BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ihsan tace “hakane wallahi, Kuma a saka mana ita a hands-free”

Waheeda ta dauki wayarta takira Babban Yaya, yana zaune ad’akinsa a lokacin yana tunanin kiranta, tunda tatafi rabonsa da’ita, yayi missed dinta sosai, ya jira ya jira kozaiga kiranta Amma shiru bata kiraba, yasan cewa idan ta kirashi tayi kewarsa ne, yana duba wayar yaga kiranta yana shigo wa, cikin sauri Yad’aga yace “Sai yau kenan”

Yan biyu da Maya suka hada ido sukai murmushi kowa yayi shiru yana jira aji amsar Babban Yaya.

Waheeda tayi murmushi tace “Babban Yaya wallahi inason kiranka, kayi hakuri”

Yace “okay, Ina twice?”

Tace “suna Nan kalau, suna falo, yauwa Babban Yaya kasan me? Daddy ne yace zaimin aure, nabashi hakuri yaqi ji, tunde laifin danayi wa Ummah , to nayi wa Didat magana naji shiru, shine nakeso kabani shawara ko in yiwa huzaifa magana… Huzaifa de ai kasan huzaifa, zaka sanshi ma, Dan gidan minister ne maici a yanzu… “

Tunda tafara magana Babban Yaya ya runtse Idonsa, jiyake kamar ana watsa masa garwashi ajikinsa, ajiyar zuciya yayi yabude Idonsa, sannan yace”to Ina ruwana Kuma? Miye nawa aciki? Wato Waheeda na lura babu Wanda kika raina sama Dani duk cikin qanne na, nizaki kira kina fadamin hauka, saboda raini, wato ga sa’anki,ni karki sake kirana….. “

ya qarasa maganar tareda kashe wayarsa, dama bashi tayi niyyar gaidawa ba? Bakira tayi dantaji muryarsa ba? Wata zuciyar tace dashi saboda samarin ta takira ka, idanunsa ne sukai jajir baisan lokacin da yaji hawaye yazubo masa ba, yasaka hannu ya hargitsa sumar Kansa,ya kalli wayar sannan yayi jifa da’ita ta had’u da bango ta tarwatse
1/28/22, 20:50 – Ummi Tandama😇: UD

Ihsan da intisar ne suka kwashe da wata irin dariya, dariya suke suna nuna Waheeda da hannu,Waheeda takasa cemusu komai Sai kanta datake jinjinawa alamun gaskiya ne.

Maya kuwa jijjiga kanta take ahankali tana sake gaskata tunanin ta akan Babban Yaya, haqiqa Dama ta dad’e tana wannan tunanin, Sai gashi yau ta tabbatar da abinda take zargi

** *** **

Hawayen Idonsa ya share, yayi shiru yafad’a duniyar tunani, Mutum d’aya ce tafad’o masa Arai,yasan idan ya kirata zaiji ‘Dan Sanyi a ransa, babu 6ata lokaci ya d’auki wata wayar yayi Dialing number ta, bugu d’aya tad’auka muryarta can ciki, Shima cikin shagwa6a yace “Anty….”

Hajiya Anty tace “Na’am d’an Ummah ya akayi”

Cikin damuwa yace “banajin dad’i Anty , narasa meyake damuna…” ya qarasa maganar qwalla Nason taruwa a’idonsa

Tashi tayi daga kwanciyar da tayi, cikin yanayin rashin lafiya tace “meyake damunka?”

Cikin tashin Hankali yace “Anty ya naji muryarki haka? Lafiya kike kuwa?”

Runtse idonta tayi tace “wallahi zazzabi nakeji Naufal, Amma nayi allura ma, nasan anjima zanji sauqi insha Allah, Ina Ummi? Kuna waya deko?”

“Bama waya Anty, Amma zanyi mata magana yakamata tazo ta duba ki”

Murmushi tayi “a a karka damu, karabu da’ita tahuta”

“a a Anty dole zatazo taganki, please kikula da kanki, Sai anjima” yana fad’ar haka yakashe wayar tareda Dialing number ummi 😃

Tayi mamakin ganin Kiran Babban Yaya, har wayar takusa katsewa kasa d’auka tayi, saboda wani irin dad’i dataji Wai yau itace Big Brother yake kiranta, haqiqa tana d’aya daga cikin mata masu sa’a a duniya, cikin sauri ta d’auka tareda fad’in “Big Brother, My Husband to be ….”

Runtse Idonsa yayi, jiyake kamar ta watsa masa ruwan zafi a qirji, Wai husband to be…. 😖

Ajiyar zuciya yayi yace “Ummi… Anty nah batada lafiya, kisa lokaci kije kiganta”

Yatsina fuska tayi tace “mene? Wai Dama ba kirana kayi domin kaji muryarta Kuma mu Tattauna akan batun auren mu ba?”

Cikin 6acin rai yace “Duba lafiyar matar Nan yafimin komai ummi, idan kika d’auke mahaifiyata, duk duniya babu wadda nakeso sama da’ita”

Cikin haushi ummi tace “to ai Kai kace, wannan a kanka kake magana, kaine kake sonta Bayan mahaifiyar ka, tunda aka had’ani dakai maganar arziqi bata ta6a shiga tsakanin muba, kawai sai yau Ina murna kakirani,babu tambayar lafiya ta babu komai shine zakace inje Inga wata mata, gaskiya bazaka takuramin ba,Kai Bama lalle naje ba….”

ta qarasa maganar cikin rashin kunya

Cikin masifa yace
” muddin kikace bazaki mutunta iyayena ba,to bazan iya zama dake ba, ke ko wani daga cikin ‘Yan gidan mu kikace bazaki mutunta ba, to babu dole, dama can banida ra’ayin auren yarinyar da banaso, inaso kisani dole akamin a kanki, danhaka bazaki samun ciwon Kai ba….”dif yakashe wayarsa

Ummi ta qulu iya quluwa, Sai huci take tana hura hanci, inbanda tana so duniya tasan ta’auri mutum mashahuri babu abinda zaisa ta tsaya wannan gayen yana fad’a mata baqar magana, badan taso ba, haka ta shirya ta nufi gidan Hajiya Anty.

Tunda suke unguwa d’aya bata ta6a shiga gidan ba, Sai yau, lokacin data qarasa megadi yatare ta yana tambayar ta wajan wa tazo, cikin Isa da gadara ta fad’a masa cewa itace matar da Naufal zai aura, cikin girmamawa megadi yabud’e mata gidan tashiga

Duk irin shigar da tayi ta alfarma tana ganin hajiya Anty a hakimce afalo duk Sai taji ta raina kanta, saida tagama qarewa hajiya Anty kallo taga mace har mace ga kyau ga kwalliya, ga Kuma irin daular datake ciki, saita yatsina fuska sannan tace “Sannu yajikin?”

Hajiya Anty tana kallon ta, duk taga abinda tamata,babu maganar gaisuwa kawai sai sannu 😒, Saita shareta ba tace mata komai ba Saima murmushi da tayi tace “A a kice yau amare ne a gidan namu, sannu da Zuwa Daughter”

Ummi ta kalli hajiya Anty asheqe, Wai Daughter, matarda ko haihuwa bata ta6a yiba itace zata kalleta qatuwar budurwa da’ita tace mata Daughter 😏

Saitayi yaqe ta kawar dakai, Hajiya Anty tatashi takawo mata ruwa da lemuka, sannan tayi kitchen takawo mata kaji cikin flet, babu musu ummi ta zage ta dinga cin kajin Nan saida taji tayi qat, sannan tayi mata sallama tatafi,Hajiya Anty tabita da kallo, babu Allah yasawaqe babu komai kawai cikinta yana cika taqara gaba, kwata kwata babu alamar Hankali a wajan yarinyar, babu kunya ko kara atare da’ita, ajiyar zuciya tayi a fili tace “Allah yabasu Zaman lafiya”

Sannan ta d’auki wayarta takira Babban Yaya, yana d’auka tace “Ummi tazo, kakirata kamata godia”

“ashe tazo” abinda yace kenan, domin beyi tunanin zatazo dinba

Tace “tazo wallahi, yanzu tatafi, nayi tunanin ma anan zata wuni, Amma duk da haka naji dad’i sosai, Allah yamuku Albarka Allah yahad’e kanku”

Memakon yace Amin, saiyace “Anty inada aiki yanzu, akwai horar war da’ake mana, zan kashe waya”

Murmushi tayi tace “yakamata kazo kaga lefen Nan, idan akwai abinda baiyi maba, Sai a sauya, sannan nace ka tambayeta size d’inta na pant da bra, Shima har yanzu bakace min komai ba”

Cikin shagwa6a yace “Anty zanzo… Shikkenan?”

Tace “eh, shikkenan” daga haka, sukai sallama

Wayar Ummah ce kange a kunnan ta, tana zaune afalo tana waya dashi cikin nutsuwa, tun Bayan da Babban Yaya yawatsa mata qasa a’ido yanbiyu suka mata dariya, bata sake bi takansa ba, ta nutsu ta ajiye Didat agefe, takama Huzaifa 😃
Huzaifa yasake lanqwashe muryarsa yace “Waheeda bazaki Bani Dama naturo iyayena gidanku ba? Kinsan kuwa yanda na matsu naganki a gidana?”

Murmushi tayi ta dauki cup din dake gabanta me cikeda fresh milk tayi sipping sannan tace “idan lokaci yayi ai zan baka damar, saurin me kake?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button