BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

 *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
       _(Miya kawo kishi?)_     *_Bilyn Abdull ce????????_*

02

………Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam. Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya. Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar gwagwarmayar rayuwa a cikinsu.
      Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a hanun yayanta acan. Kowa ya nuna ƙin matar tasa itako ta nuna soyayyarta gareta dan bataga aibunta ba tunda musulma ce. Daɗin abinda tayi yasa Yayan nata da matarsa shiga suka fita wajen ɗauke mata Usman dake gab da kammala secondary school. Ita kuma ya saya mata gida tabar cikin su Gwaggo.
     Wannan abu ya musu matuƙar ciwo, dan ƙiri-ƙiri suka nuna ƙiyayyarsu da kishinsu akan hakan, tare da dagewa wajen cusa tsanar Usman da Maryam a zuciyar sauran ƴaƴansu, ita dai tai musu sallama harda kukan sabon zama ta ɗauka diyarta Maryam da Usman ke kira Mimi suka koma sabon gidansu.

     Rayuwa ta shuɗa, komai ya canja yara duk sun girma. Tafiya da Usman yasa Gwaggo da Mama jajircewa wajen ganin su Muhammad sunyi karatu mai zurfi dan kar Usman yafi ƴaƴansu. Sai dai shi UBANGIJI ba’ai masa dole, dan kuwa shike bama wanda yaso a kuma lokacin da yaso. Sun sami nasara sosai ta rayuwa saboda zukatansu cike suke da son ganin ɗan uwansu bai zartasu ba kamar yanda iyayensu kullum ke kwaɗaita musu, dan zuwa yanzu da gaske ƙiyayyar Usaman da nuna masa ƴan ubanci tai tasiri a zukatansu saboda huɗubar mahaifiyarsu da abokiyar zamanta. Sun buge gidansu na gado kasancewar babba ne sosai tare da siyen na maƙwafta dake son tashi suka ware ma Usman da Maryam nasu gefe su suka gina nasu a tare su huɗu tare da kason ƴar uwarsu Halima da tuni tayi aure, koda Usman yazo Nigeria yaga ɗan abinda aka rage musu baice komaiba, saima ƙoƙarin ganin ya samu kusanci da shaƙuwa da ƴan uwansa yake kamar da. Hakan bata samu ba, dan babu abinda suke masa sai ɗagawa da fariyyar sunada kuɗi yanzu, koda aka kaisa turai bai fisu da komai ba. Murmushi kawai yayi, dan al-amarin nasu yanzu dariya kawai yake bashi. Watansa kusan uku a Nigeria ya tattara mahaifiyarsa da ƙanwarsa Mimi suka wuce Malaysia, wannan ma ya sake ɗaga hankalin su Gwaggo, suka cigaba da tunzura su Muhammad.
     Tsahon shekara huɗu bai sake waiwayarsu ba sai da aurensa da ɗiyar kawunsa tilo da suka haifa ya tashi, dan kawun nasa da matarsa mai suna Asiya haihuwarsu ɗaya mace Aysha Humaira, shaƙuwar dake tsakanin Usman da Humaira ta ɓaci dan kusan shine yay rainonta, Hakan yasa soyayya mai tsanani shiga tsakaninsu. A Nigeria sukazo akai bikin duk da ƴan uwansa nata masa wulaƙanci, shidai baibi takansu ba sai fatan shiriya yake musu.
      Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ƙasar saudia sunje aikin hajji, mutuwar tasu ta samu asaline dalilin accident daya wanzu a cikin harami a wannan shekarar. Sun shiga tashin hankali sosai, wanda har yay sanadin kawunsa ya samu ciwo shima yabar duniya. Girma ya dawo hanun Usman, dan kuwa ragamar rayuwar ƙannensa biyu ta dawo garesa, wato dai Humaira data zama matarsa da Mimi. A wannan gaɓar ƴan uwansa sun kirashi sun masa gaisuwa, yaji daɗi har cikin ransa.
       Bayan ya aurar da Mimi ga wani abokinsa dake anan Malaysia shima dai ɗan Nigeria ne babu jimawa ALLAH yayma Hajara (Mama) mahaifiyar su Muhammad ƴan uwansa rasuwa itama. Har Nigeria yazo tare da matarsa da ƙanwarsa Mimi dake fama da ƙaramin ciki, hakan da yayi sai ya sanyaya jikin ƴan uwan nasa dan kuwa su ko auran Mimi duk da ya basu hakkinsu ƙin zuwa sukai, hakama rasuwar mahaifiyarsa da kawunsa da uwar matarsa a waya kawai sukai masa ta’aziyya. Ya nuna musu hakan ba komai bane su manta kawai.
        Ɗan shirin da suka samu a tsakaninsu a wannan karon ya samu damar sanin duk iyalansu, dan kuwa a baya basu taɓa yarda yasan fuskokin matansu ba ma balle adadin ƴaƴansu ba. Muhammad matansa biyu. uwargidansa Wasila ɗiyar ƙanwar gwaggo nada yara huɗu a lokacin, babban shine Al-Mustapha da yaci sunan MD Shareff mahaifinsu suna kiransa da Shareff. Sai Maheer, Binta, Ishaq da ƙaramin ciki da take kan laulayinsa. Wasila da yara ke kira Mommy a gidan ba wani sanin Usman taiba amma ta mugun tsanarsa saboda huɗubar Gwaggo, ƙinsa take tamkar itace ƴan uban nasa ba mijinta ba. a gefe tana matuƙar jin kishin yana rayuwa a ƙasar waje a ganinta kodai yaya ya fisu nasibin rayuwa. Ta shiga matuƙar takaicin ganin su Muhammad sun fara sakkowa akan ƙin ɗan uwansu da sukeyi, dan haka ta shirya sake haddasa sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu kamar yanda Gwaggo ke ɗaurata akan hanya. Sai amaryarsa Ubaida da suke kira (Aunty Amarya) nada ciki tsoho itama haihuwa yau ko gobe, mace ce mai son jama’a da haƙuri, duk da ƙiyayyar iyayen miji da take fuskanta da iskancin kishiya ta zama mai haƙuri da kawaici a gidan. Sai matar Abubakar Mariya da suke kira Mom. Itama mace ce mai dattako da mutunci. Ba wani daɗin iyayen mijin nata takejiba saboda Gwaggo itace ke juya Mama, bata son kowa yay farin ciki a gidan sai ɗiyar ƴar uwarta. Amma haka taita kawaici da shanye haɗata fitinar da aka dingayi da uwar mijin tasu har ALLAH ya rabasu lafiya da ita. Itama dai yaranta biyu duk maza. sai dai tana da ciki ɗan watanni biyar. Umar dai yaƙi aure, hasalima ya zama fanɗararre a cikinsu sai addu’a. Tuni yana kudancin ƙasar sai ya gadama yake waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ƴan uwan ba’a komai suke sakashi a lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce. Kamar yanda ƴan uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa matar a garesu. Ƙyaƙyƙyawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga tarbiyya da mutunta mutane.
     Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba’a faɗaba Humairah ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ƙiyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matuƙa, sai dai koda wasa taƙi bada fuskar da Mommy ɗin zata kawo mata raini.
     Rasuwar Mama yasaka baƙin halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu zaman lafiya tsakaninsu da ƴan uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune ƴan ɗakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba ɗaya ya tashi a taɓare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ƴaƴan anguwa yake da musu ƙwacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.
      Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara gurbi bayan Umar a zuri’arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ƴaƴansu lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ƙanensa. Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka zauna shawarar matakin da zasu ɗauka akan yaronsu duk da gida ɗaya suke da Gwaggon sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ƙyautu ya mallaki muhalli a ƙasar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daɗi, dan basu ɓoye masa komai game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo. Ya jimanta al’amarin tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai ɗauke Shareff ɗin ya koma hanunsa insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ƙara ɗinkewa kamar komai bai faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ƙara masa dana cikin gidansu kasancewar gidan nasu ƙatone sosai kowace mace ma da part ɗinta, ga kuma na Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar ɗin sukace ya ɗauka yaƙi.
     Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ƴan uwansu. Basubi takanta ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar Shareff hanun Usman ta sake tasowa. Nanma dai ansha ƙaramin yaƙi dan Mommy haukane kawai bataiba ɗanta zai koma hanun maƙiyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba. Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama Shareff tafiya ba.
         A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama dai yaranta uku ne a yanzu tana auren ɗan wan gwaggon dan ita ta haɗa….

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page