BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kan Ummah ya d’aure, ta kalli Maryam dinta dakuma Maya tace “Wai wacce Waheeda kuke magana a kaine?”

Wayar Ummah ce tayi qara, ta d’auka tare fadin “sa’ad ya akayi?”

Yace” Ummah, wannan gayen daya sace wayar Waheeda fa inaga Dan damfara ne, ba’iya wayar yakeso ba, harda damfara a tsarin nasa, yanzu Ina zaune yaturo min saqo Wai me wannan wayar batada lafiya, tana kwance agadon Asbiti, Ana buqatar tallafin kudi, Sai kuma account number aqasan saqon”

Ummah tace “innalillah…. Sa’ad shiyasa na kulleta Adaki fa, saboda muna Zaman zamanmu wata Rana zatasa azo har gida a sacemu”

Sa’eed ne yake Kiran wayar, Ummah tace “Sa’ad kashe, ga dan’uwanka Nan Shima yana kira”

Tana daukar wayar Sa’eed din, Shima abinda yafada mata kenan, Ummah ta kashe wayar ta kalli su Maryam “wallahi lafiyar Waheeda kalau……” anan Ummah ta basu labarin abinda yake faruwa, Maya tace “Kai Amma wannan anyi tsinanne, yazo har gida yasace mata waya sannan ya dinga turawa mutane cewa batada lafiya aturo Masa kudi?, Ummah Ina Waheedan?”

Ummah ta nunawa Maya d’akinsu Waheeda, tatashi ta nufi Dakin, anan taga Waheeda ta zauna tayi shiru tana tunani

Maya ta dafata tace” Alhamdulillah, har hankali na ya kwanta wallahi qawata, text fa akamin bakida lafiya, kina gadon Asbiti a kwance, Wai Ana buqatar tallafin kudi ta wani account Number dayake Qasan saqon “

Waheeda tayi shiru takasa Bawa Maya amsa, Maya tace” Waheeda kalau kike kuwa? Inata magana kinyi shiru? Yanzu Waheeda shawarar Dana baki ashe baki d’auka ba saida kika kula saurayi?”

Waheeda tacire hannunta daga tagumin da tayi tace”Maya Babban Yaya”😂

*** ** ***

Motsa jiki yake cikin nutsuwa da kwanciyar Hankali, wayarsa dake ajiye acan Gefe yaji tana ringing, kafin ya dauka harta katse, dakatawa yayi da abinda yake ya d’auki ruwa yasha, sannan ya d’auki wayar, number datake kiransa ma baisan taba, saikuma saqo guda daya, daga Waheeda, yayi mamakin ganin saqon ta, saboda yasan bata masa text message, Kiran ma ba sosai take neman saba, shiyasa saqon ya d’auki Hankalinsa, wajan zama ya nema, sannan ya bud’e saqon Nata, abinda yagani ne yasashi yatsina fuskar sa, kamarya yatura kudi ta wannan account din? Waheeda ce batada lafiya Amma akasa fada masa har wani account number ake turowa atura tallafin kudi tanan? Account number waye wannan din?
“mashirmaciya” yafadi hakan a fili
Sannan yayi Dialing number Tata, har ta kusa katsewa sannan aka d’auka, memakon yaji muryar Waheeda, Sai yaji muryar wani, lokaci d’aya yanayin fuskar sa ta sauya,wani irin baqin kishi yataso masa, cikin 6acin rai,yace “waye?”

Daga d’ayan bangaren Sas soja yace “yayan me wayar ne, dama batada lafiya ne, tana kwance agadon Asbiti, muna neman tallafin kudi ne Wanda za’a mata aiki dashi, shine mukabi list din contact dinta muka tura musu”

Sumar Kansa ya hargitsa, cikin ransa yace Waheeda zata kasheni, Amma a fili saiyace “za’a turo” daga Nan yakashe wayar

Yana kashewa wani Kiran yasake shigo wa, number da’aka kirashi da’ita d’azu ne, ya d’auka tareda sallama, daga d’ayan bangaren akace “dawa muke magana?”

Kai tsaye yace “Naufal Umar Arabo,a.k.a Big Brother”

“Ok ikon Allah, ashe Big Brother ne, wato yalla6ai abinda yake faruwa shine, akwai wata yarinya da akai kidnapping dinta, kidnappers din sun nemi atura musu kudi, Kuma iyayen yarinyar sun tura musu kudin, daga qarshe Sai suka aikowa iyayen yarinyar da gawar ‘yarsu, to Wanda aka turawa kud’in mun bibiyi Sim card din dayake amfani dashi mungano yana waya da iyayen yarinyar ne ta wata number waya, munyi bincike akan number, mungano number wata yarinya ce sunanta Waheeda Umar Arabo, kamar yanda mukagani a rigister Sim card din, saboda haka munyi tracking number Waheeda Umar Arabo mun dauki wasu daga numbers din dayake kira, aciki muka Gani harda taka number,yanzu haka ma kunyi waya, shine mukeso ka temaka mana, kafada mana inda yarinyar take, zamuje da’ita office dinmu, domin ta amsa mana wasu tambayoyi dangane da wannan Mai laifin ko Allah zaisa mu kamashi “

Babban Yaya yayi shiruuuu yadafe goshinsa da hannunsa 🤦🏻‍♂ï¸?,Yama Rasa abinda zaice, har sukaji yayi shiru sukace”yalla6ai lafiya dai ko?ko bakasan yarinyar ba?”

Ajiyar zuciya yayi yace”nasanta, she’s my Sister, kuyi hakuri kubani awa hudu, zanzo qasar, saina Baku ita”

Godia sukayi masa dangane da had’in kan daya basu,sannan suka kashe wayar

Yajima a zaune a wajan, Yama Rasa wazai nema domin qarin bayani? Menene yahad’a ta da wani har zata d’auki waya ta bashi? Tashi yayi yaje ya shirya, yayi mutuqar kyau cikin qananun Kaya, saida ya toshe kunnansa da Bluetooth sannan ya d’auki wayarsa ya futo daga gidan

Karfe hudu na yamma ne yakawo shi gida, yana zuwa yakirasu, yafad’a musu yazo,su qara so sutafi da yarinyar, tun karfe uku yakamata ace yazo, but saida yagama da jama’arsa sannan yaqara so cikin gidan, kowa ganinsa yayi afalo kamar anjefo shi, gaba d’ayansu suna Nan ‘Yan gidan, zama yayi akan kujera, cikin mamakin ganinsa Ummah tace “Son, lafiya naganka agida?”

Kansa a qasa yace “aina Dena zuwa ko’ina Ummah, haqura zanyi da aikina, saboda idan natafi ma, Waheeda Virus zata dawo Dani”☹️🙊😂

Ummah tayi shiru kamar andoka mata sanda, cikin ranta tace yaji komai kenan, su Ihsan ne suka tafi da gudu d’aki suka fad’awa Waheeda Babban Yaya yazo

Gabantane yafadi, ahankali tatashi tad’auko hijab d’inta ta6oye shi abayanta, tare suka futo falo, Waheeda tafara bin bango zata gudu, a lokacin Yan sanda sukai sallama cikin falon

Babban Yaya yad’ago Kansa ya Kalle su, idanunsa sunyi jajir saboda tsantsar 6acin rai, ba taredaya Kalle taba yace “ke Zonan”

Hawayene suka fara sintiri akan kyakykyawar fuskar ta, agaban sa ta tsugunna tafara sheshshekar kuka,but takasa magana,kwata kwata taqi d’agowa ta kalli qwayar idonsa, cikin 6acin rai yace “ni Baban kine?”

Cikin kuka ta girgiza masa Kai hawaye wani nabin wani

Yace “to tunda ban haifeki ba, bazai iyu ki kasheni da raina ba”

qafarsa takama tariqe, cikin kuka , tace “Babban Yaya, Allah natuba, bazan sake ba, Babban Yaya kayi hakuri karka sa sutafi Dani, wallahi Allah bazan sake ba”

Kuka ne yakama ‘yanbiyu, su kansu Waheeda tabasu tausayi, sukuwa ‘yanbiyu maza Sa’ad da Sa’eed, wayarsu suka d’auka suke dannawa, Ummah ma tayi shiru tana Kallan su

Gaba d’aya falon ya kaure da kukan Waheeda dakuma na ‘yanbiyu, Babban Yaya ya kalli ‘Yan sandan dasuke tsaye a bakin qofa yace “Yalla6ai gatanan kutafi da’ita”

Volume din kukansu ne yaqaru, wata daga cikin police din mace, tazo takama hannun Waheeda tana janta, cikin kuka Waheeda take fadin “wayyo Allah na zasu tafi Dani, Babban Yaya! Babban Yaya!! Babban Yaya!!”
Har suka jata, suka tafi da’ita, bata daina kiransa ba.

Amnah
1/28/22, 20:50 – Ummi Tandama😇: BABBAN YAYA

Writing By Amnah El Yaqoub

Like my Page On Facebook
https://www.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/

13&14

‘Yanbiyu ne sukai d’akinsu da gudu suna kuka, Ihsan ta d’auki wayarta cikin kuka ta fad’awa Anty Maryam halin da ake ciki.

Kwantar da Kansa yayi ajikin kujera ya Lumshe idonsa, yanda take qwala masa kira har yanzu muryarta takasa barin kunnansa, Ummah ta Kalle shi tace “kaje Kaci abinci kahuta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button