BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

“jiya nazo Anty, nazo na maida Waheeda school, sannan Baba Habu yamin waya naje Naga yar abokin Uncle, Wai Nadiya”

“aiya wuce ‘Wai’ Naufal, Nima nasan yarinyar tun tana qarama, nasan wannan Karan insha Allah baza’a samu matsala ba, mun kusa shan biki” ta qarasa maganar cikin murmushi

Ajiyar zuciya yayi yace “Anty kenan, ni yanzu babu wacce nakeso, Kuma bazan iya auren yarinyar da banaso ba, maganar gaskiya kenan, idan kema kin gaji da ganina haka saiki Bani ‘yarki” (tofa)

Kallan sa tayi, jikinta yayi Sanyi, hannun sa takama ta riqe tace “inda ace na Haifa ai zan baka Naufal, ka daure kaje kaga Nadiya, insha Allah zata Maka”

Yace “to Anty insha Allah anjima da yamma zanje”

Tare suka futo daga gidan, saida yaga tashiga motar ta tafita, sannan ya qarasa wajan Maigadin gidan, sallama yayi masa, Baba yusha’u yace “Yalla6ai ko akwai abinda kake buqata?”

“kayanka nakeso kabani Baba, zanyi amfani dasu”

“kayana Kuma Yalla6ai,kaida kanka? lafiya dai ko?”

Murmushi yayi yace “karka damu baba, nine zanyi amfani dashi, kahada mun harda wayar ka”

Jiki na rawa Baba yusha’u ya ‘Dauko masa kayan, tareda wayar “

Ya kalli kayan yaga sunyi yanda yakeso, sannan ya kalli Baba yusha’u yace” Baba wannan wayar ai kalau take, babu wadda tafita tsufa? “

Baba yusha’u yace” eto, saide wata tsohuwar wayata data lalace idan aka kirani banaji Kuma ba’a Jina, Kuma murfin wayar baya zama da kyauro nasa nariqeta, kafin hajiya ta sauya min wannan “🤣

Babban Yaya yace
“yawwa, Bani ita”

Baba yusha’u ya Dauko yabashi, yakar6i kayan yajuya yashiga motarsa sannan yabar gidan

Kai tsaye Gida yakoma, yabar kayan acikin motarsa, yanbiyu da Waheeda suna falo sunacin abinci, Ummah tayi masa sannu da zuwa tana Bawa yanbiyu magani, zama yayi a kujerar yace “Ummah wace ba lafiya Kuma?”

Yanbiyu ta nuna masa tace “gasunan, kasan halin jinyarsu ai, idan daya tafara dayar ma Saitayi, Wai cikin su ne yake ciwo”

“ok Allah yasawaqe”

Ya kalli Waheeda yace “ki gama nakai ki islamiya tunda su babu lafiya”

Ranta ne ya6aci cikin shagwa6a tace “to Babban Yaya subazasujeba saini kadai? Lafiyarsu kalau wallahi, tsabar sharri ne kawai”

Wani irin kallo yamata, Nan take tayi shiru ko qwaqwqwaran motsi bata sake yiba

Dinning ya nufa da Kansa, yazuba abincin yanaci yana Kallan TV sama sama, har Waheeda tagama taje daki tafuto cikin shirin islamiya, ta kalli Ummah tace “Ummah zan tafi, saimu dawo tareda Maya, tunda yanbiyu bazasuje ba yau”

Ummah tace “saikun dawo”

Tashi yayi zai fita, ya kalli Ummah yace “Ummah naje gidansu Nadiya”

Murmushi Ummah tayi tace “Aida kabari Sai gobe, yanzu Naga alamun Garin akwai hadari, Amma idan kaje gobe zakufi sakewa ku Tattauna”

Yace “no,Ummah zanyi sauri naje insha Allah”

Cikin farinciki tace “to a dawo lafiya, ka kula da kanka”

Waheeda tace “to Ummah karki damu Nima zan kula dashi”

Ummah tace “Allah ya shiryeki Waheeda”

Waheeda tashiga gidan gaba taja murfin motar tarufe, tajuyo taga Babban Yaya yana Kallan ta, idanunta tajuya tace “Babban Yaya lafiya?”

“meyasa kikasa Ribom a kanki?”

Dariya tayi tace “laaa Babban Yaya bafa Ribom bane”

Muryarsa ya rage kamar yana tsoron wani yaji sannan yace “qarya kike yi, to mugani”

Hannu tasa tajanye hijabin daga kanta, dogon gashinta Mai tsantsi ya baiyana, ta dago tana Kallan sa tace “kagani?”

Ahankali yakai hannunsa kan gashi Nata, ya gyara matashi, sannan yace “nagani, mayarda hijabin”

Kallansa tayi tace “Babban Yaya idan baka so nadinga acuci da gashina kabani kudin kitso”

Kafadarsa yadaga yace “no, karkiyi kitso, kibarshi haka yafi”

Babu musu tace masa “to, mutafi karna makara”

Gyara zama yayi yace “kinsan de Banason aure yanzu ko?”

Mamaki yakama Waheeda, takasa magana saita gyada masa Kai kawai, ajiyar zuciya ya sauke, yakai hannun sa Mai laushi yakamo Nata hannayen yace “su Baba Habu sun hadani da wata yarinya Nadiya, idan na saukeki a islamiya wajan ta zanje yanzu, inaso na gwada sa’a ta ko Allah zaisa narabu da’ita”

Waheeda ta kalli qwayar idonsa, tana so ta tambayeshi abinda yadade Yana yawo a ranta, Amma tana tsoro karya mata fada, dakewa tayi, tayi jarumtar cewa “to Babban Yaya meyasa baka son auren? Sune baka so kokuma auren ne duka baka so?”

Kai tsaye yace “sune banaso”

Cikin mamaki tace “towa kake so?”

Kallan manyan idanunta yayi yakasa bata amsa, Waheeda taga Sai Kallan ta yake tace “Babban Yaya kayi shiru kana kallona”

Hannunta yasake riqewa cikin nasa hannayen yace “Aike qanwata ce, damuke uwa daya uba daya hakane ko?”

Waheeda ta gyad’a masa kanta alamun hakane

Yaci gaba da fadin “tunda ke qanwata ce, ke jini nace, idan kika kalli qwayar idona, zakiga yarinyar danake so” (tofa)

Matsowa tayi kusa dashi haryana jin saukar nunfashin ta akan fuskar sa, tazuba masa ido tana so ta tabbatar da maganar sa, Sai can tadawo ta zauna yanda take da, tace “banga komai ba Babban Yaya banda baqi dayake cikin fari na idonka” 😂

Murmushi yayi dimple dinsa suka futo, yace “naji, wannan maganar tazama sirri tsakanin mu, banaso kowa yaji, sannan baqin gawayi nakeso kisamomin acikin gida yanzu”

😳Zaro ido tayi tareda rufe bakinta da hannunta tace “nashiga uku Babban Yaya qona Nadiyar Zakayi idan kaje?”

“banason shirme Dan Allah, amfani zanyi dashi, guda daya nakeso kisamomin”

Tunani tafara saida tagama ta Kalle shi tace “Babban Yaya ai kasan Bama qona gawayi, Amma Naga Ummah tanada wani na leda Wanda take sakawa akan gas idan yayi zafi saita saka turaren wuta, saide inje in Dauko mashi, Amma idan kaji tana jaje karkace nice”

Yace “nida kika kawo min tayaya zan fada? Yi sauri kije ki dauko”

Cikin sauri tafice daga motar tashiga falon da gudu, taje Dakin Ummah Allah yaso tana toilet, tayi sauri ta dauko ledar gawayin guda daya, ta6oye acikin hijab,ta kawo tamiqa masa tace “gashi”

Cikin mamaki tasake Kallan sa tace “Laaaa Babban Yaya yanaga ka sauya Kaya kasaka wannan tsumman? Cemata zakayi Kai mahaukaci ne?” 😂😂

Kallan ta yayi yace “saide in kece mahaukaciya” ya dauki gawayin guda daya yarabashi abiyu, yafara shafawa a fuskar sa da hannun sa, ya dauki wani rawani ya nada a Kansa,yacire agogon hannun sa, yanda yayi baqi ba zakace shine ba, Waheeda tayi shiru tana Kallan ikon Allah, saida yagama 6oye kamar sa sannan yaja motar suka tafi, agaban islamiyar ya faka motar yaqi fita, saida ta Kalle shi tayi murmushi sannan tayi masa bye bye tafice daga motar

Gidansu Nadiya ya nufa
Kafin ya qarasa ya tsaya yafaka motarsa acan nesa da gidan, sannan yafuto yatare wani Dan adedeta yace “Aron Napep din nake nakeso”
Dan adedeta ya kalli adedetan sa Sabo fil dashi, sannan ya kalli Babban Yaya yace “kamarya aro?, malam bansan kaba tayaya zan dauki sabon adedeta na nabaka?”

Babban Yaya yace “kaga mota na Nan, ka tsaya anan kajirani yanzu zan dawo”

Dariya Dan sahun yayi yace “hauka nake zan yarda dakai? Tayaya zaka mallaki wannan motar? In hakane meyasa zaka nemi Aron abun Hawa?”

Kansa yadafe, ya nufi motar ya Dauko agogonsa yabashi yace “yanzu kaga shaida mota tace ai ko? Kariqe wannan agogon idan ban dawo ba kaje ka saida shi zai iya siya Maka sabon adedeta harda Yan canji”

Dan adedeta yayi shiru yana nazari, badan ransa ya soba yafuto yabawa Babban Yaya, Nan da Nan Babban Yaya yahau yatuqa da bissmillah aikuwa adedeta yafara tafiya, baiyi gudu ba ahankali yake tafiya harya qarasa gidan, yana zuwa yahango wata budurwa tana tsaye dawani saurayi me mota, motar ya kalla ya kalli wayar hannun sa, wayar hannun sa kadai zata Iya siyan motar gayen, cikin sauri yakashe ta, yasaka acikin aljihu, sannan yafuto daga adedetan nasa ya tsaya yana Kallan su yana daddanna wayar baba Yusha’u megadi wadda taji wahala harda kyauro ajikinta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button