BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Washegari kuwa kasa kallan sa tayi 😂
Yana Kallan ta yana murmushi, ko yayi mata magana kanta a sunkuye take bashi amsa, duk ta takura kanta kamar ba Waheedan muba 💃
Yau tsawon kwana hudu kenan, kullum Sai Babban Yaya yanemi haqqin sa awajanta, Amma Waheeda taqi yarda, yana farawa zata fara yimasa kuka, shikuma baya son kukan ta, yana ganin tafara kukan saiya haqura, cikin kwana na biyar d’inne wajan aikinsu suka masa waya zasu buga wasa tsakanin su da Algeria, Kuma harda shi aka za6a acikin Wanda zasu buga qwallon
Baqin ciki yakama Babban Yaya, kawai to ya cewa couch d’in nasu, saboda beso hakan ba, yaso ace yamaida Waheeda cikakkiyar mace kafin ya dauketa sutafi honeymoon dinsu.
yauda safe suna gama cin abinci ya kalleta yace “kishirya zan maidake gida”
Cikin sauri ta Kalle shi, tayi tunanin wani laifin tayi, tace “meyafaru Babban Yaya?”
Kafad’a ya d’aga yace “an kirani ne, a wajan aikina”
Ajiyar zuciya ta sauke, tayi tunanin wani laifin tayi, zaice zai maida ta gida,ahankali tace masa “to yaushe zaka dawo?”
“babu rana” yafad’i hakan ransa a6ace, itama tanajin wannan furucin taja bakinta tayi shiru, tasan cewa ransa a6ace yake
Bata d’auki komai ba, kawai hijabinta tasaka, suka tafi, suna zuwa compound din gidan Ummah yayi parking,kafin suyi sallama yajuyo ya kalleta yace “karki dinga wasa dasu Ihsan har kuzo Ana rabaku akan abinda baikai yakawo ba,nasan halinki bakida kunya, kikama girmanki, da da dayanzu ba daya bane, duk abinda kike buqata kidauki ATM dina kije ki siyo kokuma kisa su Sa’eed su siyo miki”
Tace “Babban Yaya, kaida kace yanzu na girmi Ihsan nikuma tayaya zan kulasu har muyi fad’a?”
Cikin sauri yace “tayaya kika girmesu? Bayan kinqi Bani damar dazan maidake Antyn su?, Ina ta6abaki Sai kuka, ko bakya jin dad’in abinda nake miki?”
Yafadi hakan yana Lumshe Idonsa
Wata irin kunya ce takama Waheeda, tasaka hannunta tarufe fuskarta, Sai yanzu ne tagane inda yadosa, ashe Dama Abaya haukanta take tana hura hanci ita tazama babba, ashe wannan abun ne girman, cikin sauri ta6ud’e motar tatafi da gudu, ajiyar zuciya yasaki yanabin Bayan ta da kallo harta shige falo, sannan yayiwa driver magana yazo yajashi suka tafi
Satinsa d’aya da tafiya Waheeda taci gaba da zuwa makaranta dayake exam ma suke, yanzu tayi Hankali ta nutsu ta daina hauka, ko agida haka zaka ganta a zaune waje d’aya, wani lokacin har kunyar Ummah take ji saboda Gani take duk abinda yafaru tsakanin ta da Babban Yaya Ummah tasani, haka kawai saita dinga tsarguwa idan tana cikin su, da daddare kuwa kasa bacci take, tana ganinsu Ihsan suna kwasar baccin su Amma ita saide taita juye-juye, Kuma ba komai ne yake damunta ba Sai tunanin mijinta, Ida tunanin yayi yawa harji take kan nononta yana mata qaiqayi, saide tasa hannu ta Sosa Amma hakan bazai Hana anjima tasake jin wani qaiqayin ba, idan ta kirashi da wayar su Ihsan baya d’auka, saboda yasan itace, Sai yanzu ne take DANA SANI (first novel) akan hanashi haqqinsa da tayi ta dinga wahalar dashi, Sai yanzu yake bata tausayi, yau Satinsa biyar da tafiya, a ranar ne Kuma su Waheeda suka gama makaranta, sannan a ranar ne zasu buga wasansu, Hajiya Anty da Uncle Usman duk sunzo gidan antaru za’a kalli ball d’in, Anty Maryam itama tazo harda junior me sunan Babban Yaya, gaba d’ayansu sun nutsu kowa hankalin sa yana kan TV, Waheeda tana Gefe tana kallo itama,carbi ne a hannun ta Sai addu’ah take cikin ranta Allah yabawa mijinta nasara, dayake addu’ar mata akan mijinta batada hijabi a wajan ubangiji,cikin ikon Allah Ana fara wasa kuwa Babban Yaya shine mutum nafarko daya fara Ci, yana ganin yaci ya tsugunna yayi sujud shukr.
su Sa’eed suka tafa shida Sa’ad, falo kowa yafara murna
Wasa yayi wasa kowanne team sunaso sunga sunci, har tsawon wani lokaci sannan wani d’an team d’in su Babban Yaya yaciyo musu, Babban Yaya yana kar6ar Ball d’in ya dinga Sakata araga, saida yaci Sau uku ajere, Bayan guda d’ayan daya faraci, gudu yake sosai yana d’aga hannu, Yan team dinsu suna binsa Abaya, cikin murna suka rungume shi, Ummah bakinta yaqi rufuwa, Sai murmushi take idonta yana kan TV, su Daddy da uncle ma sunyi shiru kowa yana Gani, Hajiya Anty de addu’ah take cikin ranta Allah yakare mata d’annata, Allah yasake d’aukakashi yad’ora shi akan maqiyansa.
anci gaba da wasa kenan Babban Yaya yasake nasarar kar6ar qwallo daga wajan d’ayan team din, ya d’aga qafa zai bugata kenan Shima wani yakawo tasa qafar jikake qassss, yabige qafar Babban Yaya, lokaci daya jama’ar dasuke studio din suka fara fadin ohhhhh!
Lokaci daya hankalin masoyansa yatashi, suka miqe tsaye, cikin azaba Babban Yaya yariqe qafarsa yana runtse ido
Waheeda taji kunnanta yayi mata wani dimmm haka kamar bataji, kamar Kuma a mafarki, miqewa tayi tsaye tanufi gaban TV, gabanta yana fad’uwa, tuni hawaye suka wanke wa Ummah fuska ganin ankawo wani irin gado marar qafa, andora Babban Yaya akai, anfita dashi daga filin wasa
Kallan Daddy tayi cikin kuka tace”Alhaji tafiya zanyi, sun kashemin Dana “
Cikin tashin Hankali daddy yace” Ina zakije Hajiya? Kiyi hakuri mana “
Uncle Usman yafara neman wayarsa, Hajiya Anty ta Kalle shi cikin rawar murya tace” bazaka sameshi ba, yacemin kashe wayarsa zaiyi idan zasu fara wasan “
tana fad’in hakan hawaye yazubo daga idonta, su yanbiyu ne suka janyo Waheeda, Sai girgiza kanta take tana hawaye Amma takasa magana, Sa’ad yatashi yakashe Kallan, Anty Maryam tariqe Waheeda tace” kiyi hakuri Waheeda, insha Allah zaiji sauqi “
Cikin kuka tace”niku rabu dani, ku d’in shiru zakuyi idan mijinku ne?, Dan Allah Dan Annabi Daddy kabarni natafi, dama fishi yake Dani, qilama nice sila…..”
tafadi hakan tana fashewa da wani irin kuka
Hajiya Anty ta rungume ta tana bubbuga Bayan ta, babu Wanda baiyi kuka ba acikinsu, saisu Daddy kawai, suna mutuqar qaunar d’an’uwan nasu, haka suka zauna shiru suna faman addu’ah, shide ba’a Nigeria yake ba bare sutafi koba visa, a wata qasa yake, Kuma yanzu dare ne dole zasu jira suga wanne mataki qungiyar tasu zasu dauka akan ciwon da yaji
Babu Wanda yayi yunqurin kwanciya acikinsu, kowa wayace ahannunsa yana try number Babban Yaya ko zata shiga, Waheeda ce kawai babu waya Sai faman kuka take har numfashin ta yana sama kamar wadda take shirin suma, Sai wajan karfe biyu sannan cikin sa’a Daddy ya sameshi, cikin sauri ya miqe tsaye yace “Alhamdulillah tashiga, yabud’e wayar”
Kowa Matsowa yayi kusa da Daddy duk suka taru suka yanyameshi, Daddy daya ga haka saiya saka wayar a hands-free, harta katse bai d’auka ba, saida yasake kira Akaro na biyu sannan yada’auka, kuka yafara ji yana tashi sama sama Kuma ba kukan mutum d’aya ba, cikin ransa yace sunga abinda yafaru kenan
Daddy yace “Son, kana lafiya? Yaya jikin Naka?”
Kafin Babban Yaya yayi magana Ummah ta qwace wayar, cikin kuka tace “kafadamin halinda kake ciki, Hankali na yakasa kwanciya, sonake nataho, bazan iya zama ba”
Ahankali yace “Ummah…., ki kwantar da hankalinki, anduba min qafar, harma sun Bani injury, zan dawo gida insha Allah”
Cikin kuka Ummah tace “karka dawo in kasan jikin babu sauqi, mu saimu biyo ka”â¤ï¸ðŸ˜‚
Memakon yabata amsa saiyace “Ummah Ina Anty? Ina Waheeda?”