BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar yanda yafada dinne kuwa, domin kuwa Waheeda tana zuwa ta ganshi baqiqqirin dashi, gashi gajere, Amma duk da haka Saitayi murmushi ta qarasa wajan sa tace “qaraso gidan mana”
Babu musu yabiyo Bayan ta Sai qarewa tsarin gidan nasu kallo yake yana jijjiga Kai, komai da komai na tsarin gidan yamasa kamar tsarin ginin turawa, daga Gani yarinyar ‘Yan manyan mutane ce
Gidan suka shiga, baba maigadi dayasan cewa basa saka mayafi Kuma basa kawo samari, Sai mamaki ya kamashi, Dan haka yanufi cikin gidan zai fadawa Ummah abinda yake faruwa yaji koda sanin ta haka zata tafaru
Sas yana ganin shigar maigadi ya kalleta yace “ashe da gaske banyi qarya ba Dana saka miki suna sarauniyar kyawawa”
Waheeda tayi murmushi ta rufe fuskarta da tafukan hannunta cikin kunya, sannan tace “tun dazu nake jiran zuwanka, ashe saukar yamma zakayi”
Yace “eh wallahi,Ina hanya ma wayata ta dauke babu charge, yanzu ma kunna ta nayi na kiraki,kinga harta sake mutuwa, gashi ban kira mama na nace mata na’iso wajanki lafiya ba, kinsan me ma? Jiya fa dazan taho wajanki saida tace idan nazo na kula dake sosai, sannan tamin lissafin abubuwan da babu acikin kayan lefen Dana had’awa budurwa ta tada, Wai babu takalmi da jaka, yakamata aqara guda uku uku akan nada, da ansaka dozin d’aya, idan aka qara uku akai, kinga ya zama Sha biyar kenan, yakamata ace nakira ta nasanar da’ita nazo wajan Mai kyau,gashi wayar tawa tamutu,Bani Aron taki wayar nakirata”
Waheeda tanajin wannan dogon bayanin nasa taji dad’i, gashi de bashida wani kyau na azo agani,Amma ita a haukan ta bataga laifin sa ba, babu tunanin komai ta bashi wannan sabuwar waya tata, tace”gashi kakirata to”
Sas ya kar6i wayar yabata wata leda a hannun sa yace”ga kyautar Dana kawo miki, nayi niyyar kawo miki Riga irintamu ta sojoji, sainace idan zan sake dawowa saina kawo miki rigar, Amma yanzu ga wannan”
Waheeda ta kar6a tace”nagode”
Yace “Bari inkira mama”
yamatsa jikin get din gidan zaiyi wayar, Hankalin Waheeda yanakan kyautar daya bata, taji de abu yana yawo aciki, Amma bata San menene ba, saboda anyi wrapping din abun da wata leda me kyau, tana d’ago kanta, taga wayam! Babu Sas babu dalilin sa 🙆ðŸ»â€â™€ï¸?
Gabanta ne yafad’i, cikin ranta tace”wannan mutumin fa ba saninsa nayi ba, kar naje yagudu da wayata, ba kowa ne ya fado mata araiba Sai Babban Yaya😂
Ledar da Sas yabata ce tasulale tafadi daga hannunta, cikin sauri ta bude get din gidan tafita, mayafin data yafa yafad’i qasa Amma batabi ta Kansa ba, haka tafuto titi tana waige waige, Amma abu kamar wasa, babu soja babu dalilin sa, awajan ta tsugunna ta Dora hannunta aka 🙆ðŸ»â€â™€ï¸tace “nashiga uku na, namutu na lalace!, wallahi Babban Yaya saiya kasheni” 😂
Baba megadi yazo da gudu shida Ummah, Ummah ta dakata daga bakin get din, baba megadi ya qarasa wajanta yariqo hannunta yana fadin “Waheeda lafiya? Me yayi miki? Ina baqon naki yake?”
Waheeda bata Bawa baba me gadi amsa ba, saboda kuka dayaci qarfin ta, cikin kuka tace “innalillahi wa inna’ilaihirraji’un, shikkenan namutu, nakade har ganye na, Wallahi barin garin Nan zanyi tun kafin Babban Yaya ya dawo”
Baba megadi haka yakamota suka shigo gidan, suna zuwa compound din gidan tazube awajen tana ihun kuka, yanbiyu suka qaraso da gudu suna tambayar ta menene, Ummah ta riqeta tace “kimin bayani mana, Wai menene?megadi yacemin kinyi baqo, Wanne irin baqo kika kawo gidan? Kuma me yayi miki?”
Waheeda de takasa magana, Dan Gani take idan ta fad’awa Ummah to zata kira Babban Yaya ta fad’amasa
Yanbiyu suka dauki Ledar da Waheeda ta yar, Ihsan tabude Ledar da’aka yi wrapping dinta, tana budewa saiga chesee ya bayyana, ‘Yan hamsin hamsin guda biyu, hada baki sukai sukace “Laaaa Cizi ne”
Kallan Waheeda sukayi, intisar tace “meya miki ne?”
Cikin kuka tace “Yagudu da wayata, naduba ko’ina baya Nan, wallahi gidan Nan zan Bari” tana fadar haka ta kwasa da gudu tayi cikin gida
Anan Ummah ta fahimci komai, Kai tsaye tabi Bayan Waheeda har d’akinsu, tana zuwa ta rufeta da duka, daqyar yanbiyu suka ceceta, Ummah taja kofar Dakin ta kulle Waheeda aciki, Dan tayi alqawari wannan Karon Waheeda tadena fita bare taja mata wata masifar
Har dare Waheeda tana d’akinsu akulle, Ummah tahana kowa yabudeta, Daddy ne ya dawo daga wajan aiki Sai masifa yake, ta inda yake shiga batanan yake fita ba
Duk sunyi shiru babu Wanda ya tanka masa, ita kanta Ummah ba tasan me zatace ba
Kallan ‘yanbiyu yayi yace “kuje ku budeta tazo Nan Ina nemanta”
Inti taje ta bude Waheeda, akan gadon su taganta har lokacin kuka take, ta kifa kanta akan cinyoyin ta,dogon gashin kanta yazubo gadon Bayan ta, wani Kuma yarufe mata fuska kamar de mace me aljannu, kanta har ciwo yake saboda kuka, yanzu shikkenan wayarta tatafi, wayar ko wata daya Babban Yaya baiyi da siya mata itaba, ta Ina zata Iya Kallan idonsa tace takawo saurayi gida shikuma ya sace mata wayar? Intisar tace “kije Daddy yana kiranki”
Ahankali tataso, suna zuwa falon kowa yabita da kallo, su Sa’ad jisuke kamar Su make ta, Daddy ya kalleta yace “Dan wanne gidane Yaron? A wacce unguwa yake?”
Cikin kuka tace “Dadday bansan gidansu ba, ni bansan shi ba, yau nata6a ganinsa, Dan girman Allah Daddy karka fadawa Babban Yaya, Allah kasheni zaiyi”
Cikin fishi Daddy yace “yau kika fara ganinsa har kika d’auki waya kika bashi saboda ga yayanku me kudin banza yasiya miki waya ko?”
Ihsan tace “Daddy kayi hakuri, insha Allah bazata sake ba”
Sa’eed yakalli Ummah yace “Ummah kikira Babban Yaya kifada masa Dan Allah, sonake ya dawo ya kakkarya yarinyar Nan, Danni idan nakamaki saina miki Dukan mutuwa, inyaso nakawo gawarki, tunda haka kike so Dama”
Waheeda de tayi shiru, takasa cewa komai, Sai Jan zuciya take, fuskar Nan tayi jajir saboda kuka
Ummah tace “bazan kirashi ba Sa’eed, kullum Waheeda cikin janyo mana masifa take, kullum ninake kiransa nafada masa, yanzu Kam, bazan kirashi ba, idan kullum zan dinga kiransa Ina fada masa matsala ai Kuma idan yaga kirana gabansa faduwa zai dinga yi,sannan Kuma bance kufada masa ba, kubarshi yayi aikinsa, Daddynku zai dauki mataki akan haka”
Haka suka zauna a falon kowa yayi jugum, anrasa takamaimai Wanda zai kira Babban Yaya yafada masa abinda yake faruwa 😂
Washe gari Waheeda bataje school ba, haka ta zauna tayi shiru adaki kamar marar lafiya, ko sunan Babban Yaya taji an ambata gabanta faduwa yake,yanda ta nutsu awaje daya, Sai gidan yayi shiru, idan ka kalli Waheeda saita baka sha’awa yanda tazama wata kamila, saide kowa taciki na ciki
Tsawon kwana biyu kenan da 6atan wayar Waheeda, har yanzu babu Wanda ya fad’awa Babban Yaya, sannan daddy bai d’auki wani qwaqwaqwaran mataki ba, asalima fishi yake da’ita, Kuma a kwana biyun Nan Waheeda bataje makaranta ba, tana zaune agida abun duniya yataru yayi mata yawa, yau da yamma suna zaune, Anty Maryam tashigo gidan cikin tashi Hankali, tana zuwa ta nufi Ummah tace “Ummah yajikin Waheeda? Ashe batada lafiya Amma Ummah kukasa fadamin? Awanne asbitin aka kwantar da’ita?”
Kafin Ummah tasake magana, Maya tayi sallama cikin falon nasu tana sharar hawaye, ta qarasa wajan Ummah tace “Ummah ashe Waheeda batada lafiya? Shiyasa Bata shiga makaranta kwana biyu? Na tambayi ‘yanbiyu sunce min lafiyarta kalau ashe 6oyemin sukayi”