BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kafin yabata amsa su Sa’ad su kazo wajan sa suka zauna, suna masa sannu da zuwa, sumar Kansa ya shafa Bayan ya amsa musu ya kalli Ummah yace “Ummah nagaji wallahi, bacci nakeji”

“to meyasa kataho da daddare? Dakayi zamanka da safe kataho”

Cikin shagwaba yace “Ummah sonake naganki wallahi”

“yau Kuma shagwabar ce tatashi?” cewar Ummah

Dariya yayi, dimples dinsa suka futo, yace “Ummah, yarinyar can ta fada miki abinda yasa suka dawo da’ita gida?”

Ummah ta juya ta kalli Waheeda taga Sai fishi take, tace “gatanan ka tambayeta ko zata fadama, nide ba tacemin komai ba”

Fuskarsa ya daure yace “babu abinda zan tambayeta Ummah, ta shirya kawai gobe zan maidata da kaina, nakira principal din but bai dauki wayata ba”

Ummah ta kalli Waheeda tace “kinji meya ce ai ko? To saiki shirya”

Babu musu Waheeda tace “to Ummah Allah yakaimu” Amma cikin ranta tariga tagama shirya yanda zata gudu tabar gidan, bazata dawo ba Saitaji labarin Babban Yaya yakoma

Tashi yayi zai wuce dakinsa,cikin shagwa6a Waheeda tace “Babban Yaya Toni Ina nawa kayan?”

Juyo wa yayi ya kalleta,yaso Ummah bata Nan dasai yadaki yarinyar Nan, to babu halin duka yanzu, tunda Ummah tamasa fada last time cewa ya dinga jansu ajikinsa, saida ya daure sannan yace “bakiga iri d’ayane kayan ba? Ke yanbiyu ce? Suma nagani ne Kuma su kenan qwaya biyu, shiyasa na Dauko musu”

Tace “to nifa?”

“kiduba irin Wanda kike so” yana fad’a mata haka ya wuce d’akinsa, Ummah ta kalleta tace “tashi ki had’a abinci kikai masa”

Babu musu Waheeda ta nufi kitchen cikin farinciki batare da damuwar komai ba,Dama Babban Yaya takeji, Kuma taga alamun bazai daketa ba

Sosai ta nutsu wajan had’a masa abincin, yanda take had’a komai cikin tsafta zaka iya rantse wa mijinta take hadawa abincin, d’auka tayi ta nufi d’akin nasa, daga bakin kofa ta tsaya tayi masa nocking, saida ta dade a tsaye sannan yazo ya bude mata ‘kofar, saura kadan tasaki tiren dake hannunta, sakamakon yanayin data ganshi, dagashi Sai wani Dan gajeran wando, da alama ma wanka zai shiga, gabanta yake faduwa ahankali, cikin nutsuwa ta qarasa gabansa tayi azamar ajiye abincin saboda hannunta rawa yake tsaf zata Iya zubarwa, tarasa meyasa Babban Yaya yake abinda yakeso agaban ta, kwata kwata bayajin kunyar cire Kaya agaban ta, bayajin kunyar su zauna tareda ita dagashi Sai towel din wanka, tasan inda yanbiyu ne cewa zaiyi raina shi zasuyi idan suka ganshi Ahaka, to meyasa ita yake mata haka? Wata zuciyar tace da’ita, may be Dan kun shaqu ne, tunda yana iya hira dake Amma ba yayi da Yanbiyu, ajiyar zuciya ta sauke tafara zuba masa abincin, saida tagama sannan tanemi waje ta zauna, Kallan ta yayi yace “Lafiya?”

“Babban Yaya Dan Allah kayi hakuri” tafad’i haka hawaye yana silalo wa daga idanunta

“laifin me kika aikata dazaki Bani hakuri?”

“Babban Yaya nasan na takura ma, wallahi Nima ba laifi na bane, yarinyata ce take damuna kawai” 😥

Yace “are you serious?, 18 yrs Amma kina cewa yarinta ce take damunki, me kikayi a school din suka koreki?”

Shiru Waheeda tayi, tayaya zata masa bayani? Ce masa zatayi tana yiwa malaman makarantar rashin kunya kokuma dayan maganar zata fada masa? Tayaya zata Iya fada masa magana me nauyi irin haka? Yayanta uwa d’aya uba d’aya shi zata kalla tace wasu suna ta6a mata nonuwa Aida kunya

Hawaye ne suka zubo daga idonta, tasaka hannu ta share tace “kayi Hakuri Babban Yaya”

Kallan ta yayi cikeda mamaki, kawai daga tambaya Sai kuka? Ajiyar zuciya yayi yace “shikkenan, tunda haka kika za6awa rayuwar ki, kina ganin yan’uwanki, banta6a zuwa gida ta dalilin matsalar suba, koda yaushe kece sanadin zuwana, Kuma tunda kika girma kikai wayo babu ranar farinciki dakikamin sanadin zuwanta, kullum matsalar kice takesa nabar aikin danake nazo, kwata kwata bakya tausayi na kamar sauran yan’uwanki,duk zuwan da zanyi Sai iyayena sunmin maganar aure, Bayan kinsan banaso,to saboda me danna Sai musu Kaya zakiyi fishi “

Kanta aqasa tace” kayi hakuri Babban Yaya”

Yace “hmm kamar gaske, Bani abinci na kitashi kitafi”

Abincin tabashi, Amma takasa hada ido dashi, kar6a yayi yafara ci ahankali kamar yaro qarami Wanda baisan abinci, d’agowa tayi ta Kalle shi, ahankali tatashi tahau kan gadon, ta zauna dab dashi, spoon din hannun sa tariqe, ya kalli yanda tariqe masa spoon din yace “miye haka?”

Cikin shagwa6a tace “to Babban Yaya bakacin abincin fa sosai” wani irin abu yaji tundaga Kansa har zuwa tafin qafarsa,kamar bashi ba, Sai gashi ya gagara yimata musu, sakar mata spoon din yayi, tafara bashi abincin yanaci,Kallan ta yake yana mamakin yanda tayi kama dashi sosai, komai nashi ta Dauko, babu wani qarin bayani idan kaganta ka ganshi kasan cewa jini daya ne.

Yace “kishirya da wuri gobe”

Maimakon tabashi amsa Sai tace “Babban Yaya induba rigar danake so a internet saina kawo ma kagani?”

Yace “kiduba”

Mamaki yahanashi kasa yimata wata maganar ta makaranta, tunda yaga alamun akwai abinda take 6oye masa

Saida tagama bashi abincin haryana mamakin yawan abincin dayaci,fita tayi da kwanukan, shikam toilet yashiga yayi wanka,yayi sallolinsa, sannan ya kwanta

Waheeda kuwa wayar Ummah ta d’auka tabud’e data, daga Nan tashige dakinsu tafara browsing din rigar datake so, Sai wajan shadaya nadare taga rigar, da’inda zaka tura musu kudin su aikoma da rigar,Hankalinta yanakan wayar tace “Ihsan Dan Allah kalli rigar Nan batayi kyau ba?”

Taji Ihsan tayi shiru babu amsa, tana juyawa taga duk sunyi bacci ita kadai suka Bari, tashinta ta farayi tace “Ihsan, Ihsan tashi kigani”

Ihsan tabude idonta ahankali cikin bacci ta kalli photon rigar, ta kalli Waheeda, tace “wannan yar’iskar rigar duk nonuwa awaje zaki nuna masa? Shi Babban Yayan mahaukaci ne zai siya miki irinta?” taja tsaki Takoma baccin ta

Waheeda tace “to ai saiki hanashi siya”

Takoma wajan intisar tafara tashinta, Bayanta tafara duka tace “inti, kinga rigar danake so Babban Yaya yasiyo min, tayi kyau ko?”

Intisar tabude idonta tace “waike Waheeda Dalla Sai mutum yana bacci kibi kidameshi”

Waheeda tace “maida wuqar, niba masifa ce ta kawo ni ba, duba rigar kigani”
tsaki intisar taja sannan ta kar6i wayar ta kalli rigar tace”waheeda bakida Hankali riqe wayar Nan Dan Allah “

Fizge wayar tayi tafice daga Dakin ta nufi Dakin Babban Yaya, zuciyarta d’aya tatura kofar Dakin tashiga, duhu ya mamaye ko’ina, Sai sanyin esi dake ratsa ko’ina acikin Dakin, Lumshe idonta tayi sakamakon qamshin data shaqa me dadi, fitilar wayar ta kunna, ta qarasa gadon, ta zauna adede Kansa tana qare masa kallo, Babban Yaya yahadu sosai, babu macen da zata qi yayanta, tarasa meyasa yake gudun aure? Inama ace Allah zai bata Miji, Mai kamar yayan Nata, ta tabbatar datafi sauran mata sa’ah,baccin sa yake Hankali kwance, duk wannan sanyin esin dayake ratsa Dakin shikam babu riga ajikinsa, gajeren wando ne ajikinsa Amma ba Wanda ta ganshi dashi dazu bane, ya sauya wani.
ajiyar zuciya tayi, sannan tafara bubbuga Fillon daya d’ora Kansa tace “Babban Yaya, Babban Yaya ga photon rigar nakawo”

Cikin baccin sa yaji kamar a mafarki Ana Kiran sunansa, hannunsa yasa ya fuzgo ta tafad’o Kansa, wayar Ummah dake hannunta tafad’i can Gefe kan kafet d’in dake malale atsakar ‘Dakin nasa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button