BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

** *** **
Sa’eed ya kalli Ummah yace “Ummah ku fitar damu daga duhu mana”
Yasake Kallan iyayen nasu maza yace “Daddy, Uncle Dan Allah kuyi mana bayani, me Babban Yaya yake nufi? Tayaya zai iya auren Waheeda Bayan shi Yayanmu ne?”
Daddy yayi ajiyar zuciya yace “Naufal zai iya auren Waheeda”
Yanbiyu da Sa’eed da Sa’ad suka maida Kallan su wajan Daddy
Daddy yaci gaba da fad’in, “koda ace Naufal bai bud’i baki yace zai auri Waheeda ba Toni dakaina zan d’auketa nabashi, saboda banta6a tunanin Yaron Nan Huzaifa zaimin haka ba, ashe bashida tarbiya tunda har zai iya Kallan idonmu, a matsayin mu na iyayensa, ya fad’a mana irin wannan maganganun,abinda yake faruwa Wanda ku Baku saniba shine….
Tun muna Yara nida Usman ne kawai mukai karatun boko, Yaya Habu baiyi ba, shiyasa Lokacin da muka bar nijar muka dawo Nigeria da zama, a lokacin muka zauna da Yaya Habu akan Garin dazamu Yada Zango, a lokacin ya nuna mana shi yana jin dadin Zaman Garin jigawa, saboda haka mubashi wata dukiyar tamu da mukai gado a wajan iyayen mu, ya zauna yaci gaba da juya mana ita acan qauye, mukuma muje birni muyi abinda muka ga yadace
A lokacin babu Wanda ya haihu acikin mu duka mu ukun, Bayan mun dawo Nan da zama a lokacin muka qara karatu, mukasa iyayenku mata a a makaranta, Antynku tana fara karatu Sai Allah yabata ciki, Tasha wahala a lokacin, Yaya Habu yazo ganinta, anan yake sanar damu cewa Shima me d’akinsa tasamu juna biyu, munyi farinciki sosai, Bayan wasu watanni Matar Yaya Habu ta sauka, Aka sakawa yaro suna Yahya, a lokacin muka shirya muka tafi jigawa Wajan suna, tun muna hanya Ummanku take cikin damuwa, saboda tasan zata had’u da danginmu na Niger a gidan Yaya Habu, Kuma sha’anin surutun dangi, tabbas Sai sun fad’a mata magana akan haihuwa, na tambayeta dalilin damuwar ta, ta fad’a min komai bata 6oyemin ba, ashe aloakcin Uncle d’inku dakuma Hajiya Anty, suna jinmu, munje anyi taron suna lafiya angama lafiya, abinda Ummanku take gudu saida yaso yafaru, domin kuwa duk Wanda yaga Anty Da tsohon ciki ita Kuma bata dashi saide su dinga yimata wani Gani-Gani, saida na tsawatar musu
Washe Garin haihuwar Yahya a ranar Antynku ta haifi Naufal, Halaccin da bamu ta6a tunanin zasu mana ba itada Usman shi suka mana, saida suka kira Yaya Habu Dani da umman ku, sannan suka d’auki Naufal suka bamu shi halak Malak, Dafarko naqi yarda nakar6a, saboda suma shi kad’ai suka mallaka, Amma sai Yaya Habu yace mana mukar6a tunda sune suka bamu, tunda ita Antyn tafara haihuwa insha Allah zata sake Haifar wani, Amma yanzu mubarshi ta shayar dashi, saimu kar6eshi, tunda muka dawo gida Ummanku take kula da Naufal, tsakanin sa Da Antynku shine shayarwa dakuma wasa irin na d’a da uwa, har Allah yasa aka yaye Naufal, tazo da kanta ta kawo mana shi,a lokacin yaqi yarda ya zauna damu duk da yasaba da ummanku, dare yanayi zai fara kuka yana Kiran Anty, haka muka haqura saida ya tasa, sannan ummanku ta kar6eshi, a lokacin da hankalin sa Sarai ya dawo gidannan, yasan komai, yasan bamu ne muka haife shi ba, Amma abun mamakin koda wasa baita6a nunawa wani cewa bamune iyayen saba.
Ahankali ahankali soyaiya take sake shiga tsakanin sa da ummanku, har suka saba babu inda zasuje ace shi ba d’anta bane, cikin dangi kowa yasan Yaro na Ummah ne Amma Anty ce ta haifeshi
Bayan wani lokaci tun muna jiran Antynku tasake haihuwa har muka gaji muka barwa Allah, muka d’auki son duniya muka d’ora wa Naufal duka mu hud’un, har tsawon shekara goma
A lokacin kamar wasa ummanku tafara zazza6i muna zuwa Asbiti akace tanada juna biyu, a lokacin Nan gidan Antynku tatare take kula da komai, har Allah yasa ummanku ta sauka ta haifi Yan biyu maza, nida Usman Muka sanya musu Suna Sa’ad dakuma Sa’eed
Daga baya tasake samun wani cikin muka sanya mata sunan mahaifiyar mu, wato Maryam, Bayan shekara biyar tasake haihuwar wasu yanbiyun muka sanya musu suna Intisar dakuma Ihsan, a lokacin munyi tunanin Usman da Antynku zasu kar6e Naufal daga wajanmu, Dan har Ummanku tafara zazza6i tana tsoron arabata dashi saboda yanda yashiga ranta, tasaba dashi fiye da ‘ya’yanta na cikinta, Amma koda wasa basu ce mu basu Shiba, Bayan shekara biyu da haihuwar su Ihsan muka sake Haifar Waheeda.
Tunda aka haifi Waheeda Naufal ya liqe mata, tun alokacin muda kanmu mukasan cewa yana qaunar ta sosai, shaquwar su ta daban ce, shine meyi mata wanka, shine goyo, shine siyo mata sweet, gashi ita Kuma batajin magana, Amma haka zai zaneta yamata hukunci yanda ya kamata, Dafarko munyi tunanin soyaiyar dayake mata ta aure ce, to damukaga yanda yake zaneta idan tayi laifi, yake mata hukunci irin Wanda koda ace mune zamu mata hukunci to irinsa zamu mata, Sai muka saduda muka daina tunanin komai akan alaqar su, muka bar komai a matsayin shaquwa,tunda yanbiyu maza kansu yana had’e, suma yanbiyu mata kansu ahad’e yake, Maryam kuwa tana d’akin mijinta, shiyasa bamu damuba Dan shaquwa me qarfi tashiga tsakanin Naufal Waheeda, to yanzu Kuma ga abinda Allah yasa ya kasance, wannan shine labarin. “
Shiru falon yayi, Ummah de tana mamakin Naufal Wai yau shine yake cewa yana son Waheeda, inda tasan cewa haka abubuwa zasu faru, da tuni Waheeda ta dad’e a gidansa, Hajiya Anty kuwa farinciki takeji acikin ranta, Allah yagani tana mutuqar kaunar Waheeda, tanaji da yarinyar sosai, Sai gashi yau Naufal d’inta yafad’i abinda yake ransa, dama ta dad’e tana wannan zargin, to Abaya tana tsoron ace ya nuna yana son Waheeda, saboda su kansu ba Susan tayaya zasu yiwa yaran bayanin abinda yafaru Abaya ba, Amma yanzu da Allah yasa hakan tafaru, ai shikkenan.
Yanbiyu sukai ajiyar zuciya, yanzu ashe Babban Yaya Yaron hajiya Anty ne?
Sukuwa su Sa’eed kasa magana sukai, haqiqa idan hakane sunfi kowanne qanne sa’ar samun Yaya nagari kamar Babban Yaya, Kuma Waheeda da taqi data so, Zaman aure dole 🤗
Wayar Daddy tayi qara, ya d’auka tareda fad’in, “minister yaya gida ya iyali?”
“Alhamdulillah Alhaji Umar, ashe Kuma abinda yasamu Waheeda kenan…”
Daddy yace “wallahi”
“kayi hakuri Alhaji Umar, kasan Yaron yanzu ka haifeshi ne baka haifi halinsa ba,Nan uwarsa ta zaunar dashi tagama hure masa kunne, Amma ba laifin Huzaifa bane, kuyi hakuri Alhaji Umar”
Daddy yayi wani murmushi me ciwo yace “Babu damuwa Alhaji, ai har wanima yafuto, Kuma mun bashi”
Cikin sanyin jiki minister yayiwa Daddy sallama, shi Kansa baiso Huzaifa yamasa haka ba, da har yana murna zai samu jikoki kyawawa 🥺
‘Yanbiyu ne suka tashi sukabi Bayan Waheeda d’aki, suna zuwa suka ganta a kwance akan gadon ta zubawa waje d’aya ido tana kallo tana zubar da hawaye
Zama sukai kusa da’ita, inti tace “Waheeda kiyi hakuri, nasan abinda ciwo mutum kana soyaiya dashi Amma saboda wata cuta ta sameka yagujeka, wallahi Huzaifa yabamu mamaki, Allah yasaka miki, Amma tunda bakida haqqinsa, ai gashinan yanzu kin samu Wanda yafi shi komai da komai, ga kud’i, ga kyau, ga aji, ga kwalliya, ga Kuma farin jini, sannan kinsanshi kinsan halinsa, uwa uba ma d’an uwanki ne “
Ihsan tace” wallahi kuwa, Allah sarki Didat Shima yabani tausayi wallahi, ashe da gaske yake yana son Waheeda, kiduba kiga yanda ya yarda zai aure ta a hakan, Amma yanzu tunda ga Babban Yaya Nan Shikkenan, saikiyi hakuri ki aureshi, Su Daddy sun fad’a mana Hajiya Anty ce ta haifeshi, saboda haka saiki daina cewa zakiyi Zaman Zina dashi… “