BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kowa Matsowa yayi kusa da Daddy duk suka taru suka yanyameshi, Daddy daya ga haka saiya saka wayar a hands-free, harta katse bai d’auka ba, saida yasake kira Akaro na biyu sannan yada’auka, kuka yafara ji yana tashi sama sama Kuma ba kukan mutum d’aya ba, cikin ransa yace sunga abinda yafaru kenan

Daddy yace “Son, kana lafiya? Yaya jikin Naka?”

Kafin Babban Yaya yayi magana Ummah ta qwace wayar, cikin kuka tace “kafadamin halinda kake ciki, Hankali na yakasa kwanciya, sonake nataho, bazan iya zama ba”

Ahankali yace “Ummah…., ki kwantar da hankalinki, anduba min qafar, harma sun Bani injury, zan dawo gida insha Allah”

Cikin kuka Ummah tace “karka dawo in kasan jikin babu sauqi, mu saimu biyo ka”❤️😂

Memakon yabata amsa saiyace “Ummah Ina Anty? Ina Waheeda?”

Wayar tamiqawa Hajiya Anty, Anty ta share Hawayen idonta, sannan takar6i wayar tace “sannu Naufal, yajikin naka?”

Ahankali yace”jiki da sauqi Anty, kikulamin da Waheeda nasan Hankalinta yatashi “

Anty batayi magana ba, saita Bawa Waheeda wayar, saboda tasan yana jin nauyin ta bazai iya cewa tabawa waheedan waya ba, Waheeda kuwa tana kar6ar wayar Takoma Gefe, kuka take sosai takasa magana, cikin sanyin murya yace”kiyi shiru…, ba sosai bane ciwon”

Cikin kuka tace “kayi hakuri nadena, daga yanzu nadena hanaka komai, naji tsoro sosai, jinake kamutu”

Wani irin dad’i yaji ya ratsashi, yanzu Kam yagama tabbatar wa Waheeda tana sonsa, saboda haka wannan ciwon Koya warke bazai nuna mata hakan ba, yasamu mafaka ta yanda zai dinga zuba mata shagwa6a son ransa

Ahankali yace “I luv you so much…….muahhhh,, muahhhh” 💋💋

Yasakar mata kiss har biyu ta cikin wayar, sannan yaci gaba da fad’in “kimin addu’ah kinji, insha Allah zanji sauqi, jeki kaiwa su Daddy wayar

Tace”to” sannan tatashi takai musu wayar, Sai a lokacin Hankalinta ya kwanta, Sai ajiyar zuciya take, jikin Hajiya Anty Takoma ta lafe kamar wata mage, bata Jima da kwanciya a jikin nataba bacci yasoma d’aukarta

Yana gama wayar dakowa acikinsu harda junior, sukai sallama Bayan yagama kwantar musu da Hankali, Kiran mashkur ne yashigo wayar tasa, d’auka yayi tareda sallama, mashkur yace “friend mutanan nanfa sun hanamu shigowa Dakin, sunce har yanzu kana buqatar hutu, Sai lalla6a ka suke kamar qwai”😂

Murmushi yayi yace “rabu dasu mashkur, zamu hadu ai idan nafuto insha Allah, ciwon fa Bana kirki bane, kawai tsagewar qashi ne, da niyya na langwa6e musu, nagaji da ball d’in Dama hanyar guduwa wajan amarya ta nake nema, to Kuma Sai haka tafaru…..” 🙊

Mashkur ya kwashe da dariya yace”wato me jiran kukane aka jefeshi da kashin awaki, banga laifin ka ba Abokina,Naga ma sun sanar katafi injury, Kasha Amarci lafiya….”

Babban Yaya yayi murmushi yace “thanks Friend”

Pls kuyi hakuri Dan Allah 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
1/28/22, 20:52 – Ummi Tandama😇: RD

Basu sukabar falon ba Sai wajan karfe uku da rabi, a ranar daga Waheeda, har Ummah da Hajiya Anty, basu runtsa ba, su Waheeda suna zuwa daki alwala tayi tazo tafara sallah tana yiwa mijinta addu’ah Allah yakare mata shi, su kansu yanbiyu da Anty Maryam sunyi mamakin Waheeda, sun kuma tabbatar lalle aure yana saka mutum nutsuwa da Hankali, gashi de kamar ba Waheeda ba 😂

Da safe wani irin zazzafan zazza6i yarufe ta, babu 6ata lokaci Hajiya Anty tayi mata allura, sannan bacci me nauyi ya d’auketa

Koda suka sake Kiran wayar Naufal yana tambayar su ita, suka fad’a masa tana kwance batajin dad’i

Wasa wasa saida Waheeda ta kwashe kusan sati d’aya a kwance batada lafiya, kullum tana d’aki a kwance cikin blanket, Hajiya Anty duk ta damu,yau shiryawa sukai suka tafi Asbiti, suna zuwa tayi mata awon fitsari tayi tunanin ko ciki ne 🙊
Amma da result yafuto saitaga babu komai, akayi mata text aka Gano typhoid ne, anan suka had’o magunguna suka dawo gida

Tana fara amfani da magungunan kuwa cikin ikon Allah ta warware 👌🏻

Amma kana ganin fuskarta zakaga tayi wani irin haske, ita kanta Ummah tayi tunanin cikin ne, saida taga result d’in Nata sannan ta yarda batada ciki

Kwanan Babban Yaya Tara, yaji dad’in jikinsa, dama Allah Allah yake ya dawo gida, aikuwa Ana sallamar sa yayiwa Ummah waya yafad’a mata gashinan zuwa

Waheeda tanajin labari tafara had’a Kaya 😂
Ihsan dake maqale da waya a kunnan ta tana magana da mashkur ta kalleta tace “Ina Zaki ne?”

Kai tsaye tace “gidana”

Intisar ta kwashe da dariya tace “su Waheeda masu gida,yau Kuma keda kanki kike cewa gidanki Zaki tafi?”

Cikin gundura da zancen nasu tace “to saina zauna anan haka kawai Bayan ga mijina can yana hanya? Sai in zauna yazo yaganni Ahaka ya rainani?”

😳Zaro ido inti da Ihsan sukai, sunji abun mamaki Wai Babban Yaya ne zai rainata, kafin suyi magana Waheeda tasaka hijabin ta tad’auki jaka tafuto tareda ja musu qofar

Afalo Ummah da Hajiya Anty suna zauna, suna Magana akan abincin da za’a tsara wa Babban Yaya, sukaga Waheeda tafuto, Hajiya Anty tace “Ina zakije Daughter?”

Cikin qasa qasa da murya tace “gida”

Hajiya Anty ta girgiza kanta alamun batajiba, sannan tace “mekika ce?”

Ummah tace”cewa tayi gida zata tafi, tana nufin gidanta, gidan mijinta”😂

Turo baki gaba Waheeda tayi cikeda shagwa6a, batace musu komai ba,Hajiya Anty tace “to kije driver yakaiki, Allah yakiyaye hanya”

Daga musu Kai tayi, sum sum tafice daga falon, Hajiya Anty ta kalli Ummah tace “Zamani,mu muna shirin tar6arsa anan, kinga ita Kuma tatafi gidanta”

Ummah tayi dariya tace “hmm ai kad’an kika Gani” 😃

Kafin Hajiya Anty Tayi magana, wayar Babban Yaya tashigo wayar Ummah, cikin sauri ta d’auka tana fad’in “kinga ma yana kirana,inaga sun sauka”

Dauka tayi tareda fad’in “Son kun sauka?”

Daga nasa 6angaren yace “eh Ummah, Gani tareda su Sa’eed….”

“a a, to me kuke jira? Ku qaraso gida mana, karka tsaya mutane su dameka dayawa nasan idan kahad’u da mutane bazaka qaraso dawuri ba”

Cikin kunya yace “a a Ummah… Dama… Dama zan fad’a miki ne, na wuce gida, idan nahuta zanzo” 🙊😂

Ummah tasaki baki tana Kallan Hajiya Anty, ita batayi masa magana ba, ita bata kashe ba, Sai can taji yace “Ummah bakya ji?”

Cikin mamaki tace “inaji yayansu, to Allah yakiyaye hanya saika shigo d’in”

Cikin farinciki yace “Amin Ummah, I miss you” dif yakashe wayar

Hajiya Anty data gama jin komai ta kwashe da dariya tace “Hajiya, yaran nanfa Dama bakinsu ahad’e yake, gaba d’ayansu magulmata ne, kinga Shima damuke shirin tar6a ya wuce wajan matarsa,kinji magulmaci harda cewa I miss you, ai shikkenan Nima Bari intafi gidana, babu amfanin Zaman” tafad’i haka tana miqewa tsaye

Ummah bata iya magana ba Sai cewa tayi “to Antynsu Sai munyi waya” 😃

*** ** ***

Tana zuwa gida tagama gyara komai, gida yayi fes ko’ina yad’auki qamshi, tasaka doguwar Riga ta leshi me mutuqar tsada, ta zauna ta tsara kwalliya, tasaki dogon gashinta gadon Bayan ta, abinci ta had’a masa d’an kad’an dede yanda tasan idan yagani zai birgeshi, sannan ta zauna afalo tad’auki littafin addu’ah tana dubawa, wajan minti talatin taji tsayuwar mota, littafin ta ajiye tatashi ta nufi qofa, tana bud’ewa suka kusa cin Karo da juna cikin tsananin murna tayi wani irin tsalle ta rungume shi, murmushi yasaki, Shima yasaka hannu yasake rungume ta tsam ajikinsa tareda Lumshe ido yana sakin wata irin ajiyar zuciya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button