BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

A falon ta dinga doka sallama Waheeda tana kwance ad’aki tana jinta taqi futowa, Maya dataji shiru saita fara bud’e qofofin tana dubawa sannan tayi nasarar bud’e na Waheeda

Mamaki ya kamata ganin Waheeda idonta biyu, qarasawa tayi ta zauna akusa da’ita tace “qawata kiyi haquri, nayi tunanin kin huce shiyasa nazo, ashe har yanzu Ina Nan acikin ranki”

Ba tareda ta kalleta ba tace “aina fad’a miki NI DAKE har abada Maya”

Maya tace “subhanallah, Waheeda me yayi zafi haka?nad’auka namiki gata ne akan aurenki da Babban Yaya, ashe Bahaka bane Wai Waheeda harni kika shaqe duk qawancen mu”

Tashi tayi zaune, cikin masifa tace “eh na shaqe kin, kiyi abinda zakiyi, ai wallahi Maya Kin bani mamaki, banta6a tunanin dake za’a had’a baki a auramin Babban Yaya ba, kin cuceni kuma kin gama Dani”

Cikin sanyin jiki Maya tace “ban cuceki ba Waheeda, temakon d’an’uwanki nayi, Duk Wanda ya zauna daku zaisan cewa Babban Yaya yana sonki, Kuma nasan cewa bazaki ta6a samun masoyi kamar saba, Babban Yaya yana qaunarki Waheeda, Kuma kun dace da juna sosai”

“yanzu ke Maya idan kece akace ki auri yayanki Safwan zakiji dad’i?”

Maya tace “to menene aciki? Abu d’ayane zai dameni yanda zan sake inyi masa abubuwan soyaiya na aure, Kuma Shima lokaci ne ahankali zan saba, kema kuma idan wannan ce damuwar ki toki daina,Babban Yaya zaisa ki manta da cewa shi yayanki ne, sannan karki manta da qaddara, kowa da irin tasa,Kuma munyi alqawari zamu yarda da’ita me kyau ko marar kyau”

Waheeda tana jijjiga qafa cikin damuwa tace “shikkenan ya wuce, Amma karki sake min irin haka, ni banaso, Shima Kuma bazan iya zama dashi ba, saboda tsabar abun kunya rannan har kiss yamin, Ina zan Kai wannan rashin kunyar?”

Maya tasaki dariya tace “yakaiki rashin kunya ne? Keda kowa yasan halinki ne haka bakida kunya? To menene ma danya miki kiss? Haka zakiyi haquri ki yarda, kema kiyi masa, wannan shawarar dakika Bani de akan za’amin aure itace zata dawo kanki, haka Zaki kama abun mijinki ki wanke”

“Dan girman Allah Maya kidena min wannan maganar, kodan kinga na kulaki? Ni banason jin wannan abun kunyar,inrasa wazanyi wa hakan Sai Babban Yaya?”

Maya tace “aikuwa saiki maraba da kishiya”

Cikin rashin damuwa tace “kofa abud’e take, tazo ta zauna ban hanata ba”

Kafin Maya tace wani abu yanbiyu suka shigo d’akin, sunci kwalliya iri d’aya ko ganesu bakayi, abinci suka ajiye mata Ihsan tace “ke ga abincin ki Nan inji Ummah”

Kallan abincin tayi tace “wannan ai yayi mana kad’an, ko Babban Yaya zai iya cinyewa, yanda yake cin abinci idan yasamu waje to wallahi shi kad’ai ma zai cinye wannan”

Intisar tace “wanne Babban Yaya Kuma shida yatafi England? Ni jinake ma dake zai tafi, ashe shi kad’ai yatafi, ke yanzu Waheeda ba abun kunya bane wannan? Sabon aure Amma kibar ango yatafi shi kad’ai? Kyaje yakula wasu matan acan wallahi, tunda yanzu ya d’and’ana yaji dad’in mace “🙊😂

Cikin 6acin rai Waheeda tace” uwar me ya d’and’ana? Inti banason rashin mutunci wallahi, ba England ba, yatafi kafi England ma,dayau yafara huld’a da mata? Da idona na ganshi mata suna yanyameshi Sai yage musu baki yake, da idona nagani “

Ihsan tace” to babu so menene Kuma yakawo kishi? Keda kike cewa bakya sonsa miye dankinga mata suna yanyameshi? d’an ball nefa, ba mata ba mazama yanyameshi zasuyi, malama kinaso kina yiwa mutane ihu ke bakya so “

Tace” eh banaso, ba Kuma zan so ba, da yau yafara kula matan dazaku zo Kuna cewa nabarshi yatafi, inda ace nasan baya gidan ma da tuni Nima na kama gabana, Zaman me zanyi yanzun Ina masa gadin gida? Saikace wacce batada galihu, Nina tafi gida idan kun gama kwa taho “tafadi haka tana Jan hijabin ta tafice daga d’akin 😂😂

Babu yanda suka iya haka suka futo suka biyo bayanta, saida sukazo gida sannan Maya tamusu sallama tatafi gida, sukuma suka shige cikin gida, megadi Sai tsokanar Waheeda yake yana fad’in”Amarya kinsha qamshi”

Yau kwananta hud’u agida, Amma kamar bata gidan, Dafarko tayi tunanin zasu kulata, shiyasa take wuni ad’aki, dataga babu Wanda yake shiga harkar ta, saita fara futowa tana abin gabanta, daga Ummah har Daddy idan ta gaishe su daga sun amsa basa qara cemata komai, haka yanbiyu ma tun lokacin dasuka mata fad’a tamusu rashin kunya suka tattara ta suka watsar, Hajiya Anty tahad’o mata magungunan mata masu kyau, ta zaunar da’ita ta mata bayanin yanda zata dinga amfani dasu, sannan tabata haquri akan Takoma gidan mijinta, Amma Waheeda tayi mursisi taqi komawa, magungunan ma ta ajiye su taqi shan kod’aya aciki.

Yau satinta uku agida, Kuma har zuwa wannan lokacin bata kira Babban Yaya ba, Shima bai kirata ba, Kuma babu Wanda yace tattara kayan ki kikoma, kowa yazuba mata ido kawai.

Yau suna break fast afalo gaba d’ayansu, banda Daddy, Sa’eed ya kalli Waheeda sannan ya kalli Ummah yace “Wai wannan yarinyar Zaman me take a gidannan Ummah?”

Ummah ta Kalle shi tace “gatanan ka tambayeta”

Kallan Waheeda yayi yace “keme kikeyi har yanzu baki koma ba?”

Idonta ne yayi qwalqwal yakawo ruwa, tana juya spoon acikin cup d’in tea d’in dake gabanta tace “ni Bana sonshi….”

Sa’ad yayi sauri yace “to cemiki akai shid’in sonki yake? Banda qaddara ma me Babban Yaya zaiyi dake? Ga yanmata Nan had’ad’d’u suna bibiyarsa zai tsaya anan Ana Rena masa Hankali”

Sa’eed ma yace “okay bakya sonsa ko? To Alhamdulillah, Ummah kawai idan yazo kibashi shawara yasake ta kawai”

Ummah ta ajiye bread d’in hannunta tace “na fad’a masa tun shekaran jiya da mukai waya, idan yasamu lokaci Yazo ya rubuta mata takardar, saisu koma makaranta itadasu Ihsan”

Sa’eed yace “Hakan ma yafi, Dan wannan yarinyar Dama ba ajin auren sa bace, kawai de Dan Allah ya rubuta Sai anyi ne, ni Gara ma dayake shirya abinda yafi masa, abinda Yayanke d’in yayi daidai, yanzu ne yasan zaiyi aure”

Gaban Waheeda yayanke yafad’i, ahankali ta zaro idonta 😳batare datace komai ba

Shima Sa’ad yace “eh gaskiya Kam ya kyauta”

Hajiya Anty ce tashigo falon zata yiwa Ummah sallama kamar yanda tasaba idan zata tafi wajan aiki, tajisu suna fad’in eh ya kyauta Kam tace “waye ya kyauta?”

Ummah tayi murmushi tace “Wai suna magana ne akan auren yayansu, kinsan jiya Daddynsu yamasa waya yace idan zai taho yahad’o wasu kayan lefen Sai akai gidansu ummin, tunda tabada haquri Kuma Shima Naufal d’in yace ya haqura zai aure ta” 😂

Waheeda taji numfashinta yana yin sama kamar zai d’auke, gabanta Sai fad’uwa yake, takasa d’agowa ta Kalle su, sukwa yanbiyu Sai lodar abinci suke ko bakinsu ba’aji

Hajiya Anty ta kalli Waheeda tace “yanzu Yaya ba zakuyi haquri da maganar Ummin nanba? Ayita yin abu de? Duka duka yaushe yayi aure dazaku sake da’aura masa wani auren?”

Ummah tace “to Antynsu Yaya zanyi dashi? Jiyafa kirana yayi kamar zaiyi kuka shide ayi ayi a aura masa Ummi,yanaso yazo gobe ko jibi ayi agama magana, so yake yazo yatafi da’ita England, ita Kuma Waheeda tunda tana zaune agida, saitaci gaba da Kula da gidan, idan sukazo hutu kinga har saga gida tsaf dashi ‘yar aiki ta gyara musu “

Waheeda tacika tacika tazo wuya, batasan lokacin data Fashe da Kuka ba, cikin gudu tayi d’akinsu tad’auki wayar inti takira Maya, bugu biyu Maya ta d’auka tace”inti ya akayi Ina qawata? “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button