BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da asuba daqyar tayi sallah Takoma ta kwanta, ko Yaya ta motsa jikinta saita runtse ido saboda yanda ko’ina na jikinta yake mata ciwo, qarfe goma da rabi Ummah taga abun na Waheeda gaba yake, tun jiya jiki yaqi dadi, Nan da Nan Kuma Hankalinta yatashi, tasa Sa’ad yakaita Asbiti, yanbiyu ne suka shirya ta suka tafi gaba dayansu.

Suna fita wayar Ummah tayi qara, number tagani, ta dauka tareda sallama, daga d’ayan bangaren akace “Mama Huzaifa ne”

Ummah ta fada da fara’art tace “Au Huzaifa, ashe kaine, ya mutanan gida”

“suna Nan kalau Alhamdulillah” daga Nan Kuma Sai yayi shiru baice komai ba

Ummah data fahimci inda yasa gaba, saitace “Huzaifa Waheedan bataji dadi bane, sunje Asbiti yanzu, Amma idan suka dawo, zata kiraka”

Cikin tsantsar damuwa yace “subhanallah…. Ummah meyake damunta? Suna wanne Asbiti, meyake damunta….?”

Ummah ta jijjiga Kai ganin yanda Yaron yarikice lokaci d’aya, tace “suna wani private Hospital Annoor”

Godia yayi mata, sannan yakashe wayar

(idan kinsan bada yardata kika karanta wannan littafin ba, keda Allah, nabarki da Allah, koba yauba karkizo neman yafiya ta ehe)

*** *** **

suna zuwa Asbitin Waheeda ta yanke jiki tafadi,bayan likita ta dubata tace “yarinyar Nan akwai qarancin jini ajikinta, dole zamu qara mata jini leda d’aya zuwa biyu”

Nanfa hankalin ‘yan’uwan Nata yatashi, Sa’ad ya kira Ummah yafad’a mata halin da ake ciki, cikin tashin Hankali tace “gatanan zuwa”

Gidan Hajiya Anty tatafi, daga Nan suka nufi asbitin, suna zuwa adede lokacin Shima Huzaifa yazo, had’ad’d’en Gaye ne nabugawa a jarida, wankan tarwada ne, yanada tsayinsa daidai misali, kana ganinsa kasan hutu da jin dadi sun zauna masa, tare suka shiga Dakin da aka kwantar da Waheeda, suna zuwa kuwa numfashin ta yafara yin sama kamar zata suma, hankalin Ummah yatashi, Nan da Nan tafara hawaye, Hajiya Anty tace “Haba Hajiya, idan kina kuka sukuma yaran mezasuyi kenan?”

Kafin Ummah tabata amsa tajuya ta kalli likitar tace “doctor me kuke jirana Baku saka mata jinin ba?”

Likita tace “wallahi hajiya bamuda irin jininta, anje asiyo har yanzu basu dawo ba, group o gareta, jinin yana mana wahalar samu”

Cikin 6acin rai tace “jini yana wahala kenan haka Zaku Barta tamutu mune da asara kenan?”

Likitan tace “Hajiya Bahaka bane kiyi hakur….”

Gyaran murya Huzaifa yayi yace “A a, Anty kiyi hakuri, zanbata, irin jinina ne”
ya kalli doctor yace

“muje lab din ku d’iba”

Tafiya sukai,ya kwanta aka ‘Debi jininsa, zasu gwada ko akwai wata cutar, tunani huzaifa yayi hakanma qarin wani 6ata lokacin ne, yafada musu su dauka kawai a saka mata, shi lafiyarsa kalau, haka ya kwanta aka Debi jininsa leda biyu, sannan taje ta daurawa Waheeda tareda allurar bacci, shikuma ya kwanta zuwa wani lokaci sannan yatashi yakoma Dakin da aka kwantar da Waheeda yaharde hannun sa a qirjinsa yana qare mata kallo, Sai yanzu nema yake sake ganin tsantsar kyanta, lokaci daya yaji sonta yana sake qaruwa acikin zuciyar sa, idan bai sameta ba, bayajin zai iya yin aure a rayuwar sa

Sai dare sannan Waheeda taji Dama Dama aka sallameta tareda alqawarin hajiya Anty zataci gaba da dubata agida.

har zuwa wannan lokacin Huzaifa yana Nan bai tafi ba, su ‘yanbiyu Sai Kallan sa suke afakaice suna gulma ganin yanda yake komai nasa cikin aji da kamun Kai, saida sukaje gida lokacin karfe Tara nadare, sannan yayi musu sallama yatafi

Washe gari da safe ya dawo dubata, babu laifi jikin Nata akwai sauqi sosai, har falo aka shigo dashi, ta zumbula hijab dinta tafita, kallanta yayi yace “Baby yajikin?”

Wasa take da yatsun hannunta kanta aqasa tace “Alhamdulillah Yaya”

Yatsina fuska yayi yace “Yaya Kuma Waheeda? No.. No… Banason sunan Nan, ki sauya min wani”

Daga Masa Kai tayi, ledar dake hannun sa ya ajiye agabanta, yace “dazan taho ne nashiga super market namiki shopping, nasan bakinki babu dadi tunda rashin lafiya kikayi”

Kanta yana qasa tace “to nagode”

Dan qaramin murmushi yayi yace “Waheeda bazaki Kalle niba?”

Dagowa tayi ta Kalle shi, Saitayi saurin sunkuyar da kanta qasa, sakamakon wani irin abu dataga yana futowa daga Idonsa yana shiga Nata, gabantane yafadi, harta kasa 6oyewa saida tasa hannunta a setin qirjinta, huzaifa yana ganin haka yayi tunanin ko jikin Nata ne yatashi, ahankali yace”sorry na tsaida ke, nasan kin gaji ko? “

Hannunsa yasaka acikin aljihu ya Dauko wani zobe na gold me kyau, yamiqa mata tafin Hannunsa yace” Bani hannunki “

Kallan sa tayi da mamaki, shikuma ya Dan daure fuska yace”bani mana”

Ahankali tad’ora tafin hannunta akan nasa, yatsun hannun ya kalla Zara Zara dasu dogaye, akwai zoben gold a hannunta Wanda Babban Yaya yasiya musu, saiya cire shi yasaka mata nasa yace”wannan yafi kyau, karki cire shi”🙊🙆🏻‍♀ï¸?

Daga masa Kai tayi, ya dauki wayarsa yayi kira, Ana dauka taji yace “Momy ga Waheeda ku gaisa”

Daga bangaren ta tace “to bata wayar”

Waheeda yabawa wayar yace “ga momy na zaku gaisa”

Waheeda ta karba suka gaisa da’ita cikin mutunci, sannan ta bashi wayar, shikuma yayi mata sallama yatafi

Bayan sati daya Waheeda ta warke sosai, Hali ya dawo, tana waya da huzaifa dakuma Didat, saide har yanzu bata fada musu suturo ba, kwata kwata tama manta da maganar

(idan kinsan baki biya littafin nanba kika karanta nabarki keda mahaliccinki)

Daddy ne yasa Ummah tasake yimata maganar, haka ta zauna adaki tayi shiruuu abun duniya yafara yimata yawa,cikin sauri ta turawa huzaifa text, tayi masa maganar, Amma shiru bai turo mata amsa ba,tayi tunanin ko baiga text dinba ta kirashi ya dauka Amma saiya bata haquri cewa zai nemeta,har akai kwana biyu Didat bema kirata ba bare suyi maganar.

Yauma kamar kullum tana daki a zaune tana aikin tunani, Maya ce tazo gidan suka hadu dasu yanbiyu suka shigo Dakin, Sai mita take musu basa son zuwa gidansu

Zama sukai a Dakin Sai hira suke, Amma Waheeda tayi shiru, Maya ce ta kalleta tace “qawata meyafaru ne?”

Waheeda tayi ajiyar zuciya tace “Daddy yasake min maganar auren Nan, na turawa Didat text yaturo iyayensa, Amma har yanzu banji yacemin komai ba”

Wani irin yatsina fuska Maya tayi tace “Didat Kuma? Ke a ganinki wannan sonki yake? Kawai be’iya komai ba Sai kishi, dama Huzaifa kika Bawa Dama”

Ihsan tace “ato fada mata de, danma bakiga yanda yake bane Maya, wallahi yahadu”

Intisar tace “kuka Sani ko Didat din tafuso?”

Waheeda ta murgud’awa intisar baki tace “waye yafada miki Ana mantawa da first lover?”

Inti tace “to karki min rashin kunya, inde Didat ne keda shi, Ina soyaiya abinda kusan sati kikai a kwance babu lafiya Koya leqo qi, gashinan Huzaifa yazo, kije ki qarata da Didat d’in”

Maya tace “Gaskiya Nima Ina ganin Gara Huzaifa, kawai ki share Didat d’innan kiza6o mana Huzy”

Waheeda ta d’aga musu hannu tace “tonaji,kawai zanyi shawara da Babban Yaya”

Ihsan tace “bakida Hankali Waheeda, kirasa dawa zakiyi maganar saurayin ki Sai Babban Yaya Dan raini?”

“Bazanyi maganar dashi ba? Yanda yake yayanki Nima Yaya nane, in’aka bibiyama yafi sona a kanki”

Ihsan tace “to kirashi, Wanda baiji Bari ba yaji hoho….”

Maya tayi shiru tana wani tunani a ranta,addu’ah take a ranta Allah yasa tasamu amsar tambayar tunanin datake, cikin sauri tace “eh wallahi, kira Babban Yaya muji, shawarar tasama itace daidai” Tajuya ta kalli yanbiyu tace musu “koba haka ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button