BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gabansa ne ya tsanan ta fad’uwa, ya d’ago Kansa ya kalli iyayen nasa, daga Daddy har Uncle Usman kansu yana qasa sun kasa d’agowa kamar Wanda suke jin kunyar had’a ido da yaran nasu
Ya kalli Ummah yaga tana goge hawaye
Ya kalli ‘yanbiyu yaga Sai gunjin kuka suke duka su ukun har Waheeda
Ya kalli su Sa’eed yaga kansu aqasa suma
Ya kalli Hajiya Anty yaga ta zubawa waje d’aya ido hawaye yana silalo wa daga idonta, idan akwai Wanda yaqi jinin yaga kukan ta Aduk duniya to Hajiya Anty ce, zai iya jure kukan kowa Amma banda Nata, har zuwa lokacin Hajiya ummi tana falon, ita bata tafi ba, Kuma takasa Bawa kowa haquri
Zuciyar sa ce take zigashi akan yafad’i abinda yake ransa, tayaya za’azo har gida, harcikin falon su aci mutuncin su kawai saboda maganar Aure? Tayaya zaiguji Waheeda? Tayaya zai raba zuciyar sa da soyaiyar ta Bayan da soyaiyar Tata aka halicce shi?
Lokaci d’aya yad’auki shawarar zuciyar sa, yanaso yafad’i abinda yake ransa Kuma Yana tsoron abinda zai biyo baya, gabansa yaqara tsananta fad’uwa, cikin sauri kamar an fuzgo maganar daga bakinsa ya kalli inda Daddy da Uncle Usman suke zaune yace “Daddy nizan Aure ta”
‘Diffff…… Sai aka nemi masu kuka a falon aka Rasa,falo yayi shiruuu, kowa ya d’ago Kansa yana Kallan Babban Yaya, falon yayi tsit kamar babu wata halitta acikinsa, kowa Kallan sa yake cikeda mamaki, gaba d’ayansu yaran gidan babu Wanda mamaki bai kamashi ba Sai iyayen ne kawai dasuke Kallan sa cikeda d’inbum almara
Ummi ta miqe tsaye cikin tashin Hankali tace “ka auri wa? Wallahi saide ka za6a koni ko ita, Amma Bazan ta6a yarda ka aure ta ka shafamin qanjamau ba, saide mu rabu….”
Ummah ta kalli Babban Yaya tace “Naufal meyasa….?meyasa zaka fad’i wannan maganar?”
ta qarasa maganar tana dafe kanta dayake barazanar rabewa gida biyu 🤦ðŸ»â€â™€ï¸?
Cikin tashin Hankali Waheeda ta zaro idonta😳 Wanda yayi jajir kamar gauta saboda kuka, kamar ba itace take ihun kuka yanzu ba
Kallan Ummah tasake yi ko zata qarya ta maganar da Babban Yaya yafad’a, Amma saitaji Ummah tayi shiru, ta kalli su Daddy har yanzu kansu yana qasa sun kasa kallan mutanan falon, cikin tashin Hankali tace “Zaman Zina? Ni wallahi bazan yarda ba, banason sa, bazan iya Zaman aure dashi ba…..”
tatashi tayi d’akinsu da gudu cikin tsananin kuka
Wani irin kuka ne yataso masa, yau shi Waheeda take cewa bata sonsa, wani irin abu yatokare masa maqoshi, ko yawu yakasa had’iyewa.
Ummi ta Kalle shi tace”Naufal jiranka nake, nabaka za6i tun d’azu kayi shiru, kana tunanin zan yarda kahad’ani kishi da wannan yarinyar ne? Wallahi bazai iyu ba saide asan nayi, zanje in fad’a agida yanzu yanzu “
Baqin cikin kalmar da Waheeda tafada masa ne yake addabar zuciyar sa, jiyake kamar yafashe da Kuka kozaiji sauqi Amma kukan yaqi zuwa, ga Kuma wannan yarinyar datake qara masa wata damuwar.
Cikin 6acin rai Shima yatashi tsaye, cikeda tsawa yace” toki fad’a mana, so what….? Idan kin fad’a musu kiqara musu da cewa Bana sonki, Bana qaunarki, bazan iya zama dake ba, saboda bakya respecting iyayena “
Yajuya ya nuna mata Hajiya Anty sannan yaci gaba da fad’in”matar dakika raina kike mata Kallan sa’arki itad’in mahaifiyata ce…”
Lokaci d’aya ummi ta qame a wajan, gabanta yafad’i, cikin mamaki ta bud’e bakinta, takasa rufe shi
Babban Yaya yahad’e hannun sa waje d’aya ðŸ™ðŸ»ya kalleta yace “Dan Allah Ummi kifita daga cikin rayuwa ta, na roqeki”
Cikin kuka ummi Tajuya tafice daga gidan, Shima Babban Yaya batare daya kalli iyayen nasu ba yafice cikin sauri, saboda zuciyar sa tagama karyewa, qiris yake jira yafashe da kuka, yana zuwa compound yashiga motar sa yamata key yabar gidan a d’ari da Sittin, Kai tsaye gidansa ya nufa, yanda yake danna Hon yasa maigadinsa yabud’e masa da sauri, shigowa had’ad’d’an gidan nasa yayi tareda parking din motar sa, yad’ora Kansa akan sitiyarin motar yayi shiru, har yanzu maganganun Waheeda yawo suke masa a ransa, yana jin yanda wayarsa take qara Amma yaqi dubawa, saida kira na uku yashigo sannan ya d’auka
Daga d’ayan bangaren Mashkur yace ” Bro… Ina kabar wayar ne?”
Sai a lokacin kukan dayake dannewa agida yataso masa, fashewa yayi da Kuka harda shashsheka, daqyar maganar sa take fita, cikin kuka yace “Mashkur bata sona…”
â¤ï¸
1/28/22, 20:51 – Ummi Tandama😇: GG
Daga Huzaifa har Didat, babu Wanda ya sauya Kaya daga cikin kayan da sukai fad’a d’azu 🤣
Dama kowa kamar jira yake, shiyasa su Sa’eed suna zuwa suka biyo bayansu, suka taho gaba d’aya
Uncle Usman ya kalli doctor khamis yace “dauki jininsu doctor”
Doctor yamatso jikinsa Sai rawa yake yanata had’a gumi, yad’auki jininsu, Hajiya Anty tatashi ta kalli Naufal tace “muje kasa driver yakaishi, saboda yayi sauri ya dawo karmu tsaidasu Huzaifa dayawa”
Didat sarkin kishi ya kalli hajiya Anty yayi qasa da Kansa, wato kar Asa su huzaifa jira, shi bata ambaci sunan saba, Huzaifa kawai tasani 😂
Babban Yaya yatashi, suka futo su uku, dashi da doctor dakuma Hajiya Anty,suna zuwa compound Babban Yaya yakira driver, yasa shi yad’auki doctor khamis suka tafi.
Ummi ce tashigo gidan, Babban Yaya yana ganin ta yad’auke Kansa kamar bai ganta ba, yarasa uban me yakawo ta gidan Kuma, kwata kwata mace babu aji babu kara kullum kina yawo a gidan surukanki?
Ummi ta kalli hajiya Anty ko gaishe ta batayi ba, ta shareta,Anty tayi murmushi kawai, Babban yayama ya ganta, Kuma Sarai yagani bata gaida Hajiya Anty ba, Shima bata gaishe Shiba, har Gara shi Dama yasan kar take ganinsa 😃
Amma hajiya Anty fa?🤔
Gaba d’ayansu falon suka dawo suka zauna, dasuka shigo falon ma yayi tunanin zata gaida Hajiya Anty nanma yaji shiru, Kuma yaga ta nemi kujera ta zauna ta kame, saikace yar gida, jijjiga Kansa kawai yayi, inbanda rashin Hankali tayaya zakiga family sun taru gaba d’ayansu, Amma kizo ki zauna ai daga Gani kinsan ba lafiya ba
Yanda kowa na falon yayi shiru haka ummi ma tayi shiru tana jira taga abinda yake faruwa,su doctor basufi awa d’aya ba suka dawo, yana shigowa kuwa kowa ya maida hankalin sa Kansa, Uncle Usman yace “doctor ya akayi?”
Cikin rashin damuwa yace “Alhaji naduba babu…., kowa lafiyarsa kalau acikinsu, daga Didat d’in har Huzaifa, babu Wanda yake d’aukeda HIV”
Ummi ta zaro ido😳 tareda rufe bakinta da hannunta tana sake zare ido tana Kallan ‘Yan falon taga to waye yake da qanjamau d’in? 🤔
Daga Daddy har Uncle Usman sunkuyar da kansu qasa sukai, to daga Ina wannan matsalar take? Tayaya akai Waheeda tasamu wannan cutar kenan?
Huzaifa ya miqe tsaye, ya kalli kowa da kowa na falon yace “Alhamdulillah… Tunda gaskiya ta bayyana, ni Dama temako naso yi, lokacin Dana tarar batada lafiya nad’auki jinina nabata,ashe bansaniba tunanin da kuke min daban ne, saboda tozarci mu za’a kawo a ajiye anan Ana jira aga waye me qanjamau acikinmu ayi masa ruwan bala’i saboda shine yasakawa ‘yarku cuta, to ai yanzu kunji komai, Kuma gaskiya ta futo bamune muka saka mata ba, saboda haka nikam na haqura da Waheeda…. Maganar gaskiya, bazan iya auren me qanjamau ba, duk soyaiyar danake mata….”
Tunda yafara magana gaba d’aya falon yayi tsit, kowa kallansa yake cikeda mamaki, musanman su Daddy yanda suka d’aukake shi,Babban Yaya kuwa baiji komai ba, asali ma dad’i yaji yanda gaskiya ta bayyana,sukaga halin Huzaifa na zahiri, inda ace ya fad’a musu karsu bashi Waheeda ya tabbatar babu Wanda zai saurareshi, ko d’ago Kansa baiyi ya kalli Huzaifa ba,harya gama maganar sa yafice daga falon cikin 6acin rai