BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

** *** **
Suna zuwa gida yad’aukota a hannun sa yafuto da’ita daga cikin motar, yanbiyu dasuke daukan photo a compound sukaga Huzaifa ya ‘Dauko Waheeda, cikin sauri suka nufesu, Adede lokacin Didat da kakarsa da babansa suka shigo gidan, ta window din motar ya hango Wani ya dauki Waheeda a hannun sa, tun kafin babansa ya qarasa tsayawa da motar, yabud’e yafuto ya nufesu, yana zuwa ya cakumi wuyan Huzaifa “ubanwa yace ka d’auki wannan yarinyar…?”
Huzaifa ya kalli gaban rigarsa, yaga yanda Didat ya riqeshi cikin 6acin rai yasaki Waheeda tayi qasa, ‘yanbiyu suna ganin haka sukai kan yar qanwar su suka cacimeta Sai jijjiga ta suke, Ihsan tayi gudu cikin gida ta fad’awa Ummah abinda yake faruwa, intisar Kuma tayi wajan fomfon da’ake bayin fulawa ta ‘Debo ruwa ta watsa mata, lokaci d’aya ta farka tareda sakin wani irin kuka
Huzaifa yakama Didat, suka fara dambe 🙆ðŸ»â€â™€ï¸?
Baban Didat ya kamashi yace “wuce mutafi gida, banason tashin Hankali son”
Ummah ta qaraso wajan itada Ihsan cikin tashin Hankali take tambaya ”menene yafaru?”Didat dayake ta haki da kumfan baki yace “Ummah saboda me wannan banzan zai dinga d’aukar Waheeda? saboda me Ina son yarinya wani qato zai dinga riqeta”
Cikin 6acin rai Huzaifa yace “nafi karfin a kirani qato, tunda nine Nan zan aure ta”
Didat yanuna shi da hannu yace “Dan zaka aure ta shine hakan yabaka damar ta6a jikinta? Aibaka aure taba”
Hajiya Anty tashigo gidan ta shirya tsaf zata wuce Asbiti, tabiyo wa Ummah zasu gaisa,kamar yanda tasaba, tana zuwa batabi takan kowa ba tanufi Waheeda, datake kuka kamar ranta zai fita, tambayar ta take “meyake faruwa?”
Amma Waheeda tayi shiru tama kasa magana.
kakar Didat ce ta matso ta kama hannun sa tace “muje” ta sake Kallan Ummah tace “Hajiya zamu dawo daga baya”tana fad’ar haka tajuya tashiga motar su, shikuma Didat babansa yakama hannun sa, yayinda Huzaifa yake sake gyara gaban rigar sa da Didat ya cukwikwiye masa, mutuqar tashin Hankali Hajiya Anty tashiga, jikinta Sai rawa yake tana kallon Waheeda, bata taba ganinta tana irin wannan kukan ba, gashi taqi yimata magana, Cikin 6acin rai ta make Waheeda da duka,tace”Dan ubanki bazaki fadamin abinda yake faruwa ba? “
Cikin kuka tace” Wai… Waii…. Ninn nice nake da qanjamau… “ta qarasa maganar tana rushewa da Kuka
Yanbiyu suka zaro ido😳 suna fad’in”qanjamau Kuma?”
Didat da babansa suka juyo da sauri, kowa Idonsa akan Waheeda sunaso suji ta amsa abinda yanbiyu suke tambaya, ahankali ta daga musu kanta alamun hakane
Didat ya kalli Waheeda ya jijjiga Kansa, sannan yayi gaba, babansa ma yabi bayansa suka tafi
Yanbiyu ne suka ja Waheeda sukayi ciki da’ita, gaban hijab dinta duk ya jiqe da hawaye, hannunta ta dora aka, tana rusa uban kuka, Hajiya Anty tabiyo bayansu cikin wani irin yanayi, kwata kwata bata sanin inda take jefa kafarta, kawai tafiya take, Ummah kuwa jitayi kamar tana tafiya akan is’ka, kalmar qanjamau d’innan Sai yawo take acikin zuciyar ta,Huzaifa yashiga motarsa yaja yabar gidan
ihun da Waheeda take ne yafuto da Daddy daga cikin daki cikin sauri, Nan yafara tambayar ba’asi, Amma kowa yakasa bashi amsa, da Yanbiyu da Waheeda kowa Sai kuka yake, su Sa’ad da Sa’eed ma suka futo daga daki kowa yana tambayar ba’asi
Hajiya Anty tadauko wayarta ajaka takira Uncle Usman tace “Alhaji gidannan fa babu lafiya, katashi daga baccin Nan kazo” tana fada masa haka muryarta na rawa alamun kuka zata fara, daga Nan ta kashe wayar ta
Ko minti biyar ba’ayi ba saiga uncle Usman yashigo dagashi Sai jallabiya, Daddy yace “Hajiya, mu duk munzo Nan mun zauna, muna tambayar ku meyake faruwa kunyi mana shiru, Yara suna kuka kunbarsu babu Wanda yake lallashin su”
Ummah ta Kalle shi “Alhaji Wai Waheeda ce me qanjamau…” tana fad’a masa haka hawaye yazubo daga idonta
Daddy da Uncle Usman suka nemi waje suka zauna suna fadin “innalillahi wa inna ilaihirraji’un….”
Hajiya Anty tadafe kanta daya ke ciwo kamar zai fado,Waheeda tanajin furucin Ummah tafara girgiza kanta,cikin kuka tace “wallahi ni banida komai, Allah sharri akamin” yanda take kukan abin tausayi shine yasake karya zuciyar yan’uwan Nata ma, Nan da Nan falon nasu ya kaure da koke-koke,
Ahankali Hajiya Anty tatashi ta janyo ta jikinta ta rungume ta, idanun Waheeda yayi jajir, fuskarta ma haka, Sai ajiyar zuciya take, Hajiya Anty ta kwantar da kanta a qirjinta tana bubbuga Bayan ta, Amma kwata kwata takasa cemata komai, ita kadai tasan metake ji acikin zuciyar ta
Maya ce takira wayar yanbiyu, cikin kuka intisar ta d’auka, Maya tace “Inti nakira wayar Ummah zanyi magana da Waheeda to ba’a d’auka ba, Dan Allah ki had’ani da’ita”
Cikin kuka intisar tace “Maya Waheeda babu lafiya”
Maya tace “innalillahi…. Kinga Bari kawai Gani Nan zuwa, tunda naji kina kuka nasan ba lafiya ba”
Ko awa daya Maya bata qaraba tazo gidan, yanda taga qawar Tata ta haukace tasan babu lafiya, haka sukaci gaba da zama sun kasa ta6uka komai, Uncle Usman yayi ajiyar zuciya ya kalli Daddy “yanzu Alhaji menene abin yi?”
“Salam Alaikum” yayi sallama ciki-ciki tareda shigowa falon
Gaba d’ayansu suka d’aga Kai suka Kalle shi, Waheeda tana ganin Babban Yaya tatashi da gudu ta fad’a jikinsa tareda sakin wani irin sabon kuka,ahankali ya Lumshe Idonsa sannan yabud’e su,yaso ace su kad’ai ne daya sake rungume ta ya lallasheta, ahankali yad’ora hannun sa abayanta yana bugguga Bayan ta kad’an kad’an , but duk da hakan yana jin yanda nonuwan ta suke bugar qirjinsa
Maya ta Kalle su, itade wad’annan mutanan suna birgeta, cikin sigar rad’a yaace “kiyi hakuri, is ok, kukan ya’isa haka”
Cikin kuka tace “Babban Yaya Allah banida komai”
Zareta yayi daga jikinsa
Yaruqo hannunta suka zauna a falon, Kallan Daddy yayi yace “Daddy ni Hankali na bai kwanta da wannan asbitin da suka jeba, why not Akira family doctor yazo gida ya dauki jinin Nata agaban mu saiya kawo mana result d’in mugani”
Daddy yace “to Son…. Tun dazu ma mu bamuyi wannan tunanin ba, munkasa aikata komai, hakan ma yayi”
Maya ta dauki wayarta tayi kira, ahankali tatashi ta kalli yanbiyu tace “Ina zuwa, zanyi waya”
Yanbiyu suka d’aga mata kai, ita Kuma tafita cikin sauri
Babban Yaya yakira family Doctor d’insu, yayi masa bayanin komai ta waya, cikin qanqani lokaci doctor khamis yazo gidan, yanda yaga family din duk sun had’u waje daya, yasan cewa haqiqa akwai abinda yake faruwa, Babban Yaya ya nuna masa Waheeda, doctor khamis ya qarasa ya dauki jininta, sannan ya musu sallama cewa zaije ya dawo
Har doctor khamis yatafi, banda addu’ah babu abinda mutanan Nan suke yi, kowa yayi shiru Sai zancen zuci, Waheeda kuwa Hankalinta ne ya kwanta, tasan cewa yanzu ne gaskiya zatayi halinta, zasu yarda da abinda take fad’a musu, kusan awa biyu suka d’auka suna jiransa, Sai gashi yashigo falon fuskarsa Sai had’a gumi take, suna ganinsa kowa ya miqe tsaye kamar Wanda suke jiran me naquda
Babban Yaya ya qaraso wajan sa, yariqe hannun sa yace “doctor ya ake ciki?”
Doctor khamis ya kalli Babban Yaya yace “kuyi hakuri yalla6ai, Bahaka naso fad’a ba, Amma tabbas akwai wannan cutar”
Babban Yaya yasake shi tareda dafe Kansa🤦ðŸ»â€â™‚ï¸? yace “Oh my God”
Sai hawaye