BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Idan ta zauna kuwa wuni take a zaune, babu kunya Babban Yaya zaizo yasa ta agaba su zauna, duk abinda take buqata kawai fada masa zatayi, haka zai kama hannunta su dinga zagaya gidan suna tafe suna zancen su na masoya

Ranar biki kuka kawai take, yanda taga yanbiyu sunyi shiga Mai kyau Kaya yayi musu cif cif ita kuwa Qin shigarta yayi, dole Sai Hajiya Anty ce tasa akayi mata sabon dinki a ranar, akayi mata doguwar Riga bubu, akasa Mai kwalliya itama tayi mata, duk wani party da aka shirya dasu walima Babban Yaya yana tare da ita, idan yaga tagaji Nan da Nan zai kawo hannu ya d’auketa, ko kadan bayason abinda zai taba lafiyar cikin Nan

Anyi biki lafiya, ankai amare gidajan mazajensu Wanda Babban Yaya ya gwangwaje su dashi, gida iri daya Kuma kusa da juna

Dayake yanbiyu ne matan nasu Nan da Nan Sai kansu yahadu da su yanbiyu, ko ranar bikin haka photonsu ya dinga yawo a yahar gizo, yanbiyu sun auri yanbiyu, ga Kuma wasu Yan biyun qannan mazajen

Cikinta yana wata takwas, akasa bikin Maya wata daya Mai zuwa,Waheeda tayi farinciki tasan zuwa lokacin ta haihu

Maya tana zuwa gyaran jiki Amma koda yaushe tana tareda Waheeda, idan suka zauna wani lokacin sai tayi tagumi tana kallon qawar Tata, kowa yaganta saita bashi tausayi, Shima Babban Yaya duk nacinsa saida ya haqura ya daga mata qafa, saide tayi masa wasu Yan dabaru harya gamsu

Bikin Maya yarage sati daya, idon Waheeda yaraina Fata, haihuwa shiru shiru batazo ba, Hajiya Anty ta duba taga babu komai, Babyn ta yana cikin qoshin lafiya, haka Maya zatazo gidan sutafi tare dasu yanbiyu, duk wani abu sune kan gaba, wani zaiyi tunanin ma Yan gidansu Mayan ne, Amma duk Wanda yaji cewa yayun Waheeda ne, to saiya daina mamaki saboda kowa yasan tsakanin Maya da Waheeda akwai qauna😂

Ranar Daurin aure tun safe Waheeda ta shirya, tayi kyau sosai cikin leshi hand bag dinta tana gefenta, tayafa mayafi Dan qarami taci magani tana jiran Babban Yaya, Dan tasan inde yaganta da mayafi zasuyi tashin Hankali

Futowa yayi cikin shiri yayi kyau sosai cikin shadda kalar leshin jikinta, kallon ta yayi yace “kije ki shirya mana,tun safe kin tasheni, Kuma Naga baki shirya ba”

Kallonsa tayi tace “aina shirya”

“kije kinemi hijab, tayaya zakije da wannan mayafin, wallahi saide mufasa zuwa”

Kallansa tayi duk ranta adagule, dama jitake kamar ta Fashe da Kuka, bikin maya guda, Amma babu ita
Tace “Naga har kofar gida zaka kaini amota Kuma……”

kafin ta qarasa magana taji mararta ta daure, ga bayanta da yayi wani irin amsawa, lokaci daya ta dora hannunta a mararta, ta runtse idonta tasaki wani irin ihu

Cikin sauri Ummah tafuto aguje, Babban Yaya yarikice yarasa Yaya zaiyi mata, Ummah tana qaraso wa tace masa dauketa muje naquda ce,daukan ta yayi cikin tashin Hankali yanufi mota da’ita, Ummah takira Hajiya Anty tasanar da’ita, duk suka hadu a Asbitin

Tun misalin shadaya sukazo, Amma har qarfe hudu Waheeda bata sauka ba, suna haka aka kawo wata yarinya itama haihuwar ce,Ana shiga da’ita Dakin haihuwa Wanda suka kawo ta suka qaraso wajan su Ummah suka zauna, mamaki ne ya kamashi ganinsu Ummah da Hajiya Anty , cikin mamaki yace “Anty ashe kune?”

Babban Yaya yanajinsa bai d’ago ya Kalle shi ba, tunanin Waheeda kawai yake, ko awanne Hali take ciki?

Anty tace “Didat? Ashe kaine, wallahi bamu lura ba”

Babban Yaya yana jin ance Didat yadago Kansa, Hajiya kakar Didat kunya ta kamata, daqyar ta’iya gaisawa dasu Ummah

Didat yace “wallahi nakawo matatane haihuwa, waye babu lafiya Ummah?”

Ummah tace “Waheeda ce, itama haihuwar ce”

Yayi shiru jikinsa yayi Sanyi, ahankali yace “Allah yasauke su lafiya”

Ko awa daya basu qaraba, matar Didat ta haihu, Allah ya Albarka ceshi da samun ya mace, doctor tana bashi Babyn yakawo wa su Ummah ita yace “Ummah ga Waheeda, kusa mata Albarka”

Ummah ta jijjiga Kai tana mamakin Didat, soyaiya kenan, addu’ah sukayi wa yarinyar, sannan ya karbeta yabawa Babban Yaya ita yace “ga takwarar Waheeda, kayi mata addu’ah”

Babban Yaya ya karbi Babyn yana kallon ta, yasaka bakinsa a kunnan yarinyar yana mata addu’ah, doctor’s suka futo hannun su d’aukeda Baby’s suka Bawa su Hajiya Anty tareda fadin “tasauka lafiya, ansamu yanbiyu mace da namiji”

Cikin farinciki Babban Yaya yace “doctor zan’iya ganinta?”

“why not, bismillah”

Fadawa yayi cikin Dakin datake, yana zuwa yakama hannunta yariqe, Hawayen farinciki suka zubo daga Idonsa, ahankali ya ajiye baby Waheeda agefenta, sannan ya rungume ta yafashe da Kuka, kukansa ne yatashe ta, tana bude idonta ta ganshi, sumar Kansa ta shafa ahankali tace “Babban Yaya nakusa mutuwa”

Cikin sauri ya kalleta yace “bazaki mutu kibarni ba Waheeda, tare zamu mutu kinji? Sannu, Allah yayi miki Albarka, me kike so a duniyar Nan Waheeda?”

Murmushi tayi tace “kainake so”

“kinga ma samu na, babu wata Bayan ke”

Babyn ta kalla tace “Mena Haifa Babban Yaya?”

Babyn ya miqa mata yace “ga yarki Nan, itace babbar yarki, sunanta Waheeda Didat”

Cikin mamaki tace “Waheeda Kuma?”

“yes, Matar Didat ta haihu, yayi miki takwara, itace wannan, yaranmu suna wajan su Ummah, kin Haifa min mace da namiji masu kama dake”

Rungume yarinyar tayi tace “Allah yaraya mana su gaba daya”

Anty da Ummah dasuka shigo Dakin yanzu, suka hada baki sukace “Amin ya Allah”

Cikin sauri Babban Yaya ya saketa, suka ajiye mata yaran a gabanta

Kunya taji, taqi Kallan yaran, Yara har biyu duk Nata ne wai

A lokacin Hajiya Anty takira Daddy da Uncle tasanar dasu, dakuma mama Haajara matar baba Habu, yanbiyu ne suketa Kiran wayar Babban Yaya, dauka yayi tareda sallama Ihsan tace “Babban Yaya Ana shirin tafiya da amarya fa saboda unguwar da Nisa, Kuma Maya taqi shirya wa tace Sai Waheeda tazo”

Murmushi yayi yace “bata wayar”

Wayar ta miqawa Maya, Babban Yaya yace “Maya qawar Taki ce naquda tatashi, gatanan kun samu yanbiyu”

Cikin murna Maya tasaka ihu tana fadin “Dan Allah bata wayar Babban Yaya”

Waheeda yabawa wayar, ahankali tayi magana tace “Maya”
Wani irin hawaye yazubo daga idonta

Itama anata bangaren kuka tasa tace “sannu Waheeda, Allah yayi babu ke za’a kaini, Allah yaraya mana su, insha Allah zanzo”

Hawayen ta share takasa magana, Hajiya Anty ta qwace wayar tace “Maya yakuke kuka ne keda qawar Taki, ai murna yakamata kuyi tunda Allah ya sauketa lafiya, kiyi hakuri muma anjima zamu shigo insha Allah”

Hajiyan Didat ce tashigo Dakin tareda Didat, Waheeda ta Kalle shi tace “Didat nagode, Allah yabar zumunci, ubangiji Allah yaraya Waheeda….”

Yace “Amin” sannan suka dauki Babyn suka fita, Sai dare aka sallami Waheeda da sharadin Hajiya Anty zataci gaba da Kula da’ita agida

Yanbiyu basu dawo gida ba saida suka Kai Maya, Sai wajan karfe goma driver yakawo su gida, aikuwa aguje suka shigo falon, a Dakin Ummah Waheeda take, Dan haka Nan suka hadu suka kwana gaba dayansu.

Waheeda taga soyaiya tsantsa daga family dinta, a kwana shidan da tayi kafin suna ko kadan bata daukan yaran saide in nono zata basu, yanda yanbiyu suke dawainiya dasu saika rantse sune suka haifesu

Ranar suna Yara sukaci sunan Ummah da Uncle Usman, Babban Yaya yahada mata kayan fitar suna a kwatuna biyar tareda dalleliyar mota qirar Benz, Sai kuma na baby’s kowa a kwatuna uku uku manya, tareda kyautar filaye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button