BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummah tayi murmushi tace “Haba Yaya, ai tsakanin da kunya, abar maganar Nan kawai, jiya fa bakaga yanda matarsa tasake da yaran Nan ba, musanman ma Waheeda, ta daukemu kamar yan’uwa, Kuma yanzu taji mun dauki ‘ya mun Bawa mijinta ai abun babu dadi Yaya”

“a a yazakice babu dadi, ai be haramta ba, zai iya auren ta, Sai suyi zamansu, kude bakwa so yaranku su rayu a qauye, kiyi magana da yarinyar idan tana so shikkenan Sai awanketa a kaita Dakin mijinta”

Umma ba tasake musu dashi ba, tace masa “to shikkenan Yaya, Allah ya tabbatar da Alkhairi” daga Nan ta kashe wayar

Yanbiyu ne suka kalleta, Intisar tace “Ummah Wai meyake faruwa?”

Ummah tace “Ina baqinmu najiya, Wanda su kazo daga kaburma?, to shine yace Yanaso abashi Waheeda, zai aure ta, shikuma yarasa wazaiso Sai wannan shashashar”

Yanbiyu suka kwashe da dariya

Cikin sauri tadago kanta ta kalli Ummah tace “Tabdi, Amma Yama raina min Hankali, yana Kaburma yarasa wazai Burma aqauyensu Saini? Ni wallahi Bana sonsa”

Ummah tace “aikuwa Yaya Habu yace inde kin amince za’a bashi”

“Ummah Bana sonsa, Kuma ai Babban Yaya yahanamu kula kowa”

Da wannan maganar Tata Ummah ta gamsu, saboda tasan Burin yayan nasu bai wuce ace yaga sunyi karatu Mai tsawo ba.

Washe gari da safe, qarfe bakwai daidai, aharabar gidan tayi musu,gaba daya compound din gidan interlock ne, Sai wasu manyan motoci masu numfashi guda hudu dasuke parking space, daga can Gefe Kuma wani waje ne aka ware aka qawata shi da grass masu yawa, Sai ball dasuke zube a wajan, da alama suna buga ball ne wani lokacin. 

kowacce tana Sanye da uniform dinta, uniform din yayi musu kyau sosai musamman Waheeda, farar Riga ce me dogon hannu Wanda yake d’aukeda links,tareda Dan qaramin hijab Wanda da kadan yarufe musu breast dinsu, Sai siket ruwan toka da kadan ya wuce gwiwarsu, Bai sakko qasa sosai ba kasancewar makarantar bata musulmi bace, Yan biyu Kam sun saka doguwar safa fara, taboye musu qafarsu, Waheeda kuwa bata saka safar ba Shiyasa farar qafarta ta baiyana sosai tamkar baturiya, safar tana hannunta, saikuma school bag dinta me shegen kyau data rataya a hannunta guda daya, Hips dinta ya futo sosai acikin siket din dukda buje ne, dukansu babu me dankwali saide hijabin kowa akwai hula ajiki, ta Bayan hijab dinta kuwa kana iya hango duhun gashin kanta Wanda ta nannadeshi tayi acuci maza dashi.
bataje kusa da yan biyu ba,Dan tasan bakoda yaushe suke zama inuwa daya ba

Driver ne da Kansa yabude musu Bayan motar suka shiga, yarufe sannan yaja sukabar harabar gidan, yana sauke su a makaranta yajuyo, Dama haka yake idan ya sauke su juyawa yake, saikuma an tashi zaizo ya dauke su.

Kowa Class dinsa ya nufa, yanbiyu suka nufi Ss3 duka su biyun, ita Kuma Waheeda tayi Ss2, takusa shiga aji Aryan yasha gabanta, cikin sauri taja baya ta tsaya tace “Haba Aryan miye hakan?”

Yanbiyu suka juya suka kalleta, sukayi qwafa tareda shigewa aji, jiya jiyan Nan tagama cewa Ummah Babban Yaya yahanasu kula Samari, saboda Dan Kaburma yace yana sonta, Amma gashinan kullum saita kula wannan tatsitsin Yaron me kama da lagwani, sunmata magana akansa Amma taqi ji, ajinsu daya itada Yaron, saboda maza da mata ahade suke, saide kowa da layinsa.

Hannunta yakama suka shiga cikin ajin, ko kadan batayi yunkurin qwace hannunta ba, ajin babu kowa saisu kadai, kasancewar sun shigo da wuri, Kallan ta yayi yace “Waheeda jiya kwana nayi Ina mafarkinki, Kuma kinsan de bazan iya Bari har Aunty tashigo ajin Nan batare danayi tozali da kyakykyawar fuskar ki ba”

Fararen idanunta tajuya tace “Allah da gaske? To in hakane Bani labarin mafarkin Naka”

“bazan baki labarin mafarkin danayi ba saikinmin alqawari Zaki barni na tabbatar da abunda yafaru acikin mafarkina”

Tayi tunanin wani labarin daban zai bata, Kai tsaye tace “nayima, Ina jinka”

Hannunta yasake kamawa duka biyun yana shafa tafin hannunta, yarage murya cikin sigar rada yace “Waheeda Ina sonki sosai, karki Bari arabamu kinji” ya qarasa maganar yana turata jikin bango, idanun tane sukai wuri-wuri tafara kallon qwayar Idonsa, tace “Aryan miye hakan ne? Mekake yi haka?”

Kallan idonta yayi yace “abinda nagani amafarki zan tabbatar dashi a yanzu” yana gama fadar haka ya Dora hannunsa akan Boobs dinta yamatsa da qarfi, lokaci daya taji wani irin shock ya kamata, tunda take ba’a taba taba mata nono ba Sai yau, kokarin dauke masa hannunsa take daga qirjinta Amma takasa saboda yanda ya musu ruqo Bana wasa ba, kana ganin yanda yake matsawa da qarfi kasan sabon shiga ne, hannunsa guda daya tabige saboda azabar zafin datake ji, maimakon yasake ta saiya maida hannun kanta, ya riqe tudun gashinta da tayi acuci maza dashi yahade bakinsu waje daya (😱)

Adede lokacin Uncle Tunde yazo wucewa ta Bayan window na ajin, anan yayi tozali dasu, ihu yasaka yana kururuwa tare da nuna su Waheeda da hannu, Nan da Nan malamai suka taru, Kai tsaye office din Director aka tafi dasu,kan kace me, har labari ya watsu cikin makaranta, saida aka kira yanbiyu agabansu aka kwantar da Waheeda da Aryan aka zanesu, sannan director da Kansa yace ya Koresu daga makaranta, da’ita da Aryan dasu kansu Yan biyun, yace baya buqatar ahalinsu acikin makarantar sa

Kuka Yanbiyu suka fara, suna bashi hakuri, idanunsu yayi jajir kasance warsu farare, Amma Haka sukaqi hakura, Waheeda tatashi takade jikinta tace “aikin banza aikin wofi,babu tambaya babu komai kawai za’a rufe mutum da duka,kukuma kun tsaya Sai wani koke-koke kuke Kuna basu haquri, ai bazaku nunamin ranku yabaci ba saikun kasheni kun kaiwa uwata gawata, idan kun gama kukan saiku taho mutafi” tana fadar haka tafice daga office din, babu Wanda yamata magana acikin malaman, saboda sunsan batada kunya, Waheeda Virus zata fadi abinda yafi haka.

a bakin titi suka hadu da’ita,basuce mata komai ba Sai sharar hawaye kawai suke, itace ta tare musu adedeta suka shiga, haka Kuma itace ta fada masa inda zai kaisu, har lokacin yanbiyu kawai hawaye suke sharewa.

Amma kana Kallan fuskar su kasan cewa akusa suke, sun cika sunyi fam, kawai neman fashewa suke, suna hanya Sai tsaki take saki ita kadai, saboda gaba daya breast dinta bala’in zafi suke mata,damuwar ta daya, kar Babban Yaya yaji, ta tabbatar idan yaji wannan labarin ta mutu! sukuma yanbiyu sunyi tunanin dasu take wannan tsakin, saboda haka Saita qara tunzura su, Ana ajiyesu daga napep din tayi gaba, suka biyo bayanta tajuya taga yanda suke tafiya atsorace, ita kanta tsoron yanda zatayi bayanin abinda ta aikata take yi bare Kuma su, Amma yanda taga jikin Intisar yana rawa Sai abun yabata haushi, lokaci daya tasaki wani tsaki zataci gaba da tafiya
Yanbiyu suka hada ido, dama gashi taja ankoresu daga makaranta, aikuwa basu tsaya sauraren komai ba suka rufeta da duka, megadi hankalinsa yanakan radio Sai ihun Waheeda yajuyo, cikin sauri yanufesu yafara rabiya

Ummah tana zaune afalo tana break fast, tunda su Waheeda suka tafi school Sai yanzu tasamu ta zauna tana cin abinci, wayarta dake Gefe ne tayi qara, number Hauwa’u tagani matar Iliyasu Dan Kaburma, ta dauka suka gaisa cikeda kulawa, umma tace “Hauwa ashede Zaki kiramu, yagida yame gidan naki dasu Halima?”

Hauwa tayi dariya tace “Hajiya wanne megida? Ai kwanan mu daya da zuwa garinku tunda muka dawo narasa gane Kansa, Sai nemana yake da tashin Hankali Ina rabuwa dashi, qarshe ma yace natafi gidanmu ya sallameni, Sai daga baya nakeji ashe neman aure yake, shiyasa yasakeni, ai Bama tare Ina gidanmu hajiya “

Gaban Ummah ne yayi mummunar faduwa, haqiqa idan zancen Hauwa’u ya zama gaskiya to akan Waheeda mijinta yasake ta, tunda shine yayiwa baba Habu magana yana son yaqara auren, salati tafara a fili takasa dainawa har Hauwa’u ta kashe wayar Dan itakan tayi tunanin saboda zancen sakin da aka mata ne yasa Ummah wannan dogon salatin 😂

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button