BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin tsiwa tace”wallahi yanzu nafara saka hijabi saide in bangani ba, baki Isa kimin in qyale kiba intisar”
Anty Maryam tace “Waheeda kanki daya kuwa? Dama rashin kunyar Taki haryakai haka?”
Ihsan tace “rabu da’ita Anty, ai taga kanmu daya ne,Mp muke itama shi take yi, brezia muke sakawa itama shi take sakawa,taga ta girma tafimu nonuwa, tayi tsawon qafa, Gani take shekarunma daya muke da’ita, yau kuwa zakici ubanki, zaki San kin mana rashin kunya”
Tashi tayi tsaye ta kallesu ta watsar tace “ai Dama ba yau kuka fara hademin Kai ba, Naga su Sa’ad ma qarewa, balle ku Yan biyun qarshan zamani, qarqari kumin taron dangi kumin duka, to bazaku birgeni ba saikun kasheni kun kaiwa uwata gawata”
Anty Maryam tatashi tsaye tace “lalle Waheeda kullum girma kike kina sake zama marar kunya, zan fadawa ummah abin naki yayi yawa, yanzu har takai su Yaya Sa’ad ma sunansu kike fada” tana fadar haka tafice daga Dakin cikin fishi
Ihsan ta kalli Intisar, basu tsaya wata wataba suka rufe Waheeda da duka, intisar takama gashin ta tanaja, Ihsan kuwa Sai dukanta take, dama haka suke, hadin kaine dasu sosai, duk lokacin da Waheeda tamusu rashin kunya haduwa suke suyi mata shegen duka
Hajiya Anty ce tashigo gidan, tana Sanye da kayan likitoci komai fari, tana Sanye da glass fari a’idonta, kana ganinta kaga mace yar Gayu, da alama daga Asbiti take wajan aikinta, da kukan Waheeda tafara cin Karo, Kai tsaye Dakin nasu ta nufa, ‘Yan biyu suna ganinta suka daina Dukan Waheeda, haka tadago kanta idonnan yayi jajir tace “Kuma wallahi saina Rama, bashi kuka dauka”
Hajiya Anty batace dasu komai ba taja Dakin tarufe, tawuce wajan ummah, Sai a lokacin ummah tashigo Dakin nasu taji ba’asin fadan, da alama Hajiya Anty ce ta turo ta, Dan lokacin dazata shiga Dakin nasu ma mita take tana cewa fitinar Waheeda ta isheta☹ï¸
Da yamma sukai baqi daga qauye, a lokacin hajiya Anty tana nan bata tafi ba, megadi ne yayi musu jagora har cikin falon gidan, Anty Maryam de Takoma gidanta, Amma gaba dayansu yaran suna Nan, ‘Yan biyu suna zaune waje daya suna ganin wani abu a wayar ihsan, Waheeda kuwa tana zaune agefe cikin kujera ita daya, tunda ‘yan’uwan suka daketa taketa kumburi, taso ace ummah da Hajiya Anty basa Nan, dasai tahada wa ‘yanbiyu wata muguntar da bazasu taba mantawa da’ita ba, yanda ta zauna waje daya tayi shiru zaka rantse wata kamilar yarinya ce, saboda ta nutsu sosai kamar ba’ita ba,itace tafara tashi takawo musu lemuka da ruwa, sannan ta gaishe su, aikuwa suka amsa cikin girmama wa, tasake komawa wajan zamanta ta zauna, Ummah takalle su cikin sakin fuska tace “Saide kuyi hakuri fa, Amma bamu gane Kuba”
Namijin ne yafara dariya yace “Hajiya ai ‘yan’uwan kune daga wani gari Kaburma, ai Alhaji Habu ne yace duk lokacin da muka shigo Garin naku, mu qaraso mu gaisa nida iyalina, aini kamar qani nake awajansa” yafadi maganar yana Kallan Waheeda
Waheeda ta Kalle shi dakyau, Bama qanin bane kenan, kama ce, tunda yace kamar qani yake a wajan Baba Habu, Kai Shima de Baba Habu da yayime-yayime yake, ita Kuma umma Sai washe musu baki take
Hajiya Anty tace “Amma kun kyauta wallahi, ai Gara daban wuce gida ba, yanzu gashi munga juna”
Matar datake gefen namijin tace “Eh wallahi, ai Baba Habu akwai zumunci, Amma wadannan Yan biyu ne ko?”
Ta qarasa maganar tana Kallan Yan biyu
Dariya sukayi sannan suka amsa mata, Tajuya tasake Kallan gefen da Waheeda take zaune tace “kekuma fa qawata kinyi shiru babu ruwanki da kowa”
‘yanbiyu ne suka hada ido suka kwashe da dariya, Wai Waheeda ce babu ruwanta, shine abunda ya basu dariya
Matar tace “yakuke mata dariya, ai Naga tayi shiru da alama zatayi hakuri,qawata ya sunanki?”
Waheeda tayi murmushi tace”sunana Waheeda”
Kallan mijinta tayi tace “Baban Halima kaji suna me dadi, idan nasake haihuwa Nima ka sakawa yarmu irin wannan sunan”
Dariya yayi, ya kalli Yan biyu, ya kalli Waheeda, yace “yanzu Nan duk ‘ya’yanane?”
Dariya sukayi kawai, babu wadda tace masa komai, yace “toku Yan tagwaye wayece babba acikin ku?”
Ihsan tace “nice babba, Sai Intisar, Sai qanwarmu Waheeda”
Washe baki yayi yace “ikon Allah kenan, toke ashe kece Gambon su”
Waheeda tace “Uhm…” Daga Nan tatashi tayi daki
Matarsa tace “Allah sarki, kunga ita tatafi daki ma babu ruwanta baiwar Allah, Baban Halima Bari naje wajanta musha hira”
Tatashi tabi Bayan Waheeda, duk yanda taso share matar hakan bai iyu ba, Dan dolenta tasaki jiki da’ita suka Sha hirarsu, Sai yamma lis suka tafi, Hajiya Anty taje gidanta takawo wa matar atamfa da kudi, ummah Kuma tabasu kayan abinci sannan tasa driver yamaidasu har gida.
Da daddare suna zaune afalo gaba dayansu, Ummah da Yanbiyu maza Wanda suke bin Babban Yaya, Sa’ad da Sa’eed,, saikuma yanbiyu mata su Ihsan, kowa Assignment dinsa yakeyi, mazan ne daya yana kallo a TV daya yana danna wayarsa, Sa’eed ne ya kalli Waheeda yace “ke tashi ki daukomin bread a kitchen, yana Nan akan fridge”
Hankalinta yanakan rubutun assignment dinta tace “qarami ko babba?”
Lokaci daya shida Dan’uwan nasa suka kalleta, mamaki ya kama Sa’eed, harshi zai aiki yarinyar Nan Amma tana tambayar shi qarami ko babba?
Miqewa yayi tsaye yanufeta, tana dago kanta ta ganshi yanufota tatashi da gudu tayi kitchen, yanda take gudun yasa dogon gashin kanta yake bazuwa a fuskarta,hips dinta kuwa Sai rawa yake, haka tadinga tsaki cikin ranta, saboda bata so idan tana tafiya taji suna rawa
Waheeda kyakykyawa ce ta qarshe, tanada kyau Wanda kallo daya zaka mata kagano hakan,duk cikin yan’uwanta tafi kowa kama da Babban Yaya, yanda yake magana dimples suna futowa haka itama, musanman idan tayi dariya, kana ganin ta ka ganshi, shiyasa ko ba’a fadaba inde kagansu basai ka tambayi waceba, kaima kasan jininsa ce, kamar su tayi yawa, saide basa zama inuwa daya, baya sakar mata fuska, inde tayi laifi tana ganinsa jikinta yake rawa, saboda tasan watan azabar ta yakama, tayi laifi yakamata ya daketa hakan bazai Hana gobe tasake yin wani laifin ba,babu Wanda bai Santa ba a school dinsu, kana cewa Waheeda Virus za’a nunama ita, wannan shine Nikname dinta, dazaran tayi laifi anyi mata hukunci batada wata Sara saide tace baza’a birgeta ba Sai an kashe ta ankaiwa Ummah gawarta 🤣, Amma bata taba fadawa Babban Yaya ba, saboda tasan karonsu babu dadi, Amma yasani Sarai tana fadawa mutane hakan.
Waheeda tanada kyawun sura, hips dinta da breast dinta yafi qarfin shekarun ta, harma tafi yan’uwan Nata, Kuma tana tafiya suna rawa, sauqin ta daya dokar da Babban Yaya yakafa musu tasaka hijabs.
Washe gari Sunday babu makaranta, gaba dayansu suna tareda Ummah a kitchen suna hada breakfast, gaba dayansu tasosu take su shiga kitchen tare, wani lokacin Kuma tabarsu su kadai suyi, wayar Ummah ce tafara qara, tana dubawa taga Baba Habu ne daga jigawa yake kiranta, cikin mamaki tace “Yaya Habu da wannna safiyar lafiya kuwa?”
Dauka tayi, Bayan sun gaisa yace “munyi magana da Malam Iliyasu, Dan kaburma, Wanda naturo su suka kawo muku ziyara jiya, yayimin waya yanaso abashi auren gambo”
Umma duk saita kasa gane kan maganar tasa, tace “Wacece gambo Kuma Yaya?”
“gambo nawace daku Binta? Gambo de qanwar yanbiyu, Waheeda, yacemin yanaso abashi ita yaqara ta biyu”