BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Waheeda kuwa d’agowa tayi da jajayen idonta ta zubawa Huzaifa ido, ko kad’an takasa ce masa komai, yanbiyu kuwa kuka suke sosai saboda furucin huzaifa, bakajin komai Sai kukansu daya cika falon
Ummi ta Jinjina kanta tareda ta6e baki☹ï¸
Didat yatashi tsaye ya qarasa wajan Waheeda tareda miqa mata hannu yace “Waheeda, kiyi hakuri kinji, Ina tare dake a koda yaushe, wannan shine abinda nake nuna miki, nine nake sonki ba Huzaifa ba…..”
“kakeson wa?” maganar kaka ta karad’e falon nasu, juyawa yayi yaga kakarsa da babansa a tsaye, Kai tsaye yace mata “inason ta, saboda me zan rabu da’ita dan qaddara tahau kanta?”
“to saide ka za6a koni ko ita, haka kawai yarinyar data qika tun tuni,kana bibiyarta akan ta saurareka taqi, tazabi wani a kanka, itace yanzu saboda rashin Hankali zakazo kace kanaso ka aura Bayan tagama yawon duniya takwaso qanjamau? To bada niba bada irin gidana ba, wuce mutafi kona tsinema Albarka yanzun Nan”
Hawaye Didat yafara yace “Amma Ina sonta…”
Babansa yayi ajiyar zuciya yace “kayi hakuri son, Amma nima bazan barka kana da cikakkiyar lafiya ka sauri me HIV ba”
Didat ya kalli Waheeda, itama ta Kalle shi,bayajin zai iya daina son Waheeda har qarshan rayuwarsa, tanada cuta ko bata da cuta abinda yasani shine yana qaunarka tsakani da Allah, cikin kuka yafice daga falon da sauri, iyayensa suka Mara masa baya
Hawaye kawai tsiya ya yake a’idon Waheeda,wannan shi ake kira sai masifa ta sameka ne zaka san me sonka da gaskiya, yanzu duk soyaiyar da Huzaifa yake iqrari yana mata ashe qarya ne? Ashe saboda cuta ta sameta zai iya gudunta? Didat din datake wulaqantawa shine ya tsaya tsayin daka akan yana sonta duk da haka, lokaci d’aya taji numfashin ta yana sama kamar zai d’auke, yanbiyu da Ummah da Hajiya Anty, kuka suke sosai, duk falon anrasa Wanda zaiyi magana guda d’aya
Gabansa ne ya tsanan ta fad’uwa, ya d’ago Kansa ya kalli iyayen nasa, daga Daddy har Uncle Usman kansu yana qasa sun kasa d’agowa kamar Wanda suke jin kunyar had’a ido da yaran nasu
Ya kalli Ummah yaga tana goge hawaye
Ya kalli ‘yanbiyu yaga Sai gunjin kuka suke duka su ukun har Waheeda
Ya kalli su Sa’eed yaga kansu aqasa suma
Ya kalli Hajiya Anty yaga ta zubawa waje d’aya ido hawaye yana silalo wa daga idonta, idan akwai Wanda yaqi jinin yaga kukan ta Aduk duniya to Hajiya Anty ce, zai iya jure kukan kowa Amma banda Nata, har zuwa lokacin Hajiya ummi tana falon, ita bata tafi ba, Kuma takasa Bawa kowa haquri
Zuciyar sa ce take zigashi akan yafad’i abinda yake ransa, tayaya za’azo har gida, harcikin falon su aci mutuncin su kawai saboda maganar Aure? Tayaya zaiguji Waheeda? Tayaya zai raba zuciyar sa da soyaiyar ta Bayan da soyaiyar Tata aka halicce shi?
Lokaci d’aya yad’auki shawarar zuciyar sa, yanaso yafad’i abinda yake ransa Kuma Yana tsoron abinda zai biyo baya, gabansa yaqara tsananta fad’uwa, cikin sauri kamar an fuzgo maganar daga bakinsa ya kalli inda Daddy da Uncle Usman suke zaune yace “Daddy nizan Aure ta”
‘Diffff…… Sai aka nemi masu kuka a falon aka Rasa,falo yayi shiruuu, kowa ya d’ago Kansa yana Kallan Babban Yaya, falon yayi tsit kamar babu wata halitta acikinsa, kowa Kallan sa yake cikeda mamaki, gaba d’ayansu yaran gidan babu Wanda mamaki bai kamashi ba Sai iyayen ne kawai dasuke Kallan sa cikeda d’inbum almara
Ummi ta miqe tsaye cikin tashin Hankali tace “ka auri wa? Wallahi saide ka za6a koni ko ita, Amma Bazan ta6a yarda ka aure ta ka shafamin qanjamau ba, saide mu rabu….”
Ummah ta kalli Babban Yaya tace “Naufal meyasa….?meyasa zaka fad’i wannan maganar?”
ta qarasa maganar tana dafe kanta dayake barazanar rabewa gida biyu 🤦ðŸ»â€â™€ï¸?
Cikin tashin Hankali Waheeda ta zaro idonta😳 Wanda yayi jajir kamar gauta saboda kuka, kamar ba itace take ihun kuka yanzu ba
Kallan Ummah tasake yi ko zata qarya ta maganar da Babban Yaya yafad’a, Amma saitaji Ummah tayi shiru, ta kalli su Daddy har yanzu kansu yana qasa sun kasa kallan mutanan falon, cikin tashin Hankali tace “Zaman Zina? Ni wallahi bazan yarda ba, banason sa, bazan iya Zaman aure dashi ba…..”
tatashi tayi d’akinsu da gudu cikin tsananin kuka
Wani irin kuka ne yataso masa, yau shi Waheeda take cewa bata sonsa, wani irin abu yatokare masa maqoshi, ko yawu yakasa had’iyewa.
Ummi ta Kalle shi tace”Naufal jiranka nake, nabaka za6i tun d’azu kayi shiru, kana tunanin zan yarda kahad’ani kishi da wannan yarinyar ne? Wallahi bazai iyu ba saide asan nayi, zanje in fad’a agida yanzu yanzu “
Baqin cikin kalmar da Waheeda tafada masa ne yake addabar zuciyar sa, jiyake kamar yafashe da Kuka kozaiji sauqi Amma kukan yaqi zuwa, ga Kuma wannan yarinyar datake qara masa wata damuwar.
Cikin 6acin rai Shima yatashi tsaye, cikeda tsawa yace” toki fad’a mana, so what….? Idan kin fad’a musu kiqara musu da cewa Bana sonki, Bana qaunarki, bazan iya zama dake ba, saboda bakya respecting iyayena “
Yajuya ya nuna mata Hajiya Anty sannan yaci gaba da fad’in”matar dakika raina kike mata Kallan sa’arki itad’in mahaifiyata ce…”
Lokaci d’aya ummi ta qame a wajan, gabanta yafad’i, cikin mamaki ta bud’e bakinta, takasa rufe shi
Babban Yaya yahad’e hannun sa waje d’aya ðŸ™ðŸ»ya kalleta yace “Dan Allah Ummi kifita daga cikin rayuwa ta, na roqeki”
Cikin kuka ummi Tajuya tafice daga gidan, Shima Babban Yaya batare daya kalli iyayen nasu ba yafice cikin sauri, saboda zuciyar sa tagama karyewa, qiris yake jira yafashe da kuka, yana zuwa compound yashiga motar sa yamata key yabar gidan a d’ari da Sittin, Kai tsaye gidansa ya nufa, yanda yake danna Hon yasa maigadinsa yabud’e masa da sauri, shigowa had’ad’d’an gidan nasa yayi tareda parking din motar sa, yad’ora Kansa akan sitiyarin motar yayi shiru, har yanzu maganganun Waheeda yawo suke masa a ransa, yana jin yanda wayarsa take qara Amma yaqi dubawa, saida kira na uku yashigo sannan ya d’auka
Daga d’ayan bangaren Mashkur yace ” Bro… Ina kabar wayar ne?”
Sai a lokacin kukan dayake dannewa agida yataso masa, fashewa yayi da Kuka harda shashsheka, daqyar maganar sa take fita, cikin kuka yace “Mashkur bata sona…”
â¤ï¸
1/28/22, 20:51 – Ummi Tandama😇: SQ
Cikin sauri mashkur yace “wacece? Wacce yarinya ce wannan tasaka friend d’ina kuka haka?”
Kai tsaye Babban Yaya yace “Waheeda!”
Mashkur ya gyara zamansa yace “Waheeda Kuma? Ba sister d’inka ce ba?”
“Sister nace”
Cikin mamaki mashkur yace “but… tayaya….”
Babban Yaya ya katse shi yace “she’s my Cousin Sister”
“Amma friend abun ya d’auremin Kai dayawa, Wai kanaso kacemin Dama itace wadda kake cewa kanaso bazaka iya rayuwa batare da’itaba? Itace wadda akanta mukaje Saudia muketa ruwan Addu’ah?” 🤔
Ahankali Babban Yaya yace “itace…., inason ta mashkur, but nafad’awa su Daddy d’azu, shine tace musu Wai ita bata sona…”
“dakata Bro,tayaya kake tunanin zatace tana sonka dan Allah? Koni Nan nayi tunanin Kai yayanta ne uwa d’aya uba d’aya, haka kawai Kai tsaye yarinya taji kace zaka aure ta, Dan Allah tayaya kake tunanin zata amince Karon farko? Kaine kake mata Kallan masoyiya, ita Kallan yaya take Maka, Amma kayi hakuri, kabar komai yalafa, insha Allah zata fahimce ka, kayi hakuri “
Babban Yaya yakashe wayar, ba tareda yace komai ba, sannan yafuto daga motar yashiga ciki