BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallan sa budurwar tayi suka kwashe da dariya itada saurayin, Babban Yaya ya qarasa wajan su tareda Bawa saurayin hannu yace “Salamu Alaikum”

Saurayin ya Kalle shi daga sama har qasa yaga wani fatattakekken takalmi aqafarsa, yaga fuskar Nan tayi wani irin baqi, ya girgiza Kai tareda dauke Kansa, budurwar ta Kalli saurayin suka hada ido suka sake kwashewa da dariya

Babban Yaya yasosa girarsa guda daya da key din adedeta dayake hannun sa, abunda yariga ya zama dabi’arsa
Ya kalli Budurwar
Yace “Dan Allah Ina neman Nadiya ne”

Tace “nice Nadiya, ya akayi?”

Kai tsaye yace “Ina son magana dake”

Yatsina fuska tayi tace masa “me?”

Saurayin Nata yace “a a Beby, jeki kiji abinda yazo dashi, kika Sani ko neman sadaka yake?”

Babban Yaya baice dashi komai ba yajuya yakoma jikin adedetan sa,Nadiya ta biyo bayansa tana mamaki gashi talaka futuk daga Gani Amma yanayin tafiyarsa kamar ta manyan masu kudi, suna zuwa jikin adedetan ya kalleta yace”Nadiya inason ki, idan bazaki damu ba inaso mu qulla alaqa dake, alaqa ta har abada,Amma ni banida kudi, talaka ne ni idan har kina sona tsakanin ki da Allah, ni banida matsala, bazan 6oye miki komai ba, gidanmu munada yawa kusan mu talatin ne, sannan Mahaifiyata batada lafiya, Paralyze take yi, aikinsan Paralyze ko? “😳🙆🏻‍♀️ðŸ˜?

Nadiya ta jinjina masa Kai tana jin wannan labari nasa,inbanda rainin Hankali meyake nufi da mahaifiyarsa babu lafiya? Tsayuwa ta gyara tace”kana nufin nice zanyi jinyar mahaifiyar ka kenan idan ka kaini gidanka? Sannan acikin mutum talatin din zanyi rayuwa?”

Babban Yaya yace “Allah yamiki Albarka, nasan tunda kinada Hankali Zaki kula da Mahaifiyata, sannan kinga wannan adedetan?” yafadi haka yana buga jikin adedetan😂

Nadiya ta daga masa Kai tace “Nagani”

Yaci gaba da fadin “to sojan hayane, banawa bane, kudin nake Tarawa idan suka cika dubu Dari shida saina Bawa meshi, kinga shikkenan daga Nan yazama nawa” 😂😱

Nadiya tasake jijjiga Kai tace “cigaba Ina jinka”

Babban Yaya yace “idan kika amince Dani, ba zakiyi DANA SANI ba
(My First Novel DANA SANI)
tun lokacin Dana fara ganinki naji duk duniya babu wadda nakeso saike, insha Allah namiki alqawari idan kika amince Dani, ba zakiyi nadama ba, saboda zan hada miki lefe nagani nafada, Sai Wanda yagani, sannan Kuma…. “

Kafin yaci gaba da magana Nadiya ta daga masa hannu ✋🏻tace” dakata malam, nayi ma kama da wadda zatayi jinyar mahaifiyar ka?,konayi ma kama da wadda zata auri Dan adedeta? Bari kaji, ni matar manya ce, akwai Wanda nakeso, Big Brother yana Nan zuwa, kar yazo yaganni dakai ya raina min Hankali, danhaka Sai anjima… “
tajuya tayi gaba, Babban Yaya yafara kiranta yana fadin “Nadiya! Nadiya!!”

Amma tayi banza dashi,Shima Dama Kiran Nata dayake qarfin Hali ne kawai, dama baya so tajuyo 😆
Babu musu yashiga cikin adedetan yatafi, yana zuwa wajan Dan adedetan ya futo yabashi key dinsa yace “nagode gashi”

Dan adedeta yace “Wai harka gama? Naga ko Minti talatin bakayi ba”

Motar sa yabude yashiga yace “nagode”

Cikin sauri Dan adedeta yace “toga agogon Naka”

Babban Yaya yace “Kabarshi kawai” yarufe motarsa yatafi,saboda hadari ne yake San tasowa, Kuma yanaso yaje ya Dauko su Waheeda a islamiya

*** ** ***

Tafiya suke ahankali suna zancen su gwanin sha’awa, Maya tace “Waheeda ki dinga sauri mana, ko bakya ganin hadari”

“ke barni inyi tafiya ta yanda nakeso, idan sauri nakema jikina ya dinga rawa kenan, nikuma banason wannan rawar”

Maya ta kwashe da dariya tace “su Waheeda manyan yanmata, zan so Naga mijinki Waheeda”

“Zaki Gani Maya, kijira munayin candy Sai aure nikam, banaso naci gaba da karatu, nafiso nayi aure na indinga kula da mijina, in shaga6ashi inyi masa abinda yakeso, kinga lokacin saina tafi makaranta, tun yanzu ma mata suna nemana, idan natafi University wakike tunanin zai nemeni? “

Kai tsaye Maya tace”Maza, Amma Kuma kinsan de Babban Yaya baya so ki dinga kula samari ko? Tayaya Zaki samu mijin? Bayan munkusa gama makaranta?”

” can ta matse muku keda Babban yayan, nikam daga Candy Sai aure insha Allah “

Maya tace”gaskiya yarinyar Nan wuyanki ya’isa yanka, nikam yanzu Ina Bayan Babban Yaya, tunda yabani kudin makaranta bazan taba mantawa da alkhairinsa agareni ba, Dan haka dole indinga tuna miki dokarsa a kanki “

Kafin Waheeda tace wani abu anfara yaiyafi, neman wajan 6uya suke Amma sun Rasa, abun Hawa suka fara tarewa Amma kowanne baya tsaya wa, ruwa yaqara karfi Nan da Nan mutane suka fara gudu musanman maza, ruwa yayiwa su Waheeda duka saboda babu mafaka, suna cikin wannan halin Babban Yaya yaqara so, yana zuwa yafuto daga cikin motar yanufesu, Waheeda taga ya sauya wannan kayan daya saka na dazu, murmushi tayi, cikin shagwa6a tace “Babban Yaya shine kaqi zuwa da wuri gashinan ruwa yamana duka nida Maya”

Bece da’ita komai ba, kawai gaban motar yabude mata, tareda fadin “I’m sorry, shiga”

Maya tana tsaye tana Kallan su, lalle Babban Yaya yana son Waheeda, wanne Yaya ne zai budewa qanwar sa mota saikace wata budurwar sa? Anya kuwa yayanta ne?

Saida Waheeda tashiga sannan yarufe, itama Maya tayi sauri tabude gidan baya tashiga, zagayawa yayi yashiga motar, yajuyo yana fuskantar Waheeda, cikin sigar lallashi yace “Sorry”

Bakinta ta turo gaba taqi magana, yasaka hannu yakamo kyakykyawar fuskarta yace “kinji”

Murmushi tasaki, dimple dinta suka futo, tace “shikkenan, Kuma alqawarin dazu, bazan fadawa kowa ba”

Murmushi yayi Shima yace “good girl”

Maya tayi gyaran murya, Dan taga alamun sun manta tana motar 😂
Tace “Babban Yaya Ina wuni”

Firgigit ya dawo haiyacinsa, shaf ya manta tana cikin motar, a taqaice yace “Lafiya”

Sannan yaja motar suka tafi, suna hanya Waheeda Sai zuba masa surutu take, Amma amsar dayake bata batada yawa, har suka qaraso gidansu Maya, suka ajiye ta sannan suka dauki hanyar gida, Bai wuce dasu gida ba saida yashiga tawani shago yasai mata waya qirar iPhone, ya ajiye agaban motar sannan yaja motar suka qarasa gida

Yana tsaida motar a compound din gidan nasu, Waheeda tafara kokarin fita, tana kama handle din kofar taji taqi buduwa, tajuyo tace “Babban Yaya bude”

Wayar daya siyo ya Dauko ya ‘Dora mata akan cinyarta yace “Gashinan, nasan inda kinada waya Zaki kirani kicemin kun tashi, bazan Bari ruwa yamiki duka ba kamar yau”

Waheeda tafara kokarin budewa, tana Ganin wayar tasaki wani ihun murna ta rungume shi, yana jin yanda tudun qirjinta yake mintsininsa cikin ransa yace “yasalammmm!”

Daurewa kawai yayi, ahankali yazareta daga jikinsa yace “bansan yaushe zakiyi Hankali ba, kina ta6ani any how kamar wani muharraminki”

Kwata kwata Waheeda batama kalli inda yakeba bare tayi nazari akan kalamansa, cikin murna tace “Toda menene inba Shiba? Babban Yaya, nagode, Allah yasa kadinga cin ball a koda yaushe, Allah yaqara girma”

Saida ya hadiye wani irin yawu, sannan yace “Amin” yabude mata motar tafita dagudu tanaso ta nunawa yanbiyu itama tayi waya

Da daddare suna kallo gaba dayansu, Waheeda tana saka number Yan gidan tana saving dinsu cikin sabuwar wayarta, yanbiyu suna nuna mata wasu abubuwan da bata Sani ba, su Sa’ad da Sa’eed tareda Babban Yaya Sai labarin qwallo suke, Babban Yaya anta6o masa inda yakeso, wato zancen qwallo, Sai hira suke sunata dariya kamar bashi ba, Ummah ta Kalle shi tace “Yayansu Yaya kukai kaida Nadiya ne?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button