BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Karfe hudu daidai, gaba dayansu yanmatan su uku suna falo kowacce Sanye cikin uniform din islamiya Mai launin light blue, sungama shirya wa Ihsan ce kawai bata saka hijab ba
Intisar tadubi Waheeda “Waheeda Dan Allah ki Ara mata hijab din, inda taga Nata ai bazatace ki Ara mata naki ba”
Yatsina fuska tayi tace “tabdi, ai saikuyi Kuma,dazu dazunnan tagama cemin marar Hankali ta6a66iya, tayaya zata saka kayan ta6a66iya?, kunifa Bari kuji banida mutunci akan kayanaaaaaa” taja naaa din sosai sakamakon tozali datayi tashi a bakin kofa yana qoqarin shigo wa falon nasu,dayake itace take kallon bakin qofa, sukuma ita suke kallo suna roqarta hijab,lokaci daya taji tanemi nutsuwar ta tarasa, taji kanta yasara tundaga qeyarta har zuwa goshinta, fuskar Nan tasa atamke, yahade girar sama data qasa, shikkenan magana ta qare, tasan yau takade har ganyenta, yaji labarin meta aikata
lokaci daya tanutsu, cikin tsananin ladabi ta kalli Intisar tace “kidauki hijab din nabaki duka, kinga wannan dayan bashida guga, Bari nadaukeshi, kekuma saiki dauki gogaggen” 😂
Cikin falon ya qaraso, qamshin turaren sa ne yasa yanbiyu juyawa cikin sauri,suna ganinsa suka juya suka kalli Waheeda, Sai yanzu suka gane abinda yasa ta basu Aron hijab din.
Wajan sa suka nufa cikin ladabi sukace “Babban Yaya sannu da zuwa”
Hannunsa ya daga musu kawai,tareda zama acikin kujerun dasuka qawata falon nasu masu launin dark green, cikin murna suka tafi Dakin Ummah suna qwala mata kira, suna zuwa suka tarar tana toilet
Kallan Waheeda yayi wadda ta qame a wajan tun shigo war sa, yamiqe tsaye batare daya kalleta ba yace “ke biyoni”
Gabanta ne yake wani irin bugawa dak! dak!, tafiya take tana binsa Amma jitake kamar batada nauyi, jitake kamar iska zata Iya dagata sama,suna shiga Dakin nasa wani irin qamshi yadaki hancinta,Dakin ya qawatu da manyan pictures dinsa, dayawa daga cikinsu duk da kayan ball yayi photon, qamewa tayi daga Nan bakin qofa saboda bai bata iznin qarasowa tsakiyar Dakin ba, takunkumin dayasa a hancinsa yafara cirewa sannan ya kalleta yace”Kneel Down here”
Cikin sassarfa taqaraso cikin Dakin tazube gwiwarta aqasa tareda daga hannayenta sama, zama yayi agefen gadon yafara cire takalmin qafarsa, sannan ya tashi tsaye yacire rigar jikinsa, farar fatar jikinsa ta bayyana, murdaddan Hannunsa yasake futowa sosai, duk abinda yake idon Waheeda quriiii akansa, tunda taga yafara cire Kaya take qarewa surar jikinsa kallo, cikin ranta tace tunda Naga yafara cire Kaya inaga yau zamu raba raini, hukuncina nayau yafi qarfin duka saide dambe 😂
Wayarsa ce tayi qara ya dauka tareda bude fridge din Dakin ya dauki ruwan gora, sannan ya dawo ya zauna, cikin aji yayi sallama yana fadin “wake magana?”
Daga d’ayan bangaren akace “ranka yadade Big Brother, Shema’u ce, Shema Lady, yanzu na bude data ne, sainaga Ana bada labari kazo, ashe ka shigo gari yau”
“no, qaryar Yan media ne kawai Shema, banzo ba”
Fari tayi da idanunta, taji shi ne kawai, Amma bata yarda ba, cikin salon yaudara tace “Big B. Kenan, saika ganni kawai” qit takashe wayarta, wayar ya janye daga kunnansa ya kalli screen din wayar, aiko saboda wayar data kashe masa yanzu koda ace tazo, bazai saurareta ba, saboda ba’a kashe masa waya saide yakashe
Tashi yayi yafara kokarin janye dogon wando jeans din jikinsa, har boxer din yafara bayyana yajuya ya kalli Waheeda yaga ta qwara masa ido tana Kallan sa 😂, saiya fasa cirewa yamiqe tsaye yana mata wani irin kallo, cikin sauri ta runtse idonta, saida yaga tarufe idonta sannan ya qarasa cire jeans din, dagashi Sai gajeren wando yashige cikin toilet dinsa, tanajin shigarsa tayi wata irin ajiyar zuciya sannan tasauke hannunta qasa, sau dayawa tana mamaki sosai dangane da tsakanin ta da yayan Nata, kamar bashine yayanta me sonta ba, bazata taba manta lokacin dazai dauketa ya goyata abayansa yana zagaye compound din gidan da’ita ba, Amma tunda ta girma, komai ya sauya, yadena wasa da’ita, yahanasu kula Samari, yahanasu saka mayafi, idan tayiwa Ummah complain tace ai saboda bataji ne shiyasa Shima ya sauya mata, Kuma mema take aika tawa dazaibi ya tsaneta? ðŸ˜â˜¹ï¸Idan akan samari ne tayaya za’a Hanasu kula samari Bayan sun kusa yin candy, idan suka gama makaranta babu saurayi qarshan zancen ace za’a hadasu da samarin dangi, ayi musu auren zumunci, Kuma a wannan zamanin waye zaizo auren cushe, auren zumunci?
Tanajin alamun bude kofar toilet din tayi sauri ta daga hannun ta sama
Be kalli inda takeba, Kai tsaye gaban mirror ya wuce yana gogo lallausar sumar Kansa ta buzaye da wani Dan qaramin towel, saikuma wani dayake daure a qugunsa, nocking din Dakin akayi, ya dakata da abinda yake ya kalli kofar tareda fadin “shigo”
Sa’eed ne yashigo da wata leda ahannunsa me d’aukeda kudade Yan dubu dubu, ya rissina cikin ladabi yace “Bà bà ñ Yaya an canzosu”
Turare yafara fesawa a jikinsa yace “kaje kaida Sa’ad ku rabasu dubu goma goma, a saka kowacce dubu goma cikin Envelope, anjima idan mun fita masallaci Sai arabawa mabuqata”
Waheeda tanajin zancen dubu goma tayi sauri tabude idonta, kudin ta kalla tagansu dayawa yanzu duk wannan mabuqata zai bawa?jitayi kamar taje ta qwace, Gata, gasu yanbiyu agida suma ai mabuqata ne 😃
Sa’eed ya kalli Waheeda yadaka mata harara sannan yafice daga Dakin yaja musu qofa,tunda yaganta a Dakin yasan laifi tayi
Kallan Babban Yaya tayi taga ya Dauko wasu kayan zai saka, maimakon ta dauke idonta saita qura masa ido, yana Kallan yanda take kare masa kallo tagefen idonsa, ya tabbatar Waheeda raini takeji, tunda har zata Iya zuba masa ido har haka tana Kallan sa to yasan cewa Dan ance namiji yasha bakinta ba za’ayi qarya ba, da niyya yajuyo ya fuskanceta sannan yafara kokarin cire towel din guqunsa, idan wani abun take so tagani saita Gani da hujja😂
Gaban Waheeda ya yanke yafadi, cikin sauri ta runtse idonta, cikin qasa qasa da murya yace “Ashe ke qaramar ‘yar’iska ce”
Ita Kuma tayi tunanin magana yamata, tunda Dama haka yake magana qasa-qasa kamar baiso, gudun kartayi laifi yace yayi mata magana ta qyaleshi shiyasa ita Kuma ta daga murya tace “Na’am Babban Yaya Dani kake?”
Dawowa yayi ya zauna agefen gadon, Bayan yagama shirya wa tsaf ya kalleta yace “badake nakeba qaramar marar mutunci, kullum aka ganni a Nigeria ta dalilin ki ne nake zuwa, haka kawai Ina Kan har kokina saikin aikata abinda zaisa dole sainazo qasar Nan, ke wacce irin mahaukaciya cene? Kwata kwata bakida aji bakida Hankali irinna yanmata, anturaki makaranta ashe soyaiya kike harda su kiss, nakafa doka a gidan Nan kina take wa yafi a qirga, saboda ga sa’anki, to yau idan jikinki yagaya miki, ko ance ki kalli samari ma bazaki kallesu ba, dangane da makaranta Kuma nasan matakin dazan dauka a kanki”
Yana kaiwa Nan ya tashi yafice daga Dakin, Waheeda tafashe da Kuka, cikin kuka tace “Nashiga uku na, ashe yaji, shikkenan Aryan yacuceni, Allah ya’isana” haka taci gaba da kneel down tana kuka, babu damar tatashi yazo yaga tatashi nanma taqara wani laifin, tun yanzu ma jitake gwiwowinta harsun fara zafi
Yana futowa daga Dakin yatarar da Dady da Ummah a zaune, gaida su yayi cikin ladabi sannan yakoma gefen Ummah ya zauna tareda Dora Kansa akan kafadarta yace “Ummah”