BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kafad’a ya d’aga yace “shikkenan tunda haka kika so” daga Nan yatashi yafita daga falon yayi waje domin Nemo musu abinda zasuci

Tana ganin fitarsa tatashi ta dinga zagaye gidan tana santinsa, wayar Ummah datake hannunta ta kalla tasaki wani irin murmushi, ko Yaya suka qare agida? 🤔

*** *** ***

Ahaka Daddy yashigo yasamu Ummah ta zabga tagumi tana sharar hawaye, ga yanbiyu agefenta suna bata haquri, ganin shigo war Daddy yasa suka tashi suka nufi d’akinsu

Daddy ya kalleta yace “mekuma yafaru kike kuka Hajiya?, inata Kiran wayar ki Amma najita a kashe”

Hawayen ta share tace “wayar tana hannun Waheeda”

Cikin mamaki daddy yace “to Ina ita Waheedan take?”

Girgiza Kai tayi tace “bansan inda take ba, Amma megadi yace sun fita tareda yayansu, shikuma munyi sallama dashi zai koma England, bansani ba ko tare suka tafi”

Kafin yabata amsa hajiya Anty tayi sallama cikin falon tashigo, zama tayi Bayan sun gaisa da Daddy tace “Anga Waheedan?”

Ummah tace “ba’a ganta ba,tana tareda yayansu”

Hajiya Anty tafara kokarin Kiran Naufal, Amma wayar taqi shiga, haka ta haqura, bata dade da zama ba tatafi gida saboda Daddy yana Nan tace zata dinga try ko wayar zata shiga

Ummah naganin fitar Hajiya Anty ta kalli Daddy sannan ta zayyane masa komai babu abinda ta rage akan wayar dataji Waheeda tana yi.
Daddy yadafe Kansa yace “ita Waheedan ce tafad’i haka?”

Ummah ta ‘Daga masa Kai alamun hakane, cikin damuwa yace “Hajiya, yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba, tun kafin yarinyar Nan ta lalace Gara ayi mata aure, zaifi sauqi”

Ummah tace “Nima abinda nayi tunani kenan, amma muddin mukai ido hudu da Waheeda sainasa Sa’eed yayi mata Dukan tsiya, duk inda suka tafi ai zata dawo”

Daddy yace “matsalar yarinyar Nan bame qarewa bace, Allah yasa de yanda take fad’a a wayar bawani tata6a yiwa hakan ba” 😖😂

Cikin jimami Ummah tace “Amin”

*** *** ***

Anan falon ya dawo ya sameta, hannun sa d’aukeda ledoji, ajiye mata yayi yazube akan kujera, duba kayan tafarayi, leda d’aya ta abinci ne daya siyo musu, d’ayar Kuma kayane yasiyo mata nasaka wa, abincin ta zuba sannan Shima tazuba Masa nasa, saukowa yayi daga kan kujerar yaja Nata abinci yafara ci, Kallan sa tayi cikin mamakin abinda taga yayi tace “Babban Yaya ga Naka fa”

Wani irin kallo yayi mata Mai d’auke da ma’anoni, sannan yace “ni wannan nake son ci, kisa hannu muci”

Babu musu tasaka spoon din tafara cin abincin, wani abincin ya ‘Debo a spoon me yawa, yaci ‘Dan kadan, sannan ya nufi bakinta da sauran, yace “meyasa bakyaci dayawa ne?”

Murmushi tayi tace “Babban Yaya ai kaima haka, bakaci”
tafadi hakan tareda bud’e bakinta, babu musu yasaka mata,haka ya dinga yimata, Sai yaci kad’an saiya bata sauran, Waheeda bata d’auki hakan da wata manufa ba, zuciyar ta d’aya take cin abincin dayake bata, Kallan bakinta yake yanda take tauna abincin cikin nutsuwa, yanda lips dinta suka hadu da maiqon Mai suke wani irin shinning, Sai hankalin sa yafara tashi, yatuna ranar dayayi kissing d’inta

Jiyake inama ace ita d’in tazama mallakin sa? Da babu abinda zai hanashi kasacewa da’ita a wannan Daren, yamaidata cikakkiyar mace, ajiyar zuciya yasauke, ya kawarda wannan tunanin daga cikin ransa, tashi yayi yanufi d’akinsa ba tareda yace mata komai ba.

Yana zuwa ‘Dakin shirin wanka yayi, ya wuce toilet ya watsa ruwa tareda d’auro alwala, ‘Dakin tashigo hannunta d’aukeda ledar kayan daya siyo mata, ganin zaiyi sallah tayi saurin ajiye ledar tashiga toilet ta d’auro alwala tazo ta bishi, saida suka idar sannan tashiga wanka, shikuma yacire jallabiyar jikinsa ya kwanta akan gadon dagashi Sai gajeren wando, tareda ‘Dauko wani diary yana rubutu aciki cikeda damuwa, daga shi har Waheeda babu Wanda yake tunanin Kiran Yan gida😂

Futowa tayi daga wanka tana Sanye da rigarta ta bacci, turare kawai ta fesa tanufoshi ta zauna aqasan kafet din, shikuma yana kan gado ya rungume diary din a qirjinsa, Kallan ta yayi yaga tasa shi agaba tana aikin kallon sa kamar tasamu TV harda tagumi, yace “lafiya?”

Murmushi tayi tace “Babban Yaya wallahi kana birgeni, babu ruwanka da neman tsokana, Kai haka rayuwar ka take, inajin Kai ka haqura da duniya ma” 😳

Kwata kwata baya cikin yanayin farinciki Amma jin wannan maganar Tata Sai dariya ta kamashi yace “na haqura da duniya Kuma?”

Fari tayi da idonta tace “Emana, gashinan to babu ruwanka da shiga harkar kowa, rayuwar ka cikin kwanciyar Hankali”

Juyowa yayi yana Kallan ta, har zuwa lokacin dairy din yana rungume a faffadan qirjinsa, yace “tayaya zan haqura da rayuwa Bayan bansamu abinda nake soba?”

Tace “zaka samu Babban Yaya,nasan saboda me kama da nine kace haka, Bari kaji ai dole ma ka sameta ko tana so ko bata so,nikam yanzu banida damuwar komai”

Yace “Serious?”

Wani iri farrrrrr tayi da Zara zaran gashin idonta, sannan ta ‘Dora hannunta akan qirjinsa tana so taja littafin daya rungume, shikuma yahana, saima Qasan fillo daya turashi ciki

Bata d’auki hakan a matsayin komai ba, batasan cewa baya son taga dairy din bane, batayi tunanin wani abu na sirrinsa yake rubuta wa aciki ba, shiyasa Bata damu da saita ganiba, saita share, saima hannunta data d’ora akan faffad’an qirjinsa take shafa gashin da yayi kwance akan farar fatarsa, sannan tace “I’m serious Babban Yaya, banda damuwar komai, kana tsaya min akan komai,nasan cewa nafi kowa sa’ar samun Yaya me kula da qanwarsa, shiyasa bayansu Ummah da Daddy banida Wanda yafika”

Kwata kwata Babban Yaya baiji abinda Waheeda take fad’a masa ba😂
idanunsa a Lumshe suke, shi Kansa ba zaice ga duniyar dayake ciki ba, wani irin dad’i yakeji yanda take shafa qirjinsa, Waheeda bata lura da yanayin data jefa yayan Nata aciki ba, kawai qirjinsa take shafawa tana wasa da gashin qirjinsa me mutuqar laushi, ahankali tace “Babban Yaya Wai meyasa bakasan aske gashin kirjinka? Yafara yawa fa….”

Babban Yaya baima bud’e Idonsa ba bare yabata amsa, baya so yayi magana ta daina abinda take masa, yafiso taci gaba, Kallan sa tayi taga Idonsa a Lumshe, tayi murmushi tad’auki wayar Ummah data gudo da’ita ta kunna, sannan ta kunna masa tasa wayar, kamar jira ake, tana kunna wayar Babban Yaya kira yashigo da wata number,tsabar nacin da me number take masa ne yasa ya rubuta wa ne number Ummi Nigeria , Waheeda ta janye hannunta daga kan qirjinsa tace “Babban Yaya Ummi Nigeria tana kira, wacece?”

Cikin takaici yabud’e Idonsa, yaji haushin shigo war Kiran wayar, gashinan ta katse masa jin dad’insa, Kansa tsaye yace “Ummi ce”

Cikin murna Waheeda tace “Bari in d’aga mugaisa”

Cikin sauri yatashi zaune yace “kice mata me? Karki d’aga, ni Bana d’aukan wayarta, me kikeso nace mata idan nad’auka?”

Waheeda takama dariya yanda taga ya rikice shi baza’a daga wayar Ummi ba,Sai hakan yasake bata dariya, tace “Toni kabarni in d’auka saimu gaisa”

Ganin zata d’auki wayar yasa yamatso kusa da’ita zai qwace wayarsa,ita Kuma tana ganin haka tahanashi, kokawa suka fara irinta masoya tana d’aga hannunta sama Dan karya qwace wayar shikuma yanaso ya qwace, saura qiris wayar ta katse Waheeda tayi nasarar picking ba tareda ta saniba

Daga d’ayan bangaren ummi tayi gyaran murya tareda lanqwasa harshe tace “Hello Dear”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button