamu principal cikin fishi yace “ranka yadade daga yau nayi resigned, nabar makarantar Nan, harni da girmana da komai yarinyar Nan zata rungume ni?”
“wacce yarinya?” cewar principal
“yarinyar Nan marar kunya mana Waheeda Virus, gaba daya ta addabi kowa,last week Ina karatu tanamin surutu a aji, ta ganni mun hada ido Amma taci gaba da surutu, to bazan iyaba, saide ku za6a koni ko ita”
Principal yace Akira masa Waheeda, tana zuwa ta tsugunna agaban sa tace “Gani sir”
Yace “Waheeda Yaya akai kika rungume ya mu’allim a aji? Kinada Hankali kuwa?”
Hawayene ya silalo daga idonta tace “sir, dukana yayi, naji zafine sosai bansan na riqeshi ba”
Principal ya kalli ya mu’allim yace “tokaji abinda tace, kaikuma metayi har akai mata irin wannan Dukan dahar yarinya zata kasa sanin ta rungume malami?”
Ya mu’allim yace “surutu take muna karatun alqur’ani”
Principal ya kalli Waheeda yace “meyasa kikai masa surutu yana aji, bakisan girman malamin ki bane?”
Idonta ta goge tace “Sir jiyane da daddare Ina bacci ake ta6amin qirjina, shine nake Bawa Neenah labari a aji, shine ya ganni yace nafuto, Ina futowa Sai ya kama dukana”
Gaba daya malam wajan ne suka hada baki tareda tafa hannu suna fadin “la’ilaha illallah…..”
Principal yazaro ido😳yace “aka ta6a miki me? Waheeda har sharrin naki yakai haka? Acikin makaranta ta ake aikata wannan ta’asar? To Bari kiji, saboda ke bazan yarda malami ya ajiye aikinsa ba, hakan bai isheki ba saikin hada kinyiwa dalibaina sharri, malamai sun gama complain akan ki bakya jin magana kwata kwata, saboda haka kitafi gidanku Sai iyayenki sunzo “🙆ðŸ»â€â™€ï¸?
Waheeda tayi shiru tana nazarin maganar sa,gaba dayama satinta uku acikin karantar mezatacewa su Ummah agida idan suka ganta tadawo gida yau? Mezasu fadawa Babban Yaya? Bata gama tunani ba taji principal yace Akira masa mama mairo, matar datake kula dasu a hostel
Mama mairo tana zuwa, yace “ga kudin mota Nan, kidauki wannan yarinyar, da duk kayanta, kikai ta gaban iyayenta kifada musu hukumar makaranta tace akawota gida Sai iyayenta sunzo”