BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari yafuto daga d’akin nasa, yana Sanye da kayan ball, suma ‘yanbiyu maza shine ajikinsu, zama sukai afalo kowa yana kokarin saka safa, yanmatan ne suka futo daga d’akinsu suma de kayan Ball d’inne ajikinsu, Amma nasu wandon dogo ne, rigar ma me dogon hannu ce, sa6anin na mazan dayake qanana, fita sukai zuwa filinsu na qwallo dayake gidan, shikuma Babban Yaya yana falon yana saka takalmin sa, gaba d’aya iyayen nasu suna compound suna shan shayi, da hajiya Anty da Ummah dakuma Daddy da Uncle Usman, akan idonsu yaran suka futo zasu fara buga Ball din, Amma babu Babban Yaya, a lokacin harya gama saka kambos dinsa, yana zaune ne yana amsa wayar Abokinsa dayake tambayar sa yaushe zai dawo, yana gama waya da abokin nasa wata wayar tashigo, yayi mamaki da’aka kirashi ta wannan number, saboda ba kowane yasan wannan number tashi ba, dauka yayi tareda sallama daga dayan bangaren akace “Yayanmu Ina wuni? Sunana Didat, qanwarka ce tabani number ka,Ina neman alfarma ne awajanka, maganar Gaskiya Ina sonta, idan kabani Dama inaso na nemi aurenta”
Babban Yaya ya Sosa girarsa guda d’aya yace “Sister na kuma?”
Daga d’ayan bangaren Didat yace “eh Yayanmu, na gansu ne abakin get d’in school d’insu, akwai mutum biyu masu kama d’aya, toba suba, d’ayar nake nufi”
Babban Yaya yana jin haka ya Lumshe Idonsa, cikin ransa yace “Waheeda”
Dafarko har yayi niyyar dakatar da Yaron, but Saiyayi tunani tayaya rayuwa zataci gaba da tafiya Ahaka? Yaushe ne zai daina hanata huld’a da samari? Duk Daren dad’ewa dole zatayi aure, wazai fara fuskanta da maganar datake damunsa?qalubalen dazai fuskanta akan haka ba d’an qarami bane, Kuma itama da alama sonsa take, tunda gashinan ta yarda harta amince a tambayeshi? Cikin Yan seconds yayi wannan tunanin, wani irin huci yayi yafitar da iska me zafi daga bakinsa sannan yace “Babu damuwa zaka iya zuwa”
daga Nan yakashe wayar tashi yafita zuwa compound da d’an gudunsa irin na ‘Yan qwallo, acan Gefe ya hangi su Ummah sun baje suna shan Shayi, yana zuwa kuwa suka fara buga ball din mazan da matan, kusan mintuna talatin suka d’auka sunayi Amma Babban Yaya baici ko sau d’aya ba, mamaki ya kama iyayen nasu dasuke Kallan abinda yake faruwa, shida a qasar waje ma suke alfahri dashi akan iya ball, tayaya wad’annan yaran zasu dinga cinsa? Ada idan sunayin ball d’in kowa saduda yake, saboda sunsan comfirm ‘Yan team din Babban Yaya sune da nasara, Amma yau Sa’ad da Babban Yaya, da intisar Sai sunci su Waheeda da Ihsan da Sa’eed suke yi.
Sunkuyawa yayi yariqe gwiwarsu, damuwa tataru tamasa yawa, idan ya tuna da maganar Ummi, yatuna da wayar da gayen Nan yamasa akan Waheeda, saiyaji gabansa yafad’i, daga qarshe ma kawai juyawa yayi zuwa falon su, intisar datake jin haushi anata cinsu, tayi sauri ta hura Whistle tace “wasa yatashi” 😂
Akan idanun iyayen Babban Yaya ya wuce falo yabar yan’uwan nasa, Waheeda tariqe hips d’inta cikin damuwa tana Kallan sa, daga Nan tabi bayansa, saide tana zuwa ‘kofar ‘Dakin nasa tayi nocking din duniya yaqi bude mata, dole Sai haqura tayi, ta wuce dakinsu.
Washe gari da yamma Ummah tana zaune ad’akinta tana tunani akan rayuwar Naufal, damuwar dayake ciki haqiqa itama tana ciki, yaqi yafuto fili yafad’a mata me yake tsoro dangane da aure a matsayin ta na mahaifiyar sa, duk sa’anninsa sun dad’e da aure, Sai yaushe ne shi zaiyi? Tun yanda ta ganshi jiya cikin damuwa har yanzu Hankalinta yaqi kwanciya, duk yanda yake dason Ball yamaqi yakoma bare tace ball din zata d’ebe masa kewa, Waheeda ce tashigo Dakin tana Sanye da dogon hijabi tace “Ummah zanje bakin get nayi baqo”
Ummah ta kalleta tace “Baqo kuma? Daga Ina kenan?”
Murmushi tayi tace “shekaran jiya nahad’u dashi abakin get din school dinmu, sunyi waya da Babban Yaya ma, shine yace yazo”
Ummah tace “kin tabbatar abinda kika fad’amin gaskiya ne Waheeda yayanku yasan da maganar sa?”
“Allah Ummah yasani”
“to shikkenan kije, Amma karki dade” cewar Ummah
Waheeda tafuto daga d’akin, ta qarasa wajan Didat, yana Sanye cikin shadda Light blue, hular daya saka ta dace da kalar kayan nasa, qarasa wa tayi tareda sallama, ta ajiye masa ruwan roba guda biyu da Lemo guda daya, baba maigadi yataso da sauri yasake gaida shi, sannan suka qarasa wajan wasu kujeru masu kyau Wanda aka qawata wajan da yar qaramar rumfa domin shan iska, Didat ya kalli Waheeda Bayan ya zauna yace “Ranki yadade gimbiya”
Waheeda tace “mudade tare”
Murmushi yayi yace “bakice nayi kyau ba, Bayan duka wankan naki ne, kinsan kafin nafuto daga gida saida nafadama mamana wajanki zanzo, tace nayi kyau sannan tana miqa saqon gaisuwar ta zuwa gareki”
Tace “nagode sosai, Ina amsawa, idan kakoma kace ina gaisheta”
“zataji insha Allah,ni sunana Didat”
Tace “nikuma Waheeda”
Kallan ta yayi yace “sunanki yanada dadi Waheeda, Ina fatan ace kin zamo wani bangaren na cikin rayuwa ta idan kin amince”
Tace “kamarya?”
“Ina nufin kibani Dama Nima adama Dani acikin Jerin masoyanki, Amma maganar gaskiya itace inada kishi sosai akan abinda nakeso, shiyasa ma nakawo miki wannan kyautar”
Yafadi haka yana bata wata leda, saida ta karba Sannan yace “hijabi ne da niqab, dakuma safa, gaskiya Ina kishinki Waheeda, aurenki nakeson yi bawai soyaiya ce ta kawo ni wajanki ba, banaso muyi shekara daya batare da munyi aure ba”
Murmushi Waheeda tayi tace “gaskiya ne, nayarda kanada kishi, tunda gashi kyauta ta farko daka fara min itace da hijab da safa da niqab, Amma Kuma duk kishinka baka Kai Babban Yaya ba” 🙆ðŸ»â€â™€ï¸ðŸ˜³ðŸ™?
Cikin mamaki ya gyara zama sannan ya kalleta yace “waye Kuma Babban Yaya?”
Murmushi Tayi tace “nasan cewa kasan Big Brother ko?”
Yace “sosai ma kuwa, waye zaice baisan Shiba? Aini shine ‘Dan qwallon dayake mugun birgeni”
Tace “to shi nake nufi, ai shine Babban Yayanmu”
Didat yace “ok, Allah sarki, haba shiyasa Naga gidanku unguwa guda gashinan aljannar duniya” yafad’i hakan cikin sigar tsokana
Waheeda tace “Shima yanada kishi, yafi son muyi karatu karmu kula samari”
Yace “ya kyauta min, inda yabarku Aida Nima bazan sameki ba, nasan da tuni wani alhajin ya dauke ki”
Murmushi tayi tace “nagode, zan koma gida, Ummah tace karna dad’e”
Shima tashi yayi tsaye, ya ajiye mata rafar kudi Yan hamsin hamsin guda daya, aqalla zasu Kai dubu hamsin, daqyar da Fama Waheeda ta d’auki kudin, sannan suka rabu akan zai sake dawowa gobe ko jibi, tanada son kudi Amma Bana hannun mutane ba, saide na Babban Yaya, tasan yayanta ne bazai taba goranta mata a kan hakaba, abinda ta lura dashi shine, shi mutum ne me kishi kamar yanda yafad’a, sannan daga Gani bashida matsala ko kad’an
Da daddare gaba d’ayansu suna zaune banda Daddy, Ummah ta kalli Babban Yaya dake danna waya yana qara Bawa Corch dinsu hakuri akan dad’ewar da yayi,Kallan Ummah yayi yace “Ummah nanda kwana hudu yaran Nan zasu tafi Umarah insha Allah, gaba d’ayansu”
Cikin farinciki Ummah tace “Alhamdulillah, Allah yayima Albarka, to Allah yakaimu lokacin, Kai banda Kai ne?”
Girgiza mata Kai yayi sannan yace “su kad’ai”
Ummah tace “To madallah, Allah yaqara hore Maka,”
Murna suka hauyi gaba d’ayansu, Nan take suka fara zuba masa ruwan godia, Waheeda kuwa jitake kamar taje ta rungume shi Dan murna, Amma babu Dama yanda taga ya d’aure fuskar Nan tana zuwa kusa dashi tsaf zai maketa 😂