BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama mairo tacika umarnin principal, akaje aka debo kayan Waheeda, suka kama hanyar garinsu

itace ta dinga nuna mata hanya har suka qaraso get din gidan, karfe goma shadaya daidai agida tamusu

Ummah tana kitchen tana kokarin Dora abincin rana saboda yanbiyu suna makaranta, saiji tayi anfado jikinta Ana kuka

Dafarko tsorata Ummah tayi, saboda tasan cewa ita kadai ce a gidan, tana juyowa taga Waheeda duk tayi baqi, cikin tsananin mamaki tace “Waheeda?!!!” 😱

Amnah El Yaqoub ✍�
1/28/22, 20:49 – Ummi Tandama😇: BABBAN YAYA

Writing By Amnah El Yaqoub

Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/

7&8

Mama Mairo taqaraso kitchen din itama “Hajiya Ina kwananmu?”

Ummah tasaki Waheeda ta kalli matar, ta manyan ta sosai, aqallah zatayi shekara hamsin dawani abu, tace “Sannu baiwar Allah, mu qarasa falo mana”

Falo suka dawo suka zauna, Ummah ta nufi fridge zata kawo mata ruwa da lemo, mama mairo Sai jinjina Kai take tana qarewa falon nasu kallo, idan banda abu irinna iyayen wannan yarinya mezaisa ‘yarsu tana rayuwa acikin wannan daula zasu dauketa su kaita boarding? Gashi Ana nema a lalata yarinya, koda yake kowa da halinsa

Ummah tadawo ta zauna tabud’e lemon ta zubawa mama mairo tana cewa “ga lemo Kisha mama, meyake faruwa ne Naga Autata agida? Wani laifin ta aikata ko?”

Mama mairo ta ajiye cup din hannunta Bayan tagama shan lemon tace “hajiya kinsan sha’anin Yara Sai hakuri,hukumar makaranta ce tace a dawo da’ita gida Sai iyayenta sunje”

Ummah ta dauki waya tana fadin “subhanallah, Bari nakira Yayansu”

Gaban Waheeda yafadi, tasan cewa inde yaji ankorota tabbas zai dawo qasar Nan, Kuma yayi mata gargadi karta yarda ya dawo qasar Nan saboda ita, saboda Dama can matsalar tane yake sakawa ya dawo, shide akaran Kansa yana dadewa kafin yazo gida, saboda yasan indai ya dawo to maganar aure zasu masa, cikin sauri ta riqe hannun Ummah tace “Ummah Dan girman Allah karki kirashi, kibar Yaya Sa’ad da Yaya Sa’eed sumin komai, Dan Allah Ummah kirufamin asiri kar Babban Yaya yaji”

Ummah tazuba mata ido tana Kallan ta, tunda taga haka tasan cewa to Waheeda ta yi wani laifin ne, tace “saina kirashi Waheeda, shine daidai dake tunda ba zakiyi Hankali ba, Anya ma kuwa kina wanka Waheeda? Sati uku da tafiyar ki duk kinyi baqi kamar baki ta6a ganin ruwa ba?” 🤔

Mama mairo tayi murmushi tace “Hajiya Bari nawuce kar rana tayi”

Ummah tace “Ina zuwa mama”
tashiga daki takawowa mama Mairo kudi dakuma turamen atamfa guda uku, cikin murna mama mairo takar6a tayi godia tayi musu sallama sannan tatafi Sai yabawa tsarin gidan nasu take

Ummah ta zauna a kujera, tana zama Waheeda tadawo jikinta ta maqalqaleta,jitake kamar za’a sake maidata wannan makarantar, kwata kwata batajin dadi, Kuma batajin zata sake komawa saide tagudu ranar da’aka ce za’a maidata
Ummah tace “Waheeda, kifadamin abinda kikayi aka koroki, rashin kunyar kika sake musu ko?”

Kuka ta Fashe dashi,takasa magana, Ummah tazuba mata ido tace “ikon Allah, bazaki min magana ba kin tsaya kina kuka?”

Cikin kuka tace “Ummah Dan Allah karku maidani, please karki fadawa Babban Yaya”

Ummah tayi shiru batace da’ita komai ba, tasake daukar wayar ta tayi dialing number Naufal, har wayar tagama ringing ta katse bai dauka ba, Sai daga baya yakirata, Ummah ta dauka tace “Yayansu toga Waheeda Nan andawo da’ita gida, sunce Sai iyayenta sunje”

“what?” abinda yace kenan

Ummah tace “to haka de matar data rakota tace, hukumar makaranta sunce akawota gida Sai iyaye sunje”

Shiru yayi yakasa cewa komai, itama Ummah tayi shiru, tayi tunanin ma bazai ce komai ba Sai can taji yace “Bata wayar”

Umma ta miqawa Waheeda waya tace “ga waya inji yayanku”

Cikin kuka tace “Ummah Allah Zagina zaiyi” tatashi tashige dakinsu da gudu cikin kuka

Ummah ta maida wayar kunnanta tace “to taqi kar6a,Kuma Nima taqimin bayanin abinda tayi, matar data kawota Kuma tatafi, itama bata tsaya tamin bayani cikakke ba, Kuma tunda kaga ta 6oye ai kasan laifin Waheeda ne”

“Allah yarufa asiri” abinda yace kenan

Ummah tace “Amin” tareda kashe wayar, tasan dole zaizo, Kuma zai dauki mataki akan haka

Waheeda saita taji Ummah tadena wayar sannan tadawo falon, Ummah ta kalleta tace “saikije kicire kayan ai, kiyi wanka, nasan bakya wanka Waheeda”

dariya ce ta kamata, tayi murmushi ta wuce dakinsu, wanka tayi sosai, sannan ta kwanta bacci, bata tashi ba Sai daya saura, tana futowa falo taga Ummah tana waya da Hajiya Anty, tana fada mata Waheeda tayi Hali andawo da’ita gida 😂

Kitchen ta wuce ta yanka salat, tafuto falo zata hada taci, yanbiyu sukai sallama, suna ganin Waheeda suka saki ihu, suka rungume juna

Ummah ta Kalle su tayi murmushi tace “yauga wasu irin yayu, kunganta agida bazaku tambayi dalili ba kawai saide kuhau ihun murna?”

Babu Wanda yabawa Ummah amsa, duk sun riqe Waheeda suna murna, Ihsan tace “Waheeda kinga yanda kikai baqi? Ko wahala kikesha?infada miki Waheeda tunda kika Dena zuwa makaranta qawarki Maya tazama shiru shiru, abun tausayi kamar anmata mutuwa, saide tazo wajanmu ta zauna”

Waheeda tace “hmm kede Bari kawai Ihsan, Nima nayi missed dinku,boarding babu dadi”

Intisar ta kalli salat din dake gaban Waheeda tace “to aqara yanka wani tumatir din mana”

Waheeda tasake yanka tumatir taja flet din gabanta zata fara Ci, suma suka matso, wani irin kallo tamusu ta kalli Intisar tace “waida harda ku kike nufi?”

Basu kulata ba suka fara ci, ganin haka yasa itama kawai ta sharesu sukaci salat din gaba dayansu

Wunin ranar, haka su Waheeda sukayi shi cikin marmarin juna, babu fada, sun had’e kansu, Sai labarin makaranta take basu kamar basune kullum cikin fada ba.

Kwananta uku agida, Babban Yaya yazo, wannan Karon zuwan dare yayi, shiyasa baisamu cikowar mutane sosai ba, wayar Ummah ce a hannun Waheeda tana yin game, su yanbiyu suna ta Bawa Ummah labarin qawayensu, Sa’ad da Sa’eed suna dinning suna dinner, cikin falon yashigo bakinsa d’aukeda sallama, yana Sanye cikin qananun Kaya dasuka kar6i jikinsa, lokaci daya qamshin turaren sa yacika falon, Waheeda tadago kanta sukai ido biyu dashi, yasaka p-cap yasaka facemask, dakuma wani glass Jan duhu, kwata kwata idan a hanya kuka hadu ba zakace shine ba, ya 6oye kamar sa ne saboda kar mutane su ganeshi suhanashi tafiya, shikuma yagaji sosai hutu yake buqata, ko awanne Hali yake ciki Waheeda zata ganeshi,duk da ya6ata mata rai ya kaita boarding bata jin zata Iya fishi dashi, tanajin sa sosai acikin ranta, ta dauke shi tamkar aboki kokuma wani Amini Nata na daban,yanada mutuqar muhimmanci acikin rayuwar ta

Ahankali ta ajiye wayar Ummah agefenta, cikin dakiya tanufeshi tace “Babban Yaya sannu da zuwa”

Tayi maganar tana qasa da fuskarta, Dan tayi tunanin zataji saukar Mari, Amma ga mamakin ta saiyace “Yauwa”

Yabata wata leda me kyau tareda nuna mata yanbiyu yace “kibasu”

Juyawa tayi cikin ladabi, tabawa yanbiyu ledar tana jira su bude taga menene aciki, suna budewa kuwa sukaga Kayane English wears masu kyau riga da siket, komai iri daya babu banbanci a kayan, murna sukai hauyi kamar qananun Yara, Waheeda tacika tayi fam, Takoma Gefe ta zauna 🤣

Babban Yaya ya qarasa wajan Ummah yazauna,tareda Dora Kansa akan kafadarta, Ummah ta Kalle shi tace “ya Hanya?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button