BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ajiyar zuciya tayi, Amma maganar sa ta farko Sai yawo take mata acikin qwaqwalwarta, karfa tunaninta ya zama gaskiya…..idan hakan ta tabbata Yaya zasuyi da wannan tsohon al’amarin da wannan Yaron yake son tado musu shi?
Kallan sa tayi tace “shine damuwar?”
Kasa magana yayi, Sai Kansa daya d’aga mata kawai
Tace “to shikkenan, zan samu ummanku muyi magana da’ita, ka kwantar da hankalin ka banason wannan kukan”
Sake d’aga mata Kai yayi, Ajiyar zuciya tayi, sannan ta rungume shi sosai ajikinta, ta sunkuya tayi kissing goshinsa, sannan tad’ora masa Kansa akan Fillo tafita daga d’akin
Tana futowa daga d’akin taga yaran basa Nan,Sai Ummah kad’ai tana kallo, godia tayi wa Allah cikin ranta, sannan ta qarasa wajan ta tace “Yaya a Kwai matsala fa, nasamu yayansu yanzu, maganar gaskiya baya son auren Nan har yanzu”
Cikin tsananin damuwa Ummah tadafe kanta 🤦ðŸ»â€â™€ï¸?”nashiga ukuna,Yaya zanyi da wannan Yaron ne, banaso Naga Naufal cikin damuwa, Bari inje in sameshi….” tafad’i haka tana kokarin tashi
Cikin sauri hajiya Anty tace “Zauna Yaya, Wai meyasa bazaku zaunar da Yaron Nan yafad’a muku wadda yake so ba?”
Ummah ta kalleta cikin damuwa tace “to inda zai fad’i wadda yakeso d’in ai zanji dad’i Nima…., idan an tambayeshi fa cewa yake shi har yanzu babu wadda yakeso, ayi namiji baligi Amma ace kullum babu wadda yakeso?”
Anty tace “to yanzu ya za’ayi?”
Cikin damuwa Ummah tace “tunda ke yafara sakewa dake har yana fad’a miki damuwar sa, kifad’a masa zai iya qarawa da yarinyar dayake so d’in, yanzu su Alhaji sun Riga sunyi magana tayaya zamu ce a banje wannan auren mu maida su qananan mutane?”
Hajiya Anty tace “Eh hakane Kuma, tunda yanada damar dazai iya qara auren shikkenan, Allah ya tabbatar musu da Alkhairi, Allah ya basu Zaman lafiya Kuma”
Ummah ta jijjiga kanta kad’an, ba tareda tace komai ba.
Bayan kwana biyu aka shirya aka Kai lefen Babban Yaya,su Daddy sunyi magana da iyayen kowa daga cikin su, Ummi dakuma Huzaifa, danhaka aka tsaida date din ‘Daurin aure sati hud’u masu zuwa😢
Su kuma su Sa’ad da Sa’eed aka tsaida nasu bikin Bayan shekara d’aya 👌ðŸ»
Yau duk suna zaune afalo gaba d’ayansu,yana jin yanda intisar take cewa “akai musu wannan uban kayan Amma abada tukwicin dubu ashirin?”🤔
Ihsan tace “ai sai kiyi tayi, kanki akeji, tunda sude bazasu qara komai ba, ni dazu danahau Instagram ma kayan nagani anata turawa, mutane Sai cewa suke anyi almubazzaranci dayawa, Kuma nasan Yan gidan sune suka saka kayan a internet”
Babban Yaya Ko Kallan su baiyi ba,bare ya tanka, yasan suna magana ne akan ‘Yan gidansu ummi, wayarsa ce ahannunsa yana Kallan pictures din Waheeda, wasu tun tana zama, wani Kuma ahannunsa take yana bata fida tana Sha, wani Kuma tana cikin baho yana mata wanka, wani Kuma yad’agata sama yana kissing Kumatunta, a lokacin tafuto daga d’akinsu wayar Ummah tana hannunta, Kai tsaye wajan sa ta nufa ta zauna, yana ganin ta yayi saurin rufe wayarsa kartaga abinda yake Gani, wayar Ummah ce tasake qara, cikin 6acin rai ta dauka tace “Wai Dan Allah Didat mekake so nama? Nafad’ama gaskiya kadena kirana anriga ankawo kayan aure na”
Daga d’ayan bangaren Didat yace “wallahi Waheeda idan kika kuskura kika auri wani baniba wallahi saikin kashe auren kin futo kin aure ni….”
Cikin 6acin rai tace “au haka kace?”
“eh haka nace, Dan renin hankali kince min Inturo iyayena baki tsaya kinji abinda zan fad’a miki ba kawai saiki cemin yanzu ankawo miki kayan aure…. A a, sadaki aka kawo miki ba Kaya ba, wallahi idan kika yarda aka miki aure da wanina dagani harke Sai ran kowa ya6abaci “
Dif… Yakashe wayarsa
Waheeda tasaki tsaki ba tareda tace komai ba, tajuya ta kalli Babban Yaya har zata masa magana saitaga ya daure fuska, dolenta taja bakinta tayi shiru 😬
Da daddare abokinsa mashkur yazo,zaune suke akan had’ad’d’iyar motar Mashkur din, wadda yayi parking dinta a compound din gidan, mashkur ‘Dan Gayu ne na gaske, akwai d’aukar wanka tamkar Babban Yaya, Ihsan ce ta kawo musu lemuka ta ajiye akan ‘Dan qaramin wani dinning table dake gabansu,ta gaida mashkur sannan tajuya, har tayi Nisa Idonsa yana kanta, bata dad’e da tafiya ba intisar takawo musu cups, cikin mamaki ya kalleta yace “kaiii, Wai daga shigar ki har kika sauya Kaya kika futo?”🤔
Murmushi tayi tace “a a, Bani bace, Ihsan ce dazun”
Murmushi yayi tareda shafa qeyarsa,intisar tajuya tatafi, mashkur ya dubi Babban Yaya yace “tsakani da Allah kunada wannan kyawawan yanmatan Amma kabarni Ina shan wahalar neman matar Aure? Gaskiya Allah yamuku kyau Abokina, Wannan kyanta ace zan’iya had’asu duk su biyun, da lokaci d’aya zanyi wuf dasu”
Babban Yaya ya Kalle shi yace “banason is’kanci mashkur….”
Mashkur ya d’auki lemo guda d’aya ya tsiyaya acikin cup sannan yace “to na tambaye ka meyakamata mu tsara na bikin kaqi cewa komai, to bagara inyi abinda ya shafeni ba, Kai kasamu matar ne shiyasa kake mana is’kanci, nikuwa Sai yanzu nagani, Dan Allah Bro wannan ta farkon datazo, Ina ciki….”
Babban Yaya yayi ajiyar zuciya, cikin ransa yafara godewa Allah daba Waheeda ce takawo musu lemon ba 🤣
Yatsani yaji wani namijin yana cewa yana sonta
Ya kalli mashkur yace”ni bazaka Jamin raini awajansu ba, kamusu magana da kanka, sannan babu abinda zamu tsara, ayi bikin haka, mashkur inaji araina matsawar narasa yarinyar danake so, to wallahi mutuwa zanyi….”
Mashkur dayakai cup din lemo bakinsa cikin sauri yafasa Sha ya ajiye, sannan ya Kalle shi da mamaki yace”kasan mekake fad’a kuwa Naufal?”
“yes, bazan iya daina sonta ba”
Mashkur yace “wacce me sa’ar ce wannan? Why not kafad’a mata? Mekake jira?”
Babban Yaya yace “lokaci yaqure min mashkur, bazan iya fad’a mata ba, Amma wani bangaren inaji ajikina ita d’in tawa ce”
Cikin sanyin jiki mashkur ya bubbuga kafad’arsa, yace “kayi hakuri Abokina, yanzu meka yanke akan hakan? Wanne irin mataki ka d’auka?”
Cikin damuwa yace “band’auki kowanne mataki ba, kawai Ina addu’ah de…”
“no, hakan ai yayi kad’an Friend, saura sati hud’u bikinka fa, kamata yayi mushirya muje Saudia, Nima zan tayaka da addu’ah Allah yabaka za6inka, idan har zai kasance alkhairi agareka, idan Kuma ba alkhairi bane Allah yabaka haquri da juriya akan rashinta “
Ransa duk adagule ya kalli mashkur yace “mashkur lokaci yariga yaquremin…. Itama aure zatayi, tayaya za’a fasa dawani ayi Dani? Tayaya zan rabu da wannan nacacciyar yarinyar ummi? Wallahi haushin ta nakeji, idan ta kuskura ta aure ni ko…. Wallahi saina mata filla-filla aranar da aka kawota kuma da niyya”
Mashkur ya kwashe da wata irin dariya sannan yace “Abokina bakada Dama wallahi, kadena wannan tunanin, kasa aranka zaka yarda da qaddara mekyau ko marar kyau, sannan karka manta komai yayi zafi maganin sa Allah, a lokacin daka shiga cikin matsala kadinga tunawa cewa akwai Allah…. Saboda haka yanzu ma shi zamu kaiwa kukan mu, me muke yanzu a qasar? Mushirya gobe mutafi Saudia, daga Nan kawai muwuce England…. “
Sai a lokacin Babban Yaya yasaki wata irin ajiyar zuciya, yace
” nagode Friend”
cikin farinciki suka rungume juna
Washe gari karfe goma a compound tayiwa Babban Yaya, sunyi waya da mashkur zasu had’u a Airport, Waheeda da Yanbiyu ne suka rakoshi har wajan motar dazai shiga, wayar Ummah tana hannun Waheeda, Huzaifa ne ya kirata cikin murna ta d’auka tafara masa magana Sai wani kashe murya take…. Babban Yaya yabude motar zai shiga ya kalleta yace “mahaukaciya…” 🤣