BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Sosai Baba Habu da yayansa sukai murna da zuwansu, Sai Nan Nan ake dasu, matarsa mama Haajara ta shimfida musu tabarma a tsakar gida kowa ya zauna, Ana sake sabuwar gaisuwa
Shayinsu na buzaye tatashi tadora musu,suna fira tana ajiyewa kowa agabansa,ta miqe tace “Bari adora muku abinci, ga miya Nan nagama ta tun safe, Waheeda tatashi tacire hijabin jikinta tace”zauna mama, zan Dora”
Tafadi haka tana nufar inda aka ajiye tukwanen gidan, Babban Yaya ya daga Kai ya kalleta, cikin ransa yace kamar me Hankali
Baba Habu ya dauki wayarsa yafara magana “gasu sun qara so mekuke jirane Baku zoba?”
Daga daya bangaren akayi magana, saiya sake cewa “wanne irin zabbi? Ga kaji Nan tun jiya Haajara take aikin su, zasuci, kutaho kuga yan’uwanku, banason rashin zumunci ni” 🤣
Kallan mama Haajara yayi yace “su Yahya ne, Suda yakamata ace suna gidan Nan dasu zamu karbi baqi Amma ke kiji Wai sun tafi neman zabbi zasu kawo asoya musu”
Murmushi sukayi dukansu, yajuya ya kalli mazan yace “to ku aiba zama zakuyi ba, tashi zakuyi mutafi ku gaisa da yan’unguwa, daga Nan muje na nuna muku gonakin mu, nida iyayenku”
Babban Yaya ya sunkuyar da Kansa baice komai ba, Dan tsoro yake yasan halin tijarar baba Habu karya jaji6o masa wata yarinyar awannan qauyen
Sa’eed yace “Baba yanzu fa kagama cewa baqi,inamu Ina Gona? tokuje dasu Babban Yaya ni zan d’anyi wani abu”
Baba Habu yace “kaji wani sakarci, tokai kana namiji Ina kaga ta zama? Sa’adun ne ko Sa’eedu? Namiji baya zama, kutashi muje”
Sa’ad yayi dariya yace “Sa’eed ne baba, ka ganeshi dakyau”
Haka suka fita badan ransu yasoba, mama Haajara ta kalli tukunyar da Waheeda ta ‘Dora, tace “Waheeda wannan tukunyar a6ule take” Waheeda hankalin ta yana kan girki batajiba
Ihsan tace “Waheeda tukunyar da kika Dora a6ule take fa”
Juyowa tayi ta Kalle su, dama aciki take dasu, suna ganin ta tana aiki Amma babu Wanda ya taso acikinsu,sun Barta tana Fama da hayaqi, dankwalinta ta turo gaba, tulun dogon gashinta yafuto ta qeyarta, tace “kibarta taita zuba, Ina wuta tana ruwa, Sai muga wa Allah zai Bawa sa’ah”
Mama Haajara tayi dariya tace “a a Waheeda, ba za’ayi hakaba” tatashi ta nufi wajan girkin, suma yanbiyu suka taso, saita basu salat da tumatir su yanka
Majalissa Majalissa Baba Habu yake yawo dasu Babban Yaya yana nunawa abokai da yan’uwan Arziqi su, kan kace me, matasa sun taru a wajan Babban Yaya, wasu suyi photo wasu Kuma videos, wasu Kuma kawai binsa suke sunata zance, ayawon zaga Garin dasuke suka hadu dasu Yahya, sune suka janye Babban Yaya kasancewar su sa’anni,sannan suka nufi gonar dashi, daga baya baba Habu ya qaraso tareda su Sa’ad, gonakin yafara nuna musu yace “wannan Babbar gonar ta Usman ce, gata Umaru can agaba, duk ni nake kula musu dashi, dazaku iya da munje wasu gonakin daku duk kun Gani”
Babban Yaya yace “Baba gobe Sai muje ai, Sai muga gari ma”
Baba Habu yayi fara’ah yace “eto Kuma kaima kace wani abu, yanzu to riqe wannan fartanyar, gyara min Nan wajan kacire ciyawar nan data futo” 😂
Sa’ad yace “baba muda mukazo ganin gona Kuma saimu fara aiki?”🤔
“aiku ba mazaje bane, kubar namiji yayi aiki”
Babban Yaya yarasa abinda yake masa dadi, haka ya karba yafara cire ciyawar dasuka futo, abokan baba Habu ne sukazo wuce wa ya daga murya yace “malam idi, ku qaraso ku gaisa da yarana Yan birni”
Su malam idi suna zuwa sukace “masha Allah, Wai duka Nan yaran Usman da Umaru ne?”
Baba Habu yace “a a, duka yaran Umaru ne, shi Usman ai babu yaro awajansa”
Ya nuna musu Babban Yaya da Kansa yake sunkuye yana Fama da fartanya, yace “ga Babban yayansu Nan nasashi aiki, kuduba kuga qwanjinsa fa, inda zai haqura da wannan tamolar ya dawo Nan mudinga noma Aida yaji dadi, dashi kadai zanbarwa wannan gonar ya nome min ita, haba meza’ai da wata tamola” ☹ï¸ya qarasa maganar yana yatsina fuska
Shide Babban Yaya baice komai ba, Sai abokan baba Habu dinne dasuke dariya dakuma su Sa’ad
Baba Habu yasake Kallan sa yace “kunji yayi shiru kamar salihi, Nan kuwa qungurmin tuzuru ne”
Babban Yaya baice komai ba yanzun ma, Shide fatansa yarabu da wannan tsohon lafiya, abokan nasa ne sukace “ai yanada Hankali, yanzu awannan zamanin ba kowanne Yaya ne zai debo qannan sa yakawo su ganin dangi ba”😂
Baba Habu yace “Eto tanan Kuma yayi qoqari”
Ya kalli Babban Yaya yace “dago haka, muje gida muci abinci kun debo hanya”
Sai a lokacin Babban Yaya yadago, fuskar Nan tasa a daure, babu wasa, haka suka tafi gida, yanbiyu da Waheeda suka zubawa kowa abinci, duk da yaran baba Habu suna zaune aqauye ne hakan baya Hana ganin tsantsar kamar dasuke dasu Babban Yaya, kana ganinsu kaga jini daya.
Baba Habu ya kalli Babban Yaya yace “Ai kamata yayi daga Nan kunufi gida can Niger, can ma kuje kuga yan’uwa”
Sani yayan Yahya yace “qwarai Kam baba, kaga Yan biyu da Waheeda ma Sai suhau a male, nasan basu taba Hawa ba”
Babban Yaya yace “saide wani lokacin baba, saboda makarantar su, idan aka musu hutu, Sai muje”
Uzurin daya basu ne yasa suka amince da maganar tasa, Amma badan makaranta ba, yasan Sai sunje.
Washe gari suka fita ganin gari da safe, Waheeda wani Riga da wando tasaka, kayan sun kamata sosai, amma data saka dogon hijabi babu Wanda yake ganin ta, sunga gari sosai, sune har Rafi ganin ruwa, su Sa’ad suna tareda su Yahya, shikuma Babban Yaya yana bayansu Waheeda yana tafiya yana danna wayarsa.
Fakar Idonsa Waheeda tayi, tacire hijabin Nata,hips dinta yacika wandon taf, sannan ta tattare qafar wandon, tashiga ruwan tafara wasa, suma yanbiyu da sukaga Babban Yaya hankalinsa yana kan waya suma suka shiga, dago Kansa yayi ya gansu suna wasa, bece musu komai ba yanemi waje ya zauna yaci gaba da abunda yake
Cikin tashin Hankali yanbiyu suka fara Kiran sunansa, suna nuna masa Waheeda, yana dago Kansa ya hango Waheeda acan tsakiyar ruwa tana mututuwa idonta Sai juyawa suke ruwa yana gaba da’ita, baisan lokacin da yayi jifa da wayar ba, ya qwala mata kira, sannan yanufe ta da gudu
Yanbiyu suka futo da gudu sukayi wajan su Yahya da Sa’eed zasu fada musu
Batare da tunanin komai ba, Babban Yaya yafad’a cikin ruwan, kafin ma ya qarasa wajan ta hartasha ruwa ta suma, d’aukota yayi tamkar ya dauki jaririya
Cikin tashin Hankali yafara tatta6a jikinta yaji shiru, jikinsa ne yad’auki rawa, fuskarta yakama yariqe yana fadin “ke! ke!! Dan Allah karki tafi”
Jijjigata yake yana fadin haka Amma Waheeda shiru ko motsi takasa, gaba d’aya yanemi nutsuwar sa Yarasa, gabansa yafara fad’uwa kana Kallan faffad’an qirjinsa zaka tabbatar da haka, ta hanyar bugun zuciyar sa, shiru yayi yarasa abin yi, tunani yayi Ana danna cikin Wanda yasha ruwa, yasaka hannunsa akan shafaffan cikinta ya danna Amma ruwa be futo ta bakinta ba, zuciyarsa ce take bashi wata shawara yana yakicewa, daga qarshe Sai ra’ayin zuciyar tasa yabi, saida ya qarewa lallausan pink lips d’inta kallo, sannan ahankali ya sunkuya yahad’e bakinsu waje d’aya🙆ðŸ»â€â™€ï¸?
Duk yanda zuciyarsa take gargad’insa akan kar yayi komai Bayan iska dazai hura cikin bakin Nata, hakan bai samu ba, laushi da Kuma santsi irin na lips din Waheeda ya d’ebeshi yafara kissing dinta,wannan ne Karon farko daya ta6a kissing din mace a rayuwar sa,wani irin dad’i yaji sosai,saida ya tsotsi lips dinta son ransa, sannan yahura mata iska cikin bakinta da qarfi, sannan ya d’auke lips d’insa daga kan Nata.
wani irin Tari ne yataso mata, a Hankali tafara bud’e idonta, harta bud’esu gaba d’aya, ta d’orasu akan Babban Yaya daya zuba mata ido yana Kallan ta, babu Wanda ya tankawa d’an’uwansa acikinsu, Sai ido dasuka zubawa juna, kowa yana tunani cikin Ransa, tsantsar kyawun dan’uwan Nata take kallo, haqiqa yahad’u harya gaji da had’uwa, shi abin sone ta kowanne fanni,ita kanta tana sarawa yayan nasu wajan iya Gayu dakuma d’aukar wanka.