BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummah ta sake Kallan sa cikin farinciki sannan tace”Yauwa yayansu ga wannan kud’in, saurayin Waheeda ne yabata dazu”

Kallan kudin yayi Asheqe sannan yace “ok”

Ummah tace “bangane Okay ba, bazaka kar6a kasa mata Albarka ba?”

Yatsina fuska yayi yace “Ummah dubu hamsin d’in kamar Wanda yayi kyautar bajinta?” ☹️

Mamaki yakama Ummah, sukuwa su Sa’eed dariya suka saka, Sa’ad yace “haba Babban Yaya, dubu hamsin fa, kodan Kai mekud’i ne shiyasa, wallahi Ummi tahuta”😃

Wani irin banzan kallo yamasa, lokaci d’aya yashiga taitayinsa

Kafin su qara cewa komai wata yarinya ‘yar kimanin shakara 11 tashigo da sallama hannunta d’aukeda wani flask na abinci, ta tsugunna ta gaida su Ummah sannan tace “Wai gashi inji Anty Ummi abawa Yaya Naufal” 😅

Haushi yakama Babban Yaya, ya kalli yarinyar yayi tsaki a ransa, ko’ina ya zama yayanta harda wani Yaya Naufal,?

Ummah ta saki ranta tace “Allah sarki, to kice ya gode, zai kawo mata kular da Kansa kinji, Allah yamiki Albarka,”

tad’auko fos dinta dake Gefe tabawa yarinyar dubu biyar, yarinyar cikin murna ta karba tafice daga falon

Waheeda ce tataso tabud’e flask din taga abinda yake ciki, sannan tayi murmushi ta kalli Babban Yaya tace
“Babban Yaya farfe….”

kafin ta qarasa cewa farfesu ne, yatashi cikin fishi, yabar falon gaba d’aya, Ihsan da intisar suka zabgawa Waheeda harara suma sukai d’aki, Waheeda ta kalli Ummah cikin shagwa6a kamar zatayi kuka, Ummah ta janyo ta jikinta tace”rabu dasu, idan sun gama fishin zasu sakko”

Washe gari da safe, suna break fast, wayar Daddy tayi qara, yayi mamakin me Kiran nasa, domin kuwa ba kasafai suke waya da minister of Education ba, d’auka yayi Bayan sun gaisa, Daga d’ayan bangaren minister Abdullahi Wakili yace “Alhaji Umar Arabo”

Daddy yayi murmushi yace “ranka yadad’e, kwana dayawa ba’a jinka”

Minister yace “wallahi kasan koda yaushe muna ta Fama da jama’ah, yanzu ma yarona ne Huzaifa yasaka ni agaba lalle lalle saina kiraka”

Daddy yace “a a ikon Allah, Huzaifa ya dawo qasar ne?”

Minister yace “wallahi ya dawo, cikin ikon Allah ya kammala karatun sa lafiya ya dawo, yazo ya sameni ne akan maganar ‘yar wajanka, last week yaje ‘Dauko sisters d’insa daga school sunyi party na candy, anan yaga yar wajanka Waheeda yace yanaso, shine da yayi bincike yagano ‘yarka ce, Kuma kasan akwai sanaiya a tsakani, shine yace ayi masa tambaya aji ko an yiwa wani alqawari? “

Daddy yace”A a babu alqawarin kowa, Allah ya tabbatar musu da alkhairi “

Daga d’ayan bangaren minister yayi godia tareda kashe wayar

Babban Yaya yanajin wayar da Daddy yake jikinsa yabashi akan Waheeda ake magana, Bai nuna komai akan fuskar saba, lafiya kalau suka gama cin abincin sannan ya dauki key din mota yafice daga gidan

Da yamma Didat yazo tareda abokinsa Mukhtar, yau wankan qananun Kaya yayi, ba qaramin kyau yayi ba, suna cikin zance da Waheeda yace “Gimbiya inaso kije gida ki fad’awa Ummah zamuje shopping idan ta amince”

Babu musu Waheeda ta wuce gida ta fad’a wa Ummah abinda Didat yace, Ummah tace “to karki tafi ke kad’ai, kuje keda yan’uwan ki”

‘Dakinsu ta wuce, ta tarar Ihsan na wanka, Sai intisar dake karatu, tare suka futo da intisar basu jira Ihsan ba, suna zuwa kuwa Didat yace “lalle babbar Yaya, yanzu ashe Kuna ciki kun 6uya, ko sau d’aya bantaba ganinku ba”

Intisar tace “Wallahi muna Nan, abubuwa ne sukai yawa, yakake”

“Alhamdulillah, Ina lafiya kamar yanda gimbiya Waheeda take, dafatan de tare dake zamuje shopping din?”

Intisar tace “babu damuwa muje”

Tsayawa sukai suna jira yabud’e musu kamar yanda Babban Yaya yake musu, shikuma harya shiga motar, saida yajuya ya gansu a inda suke sannan yayi murmushi yazo ya bud’ewa Waheeda gaba, intisar Kuma suka zauna Abaya tareda abokinsa, suna hanya abokin Sai Jan intisar yake da zance, tana amsa masa kad’an kad’an, a wajan shopping d’inma Didat Kam kawai binta yake yana aikin kallon ta kamar wani sakarai, itace me za6ar komai, saida yakashe mata kud’i me yawa sannan suka Juyo gida, tun a hanya yaga tana amsa masa daqyar, Sai yatsina fuska take, suna qarasa wa gida kuwa intisar tayi ciki, ita Kuma Waheeda ta tsaya suna sake tattaunawa, Kallan ta yayi yace “Meyake damunki ne? Naga kamar bakya jin dadi”

Yatsina fuska tayi tace “wallahi jinake zazza6i yana son kamani”

Cikin rud’ewa Didat yace “Subhanallah, Amma shine kikai shiru? Meyasa baki fad’amin ba muje Asbiti?”

Tace “Babu damuwa, zansha pracitamol agida”

Didat yace “no, ga Mukhtar Nan yayi miki injection mana, akwai saura acikin motata Ina siya Dama saboda 6acin rana, idan kikaje gida saiki kwanta kihuta, Shima doctor ne”

Cikin damuwa Waheeda tace “no, karka damu wallahi”

Didat yace “a a, tsaya yayi miki please”

Bud’e motar yayi, ya ‘Dauko allurar yabawa Mukhtar, Mukhtar ya kar6a yafasa ruwan allurar, ya kalli Didat yace “Ina sirinji?”

Didat yace “aikuwa na manta wallahi babu, but ga Wanda akamin allura dashi ban yarda shi ba, kayi mata dashi kawai”🙆🏻‍♀ï¸?

Kallan Waheeda Mukhtar yayi yace “babu damuwa ayi miki gimbiya?”

Tace “babu damuwa”

Kar6ar sirinjin yayi yazuqe ruwan allurar, sannan yayi mata a hannunta, basu qara ko minti biyar ba, sukai sallama, tajuya zata tafi gida, adede lokacin Babban Yaya ya dawo gidan, fuskarsa ad’aure take babu wasa, ya gansu Amma saiya nuna baima gansu ba, Didat da baisan da shigo war Babban Yaya ba, ya qwalawa Waheeda kira, tana juyowa yayi kissing hannun sa, sannan yahura mata tareda kashe mata ido, yashige cikin motarsa

Babban Yaya yana Kallan su, yakashe motarsa Bayan ya ajiye ta a parking space yafuto, adede kofar shiga falon suka had’u da juna, cikin ladabi tace “Sannu da zuwa Babban Yaya”

Cikin 6acin rai yace “aikece za’ayi wa sannu,mahaukaciyar banza mahaukaciyar wofi, Kin tsaya yana miki hauka Amma ko ajikinki, kwata kwata bakya kishin kanki, idan kikai wasa naqara ganin qafar Yaron Nan a gidan Nan saina kakkarya qasusuwanki ….”

“Subhanallahi …. Naufal?”
Cewar Hajiya Anty da shigowarta kenan taga yana zazzaga wa Waheeda masifa

Kallan ta yayi, yayi qasa da Kansa, idanun Nan nasa sunyi jajir tsabar 6acin rai, Sai huci yake kamar zai Fashe, ita kanta hajiya Anty ta tsorata da yana yinsa, ta kalli Waheeda datake share hawaye tace “Ke wuce ciki”

Kallan sa tayi tace “Kayi hakuri” sannan ta wuce cikin falon nasu

Hajiya Anty ta kalli Babban Yaya tace “yanzu bakaji kunya ba? Kagama yimata fad’a Amma daga qarshe haquri take baka ko kallo bata isheka ba? Hakan dakayi daidai ne kenan?”

Yace “Anty kissing dinta fa yayi” yayi maganar kamar zai Fashe da Kuka

Hajiya Anty tace “to naji tayi laifi wannan fad’an dakake mata shine zaisa ta nutsu? Qanwarka cefa, jininka ce tayaya bazakaja yarinya a jikinka ba zakadinga mata fada irin haka,?to tun tana jin tsoron ka, watarana zata daina, kaja Qanwarka a jikinka kaji nafada ma, fad’a ko duka basa shiryar da yaro”

Qwalla ce take son futowa daga idanunsa yana dannewa, idan yatuna yanda Didat yake huro mata kiss, jiyake kamar yayi ihu, cikin 6acin rai yace “Anty niba qanwata bace, kidena cewa Qanwata”

Hajiya Anty tayi sakare tana Kallan sa, a fili tace “ikon Allah, to ba Qanwarka bace, karka jata a jikinka, gata Nan ka kashe ta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button