BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BABBAN YAYA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummah ta girgiza kanta cikin ranta tace gaskiyar sane daya ce bazata sauya ba

Motar dasuka shiga glass din motar tint ne, ba zakaga naciki ba, mafi yawan lokaci irinta yake Hawa saboda shi mutum ne na mutane, ko Yaya yafuto awaje dole ne kasamu Wanda yasan shi
Suna cikin tafiya ya kalleta yace “Bani labari”

Kallan sa tayi tace “Babban Yaya wanne labari gashinan muna shirin zuwa Naga Anty”

“wacece Anty?”

“Babban Yaya wadda zamuje wajan ta, budurwarka, harna matsu naganta wallahi”

Haushi ne yakama shi, yace “to naji Dan Allah, ni labari nace kibani bawani shirme ba”

Kallan sa tayi, cikin ranta tace zancen budurwar tasa yake cewa shirme to in hakane komai ma ta fada bazai birgeshi ba, duk da haka saita Juyo tana fuskantar sa tace “Babban Yaya inaso Naga kana Ball, ka’iya ball sosai, wani lokacin idan ka saka qwallo araga Sai inji jikina yana tsuma kamar nice nasaka”

Dariya tabashi, saida yayi dariyar sa sannan yace “ke meyasa bazaki Koya ba?”

“Bayan wacce kake Koya mana agida?”

“yes, idan kinaso saina sake Koya muku”

“muna so wallahi Babban Yaya,nafiso nafi yanbiyu iya Ball”

Kallan ta yayi kawai yayi shiru, saboda qarasowa dasukai gidan yarinyar da Hajiya Anty tabashi address, a kofar gida suka tsaya yakira Hajiya Anty ya tambayeta sunan yarinyar tace masa naja’atu, daga Nan yakashe wayar yatura wani yaro Akira masa ita

Yaron ya dawo yace ance su shigo, har falo suka shiga suka zauna, babu laifi gidan sunada rufin asiri, kusan minti biyar da zamansu Sai gata tafuto tana Sanye cikin atamfa Riga da siket, Sai wani Dan qaramin mayafi data saka, da farko tsorata tayi data ganshi, saboda lokaci daya yadaki zuciyarta, gayen yahadu dayawa, fatanta daya Allah yasa Shima ta masa
Zama tayi tareda gaidashi, ya amsa cikin kulawa, acan Qasan ransa yaji dadi dabata ganeshi ba da alama bata ganin ball, Waheeda ce itama ta gaidata fuskar ta d’aukeda murmushi, ta amsa mata

Shiru Waheeda tayi tana jira taji irin kalaman soyayyar da Babban Yaya zai tsara mata kamar yanda Didat yake mata idan sun hadu a school, saitaji yace “Naja’atu Anty nace taturo ni wajanki, basai nayi Miki dogon bayani ba nasan kinsan dalilin zuwana wajanki”

Murmushi tayi tace “Hakane, nide daga wajena babu wata matsala, Ina fatan kaima haka?”

Babban Yaya yace “a a, banda wata matsala Nima, saide inaso namiki tambaya guda daya”

Kafadunta ta daga🤷🏻‍♀️tace “babu damuwa Ina jinka fadi duk maganar dakake so”

Yace “Kina school ne yanzu?”

Tace “a a, tunda nayi candy bankoma makaranta ba”

Yace “masha Allah, Nima banda burin yarinya tayi dogon karatu batare da aure ba, but meyasa ke kinyi candy Amma bakiyi aure ba har kika dade agida kina neman tsufa?

Waheeda ta zaro ido 😳ta Kalle shi da sauri

Itama naja’atu ta Kalle shi tace”me?, nice na tsufa babu aure? “

Batareda damuwa ba yace”idan bakiyi shekara ar’ba’in ba tokin kusa, tunda Naga idanunki na tabbatar kedin Nan sa’ata ce, bazan girmeki ba, nikuma gaskiya nafison na auri yarinya qarama, wadda zan Koya mata komai”

Haushi yakama naja’atu, ta jinjina kanta tace “ni Dama nasan babu wani namijin Arziqi daza’a dinga neman Kai dashi haka kawai, na tabbatar kaima kyan Dan maciji ne dakai tunda har ake neman Kai dakai duk wannan kyan Naka, tunda kana tareda P.A dinka ai shikkenan saikaje ka aure ta”taqarasa maganar tana Kallan Waheeda

Cikin sauri Waheeda tace “kaiiii Yaya nane fa”

Naja’atu ta miqe tsaye tace “Au…to Allah yasa gware kukai kuka futo” 😂
Waheeda ta kalli Babban Yaya ko zai dakatar da naja’atu daga tafiyar datake shirin yi, taji yayi shiru, ahankali tace “Haba Babban Yaya”

Kallan ta yayi ya daga murya yace “Naja’atu”

Cikin fishi naja’atu tajuyo tace “kutashi kubar mana gida tun kafin nakira Yara su tule ku da qasa”😂

Dafe Kansa yayi 🤦🏻‍♂ï¸?, sannan yadago yace “Dama wannan ledar ce kika manta bakidauka ba, Inji Anty tace akawo miki”

Tsaki naja tasaki tace “kuje da tsiyarku” daga Nan tashige tabar su afalo, ita kanta Waheeda taji babu dadi, tayi tunanin haquri zai bata Wai ashe leda zai bata, wannan rashin mutuncin ko ita akayiwa Allah ne kadai zai rabata da saurayin ranar 😖

Haka suka futo daga gidan Waheeda jiki a sanyaye, shi kuwa ransa fes

Amota kasa magana Waheeda tayi, Shima bece da’ita uffan ba, cikin ranta tana so ta tambayeshi meyasa yake gudun aure? Amma tarasa ta’ina zata fara? Duk cikin iyayensu babu Wanda yataba zama dashi yaji menene dalilin sa naqin matan da’ake hadashi dasu, kawai sude iyayen burisu suga yayi aure kawai, tana so taji menene matsalar sa, meyake so? Amma tana tsoron abinda zai biyo baya, saboda zai iya cewa ta raina shi

Tunanin tane ya tsaya lokacin dataga sun tsaya awani super market, p-cap dinsa ya dauka yasaka me d’aukeda sunansa ajiki, sannan yashiga wajan, itade Waheeda tana binsa Abaya taga Sai provision yake yi, itama yace tayaya shi haka suka dauki , su suger, cornflakes, madara, Maggi, kayan zaqi dangin su biscuit da chocolate, saida yagama hada komai tsaf, har tana mamakin Ina zaikai wannan uban kayan,? Wasu yanmata ne suka ganshi su kazo sunaso yayi photo dasu, babu musu ya tsaya sukayi sannan suka nufi wajan biyan kudin, a lokacin wani saurayi Shima yana wajan zai biya nasa kudin, ganin Babban Yaya yasa farinciki yarufe shi, Yama Rasa inda zai Dora ransa, Sai magana yake masa, Babban yaya yayi murmushi Shima yasake da saurayin kamar ya sanshi, shida Kansa ya biya kudin saurayin danasu kayan sannan yamasa sallama suka tafi gida

Suna zuwa gida taga yabawa Sa’eed wannan kayan dasuka zo dashi, sannan suka wuce Dakin Ummah, tare suka gansu itada hajiya Anty Sai hira suke da shewa kamar ba facaloli ba😃
a lokacin biyar da rabi har tayi, Ummah ta kallesu cikin farinciki tace “harkun dawo? Jinake ai sai dare”

Hajiya Anty tace “yayansu nasan de Najaatu tayi hundred percent”

Zama sukai gaba dayansu babu Wanda yayi magana, Ummah ta kalli ledar kayan kwalliyar dasuka tafi dashi tace “yanaga kunyi shiru, meyafaru ko bakuje bane?”

Waheeda ta janye hannunta daga tagumin da tayi tace “hmm Ummah cewa tayi mutashi mutafi tun kafin tasa atule mu da qasa, gashi mayafi take sakawa, shikuma Babban Yaya baya son mayafi, shine ya tambayeta meyasa ta tsufa batayi aure ba, ranta ya6aci tace masa yaje ya aureni tunda ni p.a dinsa ce, Wai ai Dama neman Kai kuke dash…. “
Hajiya Anty ce ta katse Waheeda cikin tsawa” ke dallah can rufe mana baki shashasha kawai. Yen yen yen Sai magana kike Babban Yaya baya son kaza, Babban Yaya baya son kaza, kunhada Kai kunje kunci mata mutunci kun dawo toshknn Hankalinku saiya kwanta, ita yar’iskace dabaza tace yaje ya aureki ba? Ina aka taba tafiya zance , ganin farko adiba atafi da qanwa? Saikune zaku nuna mata ku yan’uwan jini ne, banji dadi ba dabatasa anmuku wanka da qasa ba, tashi kibawa mutane waje manya suna magana kin tsomo baki kamar maganar aurenki ake “
Sum sum Waheeda tatashi tabar Dakin, shi kuwa Babban Yaya kasa hada ido yayi dasu

Ummah tace”ashe abinda kake fadawa yaran mutane kenan shiyasa kowacce Sai tace bata sonka, Toda kake cewa ta tsufa batayi aure ba kaidin shekarar ka nawa?” 🤔

Shiru yayi yakasa Bawa Ummah amsa, Ummah tace” dakai nake, nace Kai shekararka nawa bakayi aure ba? “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button