BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yace “Ummah na qoshi”

“kamarya ka qoshi? Ban fahimta ba? Kadawo daga wannan doguwar tafiyar kace bazakaci abinci ba? Yi hakuri Dawo ka zauna nabaka”

Yanbiyu suka had’a ido sukai murmushi, Daddy yace “a a, Usman kaji fa, ni banta6a ganin uwar da bata 6oye son d’anta nafarko ba sai Hajiya, qarara take nunawa Yaron Nan soyaiya”

Uncle Usman yayi murmushi yace “ya qwace wa Waheeda kujerar tane, ga auta,me za’ayi da tsohon tuzuru”

Babban Yaya yayi murmushi yace “Ummah Nasha madara, saida safenku”

Ummah Tajuya ta kalli hajiya Anty tace “kinga fishi yake, tun dazu nake masa maganar abinci yaqi ci”

Hajiya Anty takalli Waheeda,tuni Waheeda ta d’auki haske, tatashi tafara zuba abincin tace “Bari nakai masa Ummah”

Ummah tace “jeki Kai masa, idan yaqi ci kirabu dashi, shiyasan meyake damunsa Kuma”

Waheeda tadauki abincin ta nufi d’akinsa dashi

Gaba d’ayansu ‘Yan falon Saida furucin Ummah ya basu dariya, Wai shiyasan meyake damunsa

Anty Maryam ta shirya zata tafi, Sa’eed ya d’auketa shida Sa’ad, zasu rakata gidanta

Waheeda na zuwa kofar d’akin nasa batama nemi izni ba tatura ‘Dakin nasa tashiga, yana zaune agefen gadonsa abun duniya yataru yamasa yawa, ga zancen tafiyar su qauye gakuma 6acin ran Waheeda

Yanayin data ganshi aciki ne yasa tayi sauri tayi qasa da idonta, daga shi zai gajeran wando da alama bacci zaiyi, inde yayi wannan shigar Dama tasan bacci zaiyi, agaban sa ya ajiye abincin kanta aqasa tace “gashi Wai inji Ummah”

Tafad’i haka Sannan ta takure awaje d’aya kamar wata baquwa

Yace “ki d’auka kimaida mata, ai nace Nasha madara”

Muryarta ce tafara rawa tace “Dan Allah Kaci”

“kindamu dacin abinci nane? Inda bakya son damuwata ai bazaki dinga batamin rai ba, idan aure kike so saiki futo fili kifadamin aure kike so Sai Amiki”

Cikin sauri tace “Allah Bahaka bane, ni banason aure, Dan Allah kayi hakuri Kaci abincin”

“nafada miki bazanci ba, Ummah ce ta aikoki kikawo min, Kuma nariga nafada mata banajin yunwa”

Kanta aqasa tace “qarya fa nake, nice nakawo ma”

“to saiki koma dashi, bazanci ba”

Kukane yazo mata, ahankali hawaye ya silalo daga idanunta, cikin kuka tace “Babban Yaya Dan Allah kayi hakuri kadena fishi Dani, wallahi bazan sake ba, kakawo paper da biro muyi dakai arubuce bazan sake 6atama raiba”

“ko gaban alqali mukaje bazaki daina halinki ba, kitashi kije kawai, rayuwa ce, ta’ishi kowa”

Tanajin wannan furucin nasa tasake fashewa da Kuka, da sauri ta nufeshi tad’ora kanta akan cinyarsa tana bashi hakuri cikin kuka

😳😳Zaro idonsa yayi, cikin sauri yahad’e qafafunsa waje d’aya, sannan ya janye kanta daga wajan,gudun karta sake aikata abinda tayi yanzun, ta6aro masa aiki, yasa cikin sauri yace “naji… Naji, Nina haqura, shikkenan komai ya wuce, Bani abincin”

Cikin sauri ta bashi abincin, sannan tace “kona baka Babban Yaya?”

Yace “a a, tashi kije, zanci da kaina”

Tashi tayi tsaye sannan tace “thank you” tafuto daga Dakin, shikuma yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya

Bata dad’e da futowa daga falon ba su hajiya Anty suka tafi, suna fita Maya tazo gidan, Bayan sun gaisa dasu Ummah, Waheeda tajata sukayi cikin d’aki, zama sukai akan gado Maya ta qarewa Waheeda kallo, tace “lalle Waheeda kinga rayuwa, ‘yanbiyu suka cemin ‘Yan sanda sun tafi dake bakiji yanda gabana yafadi ba”

Waheeda tayi ajiyar zuciya tace “Maya ai rayuwa Kam Ina kan ganinta, Babban Yaya nefa yace sutafi Dani” 🥺

“ai Dama saida nace Miki ki dinga jin maganar sa” cewar Maya

Waheeda tace “to Maya mutum saiya zauna babu saurayi? Candy fa muke shirin yi, idan ya hanani kula samari shine zai aure ni?”

Maya tace “kika Sani”

Cikin masifa ta hayaiyaqowa Maya tace “kamarya nasani,? Me kike nufi? Koji kike agarin maguzawa muke?”

Maya ta dafata tace “maida wuqar qawata, ke kinsan da hakan meyasa zakice min idan bakiyi samari ba shizai aure ki?”

Tashi tayi tsaye ta nuna wa Maya qofa da hannunta, tace “tashi kifice daga ‘Dakin Nan kafin namiki rashin mutuncin Dana saba Maya, nasan irin Zaman da zanyi dake wallahi”

‘Yanbiyu ne suka shigo ‘Dakin suka tarar da drama, Ihsan tace “kema de Maya da naci kike, Ana wulaqantaki kina liqewa, ai shikkenan”
Tana fad’ar haka tatada kabbarar sallah duk da ba tasan menene dalilin fad’an nasu ba

Intisar tace “Maya muje na rakaki hanya, mungode, Dakin Sani ma bakizo ba, Dan waheeda ba’a mata gwaninta, gobe ma qauye zamu tafi muyi kwana biyu”

Maya ta kalli Waheeda tayi murmushi tace “a dawo lafiya qawata” daga Nan suka futo daga ‘Dakin, Waheeda kuwa ko uffan ba tace musu ba, tayaya ma Maya zata dinga had’ata da Babban Yaya? Yayanta uwa d’aya uba d’aya saikace wasu kafirai ba musulmai ba? Tsaki tasaki Bayan fitarsu tashige toilet domin d’auro alwala

Washe gari haka suka had’a kayansu, kowa ya shirya Amma banda Babban Yaya, yana d’akinsa yaqi futowa, kwata kwata baya son zuwa, Amma babu yanda ya’iya, haka yafuto suka had’u afalo, sukayi wa Ummah sallama

Suna zuwa compound yaja ya tsaya, jiyake kamar yafashe da Kuka, Sa’ad ya Kalle shi yace “Babban Yaya ya za’ayi ne?, Naga kamar mota d’aya tayi mana kadan”

Waheeda tayi zuruf tace “eh wallahi, aqaro mana wata, kowa yabaje son ransa” 😃

Babban Yaya ya kalleta, sannan ya kalli Sa’ad yace “bawata mota daza’a qara, mushiga Prado din can kawai muje, babu driver acikin mu ai bare muyi kayan motoci”

Waheeda tayi qasa da kanta, cikin ranta tace wannan Dani yake, sukuwa yanbiyu dariya suka saka, ta Kalle su ta share su

Sa’ad ne zaiyi driving, Babban Yaya yana gefansa, Bayan motar Kuma Sa’eed da Yanbiyu da Waheeda suka shiga, kasancewar glass din motar baqi ne Sai sukai tafiyar su cikin salama babu Wanda yake ganin Babban Yaya bare masoyansa su tsayar dasu

Tafiya tayi tafiya yanmatan duk sunyi shiru kowa yana danna wayarsa banda Waheeda, ☹️
Saisu Babban Yaya dasuke fira shida yanbiyu maza, Waheeda taga kowa harkar sa yake ba’a Tata, ta kalli Babban Yaya tace “Bàbban Yaya yunwa nakeji”

Sa’eed yace “Ina abincin dakuka Dauko?”

Waheeda tace “wanne abinci? Ai bamu Dauko komai ba”

Babban Yaya yajuya ya Kalle su gaba daya yace “waiku wanne irin mashirmata ne? Ku baku iya komai na mata ba komai Sai ance kuyi? Babu irin shirin Nan da mata suke yi kamar su snaks? Saide kici babu kuwa” ya qarasa maganar yana hararar Waheeda

Cikin sauri tayi qasa da kanta, saida suka yi gaba sannan yaga wani yaro yana saida qwai, suka dakata yasauke glass din qasa kadan ya cewa Yaron “basu su juye subaka bucket din”

Waheeda ta leqo kanta tace “Bàbban Yaya nikam guda uku ma ya isheni, bazan iyacin sama da uku ba”

Cikin mamaki ya kalleta yace “Toda nawa zakici ya isheki inba ukun ba?”

Bakinta ta turo gaba tayi shiru, kowa saida ya Debi qwan yanda yakeso, sannan yabawa Yaron kudin da yafi karfin qwan gaba daya harna bucket din, sukaci gaba da tafiya, Waheeda ta 6are guda daya tad’an tashi kadan daga wajan zamanta, tamiqawa Babban Yaya saitin bakinsa tace “Babban Yaya haaa”

Dafe Kansa yayi da hannunsa yayi shiru 🤦🏻‍♂�

Cikin fada Sa’eed yace “ke Dalla malama kimana shiru, haba, duk kin damemu, yarasa qwan dazaici saina bakin titi saikace ke?”

Babban Yaya yayi murmushi, yasaka hannun sa ya riqe hannun Waheeda data miqo masa qwan, sannan ya karyi Dan kadan, yasaki hannun Nata, Waheeda Takoma wajan zamanta ta zauna, tanacin sauran Wanda Babban Yaya ya karya, har suka kusa Garin, bata sake magana ba, daga qarshe ma bacci ne ya dauketa, saida suka qarasa Garin sannan suka tasheta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button