BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai tsaye tace “inde Dama ce nabaka, menene acikin muryar tawa?”

Yace “bakisan menene acikin muryarki ba? Muryarki tana d’aukeda wani sinadari, duk Wanda yajita, dole ne tatafi da Imaninsa”

Dadi yakama Waheeda, ashe muryarta tanada dadi shiyasa Babban Yaya yahanasu kula Samari, ashe Dan karsu hadu da samari su dinga yabon baiwar murya me dadi irin tasu shiyasa yaqi dadi yahanasu kula samarin

Cikin jin dadi tace “Nagode sosai, baka fadamin sunan ka ba”

Yace “Af… Aina manta ban fada miki sunana ba, gaba daya nagama shagaltuwa dajin wannan daddad’ar muryar Taki ne, sunana Hassan, Ana kirana Sas, ni soja ne, iyayena da kowa da kowa nawa suna zaune a kaduna, iyayena suna damuna inyi aure, nikuma har yanzu ban hadu da wadda nake soba, tun Bayan rabuwa ta da budurwata ta farko “

Waheeda tace” Allah sarki, Allah yabaka mace tagari, nikuma sunana Waheeda, Ina Garin kano, Ina zaune a unguwar, Amma inaso kabani labari menene yahada ka da budurwarka har kuka rabu? “

Yace” Waheeda sunanki nada dadi kamar yanda muryarki Takeda dadi, zan baki labari anjima idan kin Bani damar sake kiranki Akaro na biyu, saboda alfarmar Dana nema shine indinga kiranki sau daya a rana “

Waheeda tace”nabaka Dama ka kira”

Cikin farin ciki yace “yanzu kin amince indinga kiranki sau biyu kenan a rana?”

Kai tsaye batare da tunanin komai ba tace “Na’amince”

Yace “nagode Yar’uwata, gaskiya kinada hali Mai kyau, please ki kula da kanki karki Bari ko quda yata6a ki”

Cikin farin ciki tace “to shikkenan” sannan ta kashe wayar

Ihsan da Intisar da tun dazu suke Kallan ta sukace “dawa kike waya Waheeda?”

Harararsu tayi tace “miye naku? To da saurayi nake waya, soja ne, Kuma ni tundaga yanzu ya kwanta min araina, so kuke naqi kula samari kamar ku daga qarshe a hadani da wani a dangi? To banason auren had’i, danhaka samari na zan kula”

Intisar tace “aikuwa wallahi baki isaba, bazakija Babban Yaya yazo ya qwace mana wayoyin muba, tunda yahanamu, kega me kunnan qashi ko?”

Waheeda tace “kunnan qarfe Bana qashi ba,nide saina kula samari, ku Kuma dakuka tsaya Babban Yaya yamuku hud’uba, to saikuje kuyi tayi, bakusan halin Babban Yaya bane, kaiku zaiyi yabaro”

Ihsan tace “Waheeda idan kika kuskura kika sake fadar wata magana dangane d Babban Yaya na rantse da Allah Sai munyi miki duka a Dakin Nan, qarqari kice Ummah zatazo cetonki, to wallahi kulle kofar zamuyi saimun nuna miki jiki, banza marar kunya” tafadi haka tareda kokarin cire uniform dinta.

Waheeda tace “ku kasheni ku kaiwa uwata gawata, qarshe kenan” tafadi haka, tareda shigewa toilet domin watsa ruwa

Sas soja bai sake Kiran Waheeda ba Sai dare, a lokacin harta matsu ya kirata, a zaune suke afalo yakira, tana dagawa tayi cikin dakinsu da gudu, kowa yabita da kallo gaba dayansu sunyi tunanin Babban Yaya ne ya kirata, yan biyu ne kawai suka San abinda take 6oyewa, kwanciya tayi akan gado,tana yi masa sallama, Bayan sun gaisa tace “Ina jinka, tun dazu nake jiran kiranka, Amma baka kiraba”

“kiyi hakuri sarauniyar kyawawa, oganmu ne ya kirani, kinsan sojoji babu zama”

Murmushi tayi tace “Ina jinka, kabani labarin abinda yarabaka da budurwarka”

Yace “Mun dad’e tareda yarinyar,kinga nide soja ne, Amma bantaba yin kuka ba Sai akan yarinyar Nan, nayi kuka kamar zanyi hauka, Waheeda muna cikin soyaiya da yarinyar Nan har ankai kudin gaisuwa da komai, mamanta tace ai akwai Wanda ta yiwa alqawarin auren ta, waje daya suke aiki dashi, haka aka bamu hakuri, akwai gida na bakiga yanda na tsara Shiba, Sai hakura nayi dashi nabawa qanina shi, gashi nine Babba a gidanmu, kowa so yake nayi aure, yanzu haka lefen Dana hadawa yarinyar suna Nan, kawai wasu qananun abubuwan ne ba’a saka ba, yanzu gashi narabu da’ita komai ya zama tarihi, saide in nemi alfarma awani waje ko za’a Bani Dama “

Waheeda ta Lumshe idonta tace” wacce irin alfarma kenan?”

Yace” Alfarma mana, nasamu Dama nashiga cikin zuciyar ki, kibani key dinta na kulleta, ta yanda babu wani d’a namiji dazan iya bud’ewa bare yasamu damar shiga “

Tace”to inde wannna ne, nabaka Dama, Allah ya tabbatar mana da alkhairi “

Farinciki yakama Sas, yace”amma inaso namiki wata tambaya guda daya”

Tace “Ina jinka”

Yace “gashi bamu taba ganin junaba har mun qulla alaqa, meyasa kike sona?”

Ajiyar zuciya tayi tace “gaskiya nayaba da Hankalinka, dakuma tarin nutsuwarka, wannan kawai shine”

Murmushi yayi yace “zakici gaba da sona Waheeda idan kikai tozali Dani? Karnaje dadin baki kikemin, saboda nide baqi ne, banida d’iqon fari kod’aya ajikina, ni baqi ne”

Waheeda tayi shiru tatafi tunani, tatuna wata hira dasuka ta6ayi dasu Neenah aboarding, sunce mata maza baqaqe sunfi lafiya ko a wajan aure, sunfi fararen mazaje bada himma🙊
Sas yace “kinyi shiru Waheeda”

Cikin sauri tace “ai nafison irinsu, Allah yabarmu tare”

Yace “Amin, yaushe zanzo naganki kiganni? Banaso ki ganni awaya kiji bakya sona Waheeda, Gara nazo ki ganni a zahiri, sannan inyi magana da babanku cewa Ina sonki, inaso na aureki idan kin kammala makaranta”

Waheeda tasake yin qasa da murya tace “Allah yakawo ka lafiya”

Yace “to shikkenan, ki kulamin da kanki, karki manta kiyi alwala sannan kiyi addu’ah kafin ki kwanta”

Waheeda tayi hamdala cikin ranta, ta San cewa tabbas tayi dace da samun Miji na gari

Duk abinda take ‘yanbiyu suna ganin ta, basuce mata komai ba saboda idan sunyi mata magana ma rashin kunya zata musu, kawai de sunsa aransu duk lokacin da taja Babban Yaya yahanasu riqe waya Sai sunyi mata dukan mutuwa 😂

Tsawon sati biyu Waheeda ta d’auka tana waya da soja, ba tareda kowa nagaidan yasani ba, daga ita Sai yanbiyu ne kawai suka sani, zuwa wannan lokacin Hankalin Babban Yaya ya kwanta, yanayin ball d’insa cikin nutsuwa bashida damuwar komai, tunda yaga yayi sati d’aya, yayi biyu, har uku, ba’a kirashi agida akan matsalar Waheeda ba yasan cewa taqara Hankali, idan yaga Kiran Ummah har d’auka yake cikin nishadi, yasan cewa kawai gaisawa zasuyi.

Cikin sati na hud’un ne Sas yace mata zaizo yaganta ranar asabat, ranar kuwa tun safe takasa zaune takasa tsaye, yanbiyu tun kafin su tashi daga bacci tafara tashinsu, cikin ladabi tace “Inti yau Soja zaizo, mezan shirya masa?”

Intisar tace “waida gaske zuwan zaiyi? Bakya tsorone Waheeda?”

Bakinta ta turo gaba tace “Toni Ina sonsa, Dan Allah Kuna ‘yan’uwana mata idan Baku Bani goyon baya nafita kunyar sa ba, wakuke so yabani?”

Tausayin ta yakama Intisar, tajuya ta kalli Ihsan, Ihsan tace “kinga Inti babu ruwana, idan Babban Yaya yaji, mezamu ce masa?”

Waheeda tace “Kai Ihsan Dan Allah, idan Ummah ta tambaye ku karkuce saurayina ne, kawai kuce mata Dan makarantar mu ne, ba shikkenan ba?”

Nan take,Waheeda ta kalallame zuciyar ‘yan’uwan Nata, suka d’auki shawarar data basu,Waheeda ta wuce kitchen tafara hadawa soja kayan makulashe

Karfe hudu na yamma, soja yazo, d’an sahu ne yakawo shi har unguwar ya ajiyeshi, yakira wayar Waheeda yasanar da’ita yazo

Rabonta da saka mayafi harta manta,saboda Babban Yaya yahanasu, Amma yau haka taci kwalliya cikin Riga da siket, kayan ya kar6i jikinta sosai, tayi kyau nesa ba kusa ba, fuska taci kwalliya, tadauki mayafi Dan qarami ta yafa, sannan tadauki kayan data had’a masa tafita dashi compound din gidan, Ummah tana daki ba tasan Wainar dasuke toyawa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button