BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

       Maimakon ya nufi gida sai kawai ya zarce wajen aikin da companynsu keyi. A can ya samu Khaleel. Ya danne dukkan damuwarsa da haɗiyesa yana mai kallon ƙanin nasa jarumi da halinsu ke kamanceceniya tamkar uwa ɗaya ta haifesu. Murmushi yay da miƙama Khaleel ɗin dake gaishesa hannu alamar yafi son suyi musabaha. Hannu Khaleel ya bashi suka gaisa, ya mika masa irin hular dake a kan duk wanda ke’a wajen. Babu musu ya amsa ya saka, daga haka suka fara zagaya ginin da ayanzu ya fara bayyana kansa gamai kallo. Tabbas aka kammala estate ɗin ba ƙaramin ƙyau da ɗaukar hankali zaiyi ba. Duk inda suka gitta ma’aikata gaishesa suke da girmamawa shiko yana amsa musu da kulawa. Inda yaga gyara yay magana, inda ya kamata ya yaba ya yaba musu. Hakan sai ya ɗauke kaso mafi yawa na damuwar da yake a ciki har lokacin sallar azhar yayi suka nufi massallaci. Koda aka idar da salla wani gidan cin abinci suka nufa anan kusa da ƙafa. A lokacinne kiran Fadwa ya shigo wayarsa. Ɗagawa yay yakai kunne sai dai baiyi magana ba.
    Muryarta a raunane cikin kuma ɗari-ɗari tai masa sallama. Amsa mata yay kadaran kadahan, sai duk ta daburce, amma cikin dauriya da in ina tace, “Am sorry dan ALLAH. Wlhy babu ruwana sai da nace karsu je. Ganin bazasuji maganata ba yasa na bisu da tunanin ko kana can.”
      “Is ok”.
Ya faɗa a taƙaice. Ita tasan is not ok a cikin muryarsa. Amma sanin baya son nacin magana saita saki waccan ɗin kamar yanda ya buƙata. “To ga abinci na kammala amma naga baka dawo gida ba har yanzun”.
    “Karki damu gashi zanci a inda nake”.
   Zatai magana ya dakatar da ita da faɗin, “Zanci na dare idan na dawo bye” Ya yanke batare da ya jira amsarta ba. Kiran nata ya ɗan sakama masa jin sassauci, dan garama ita, Anaam ko zai cika duniya da fushi ai bata taɓa nuna masa ta damuba a kwanakin datai gidan nasa duk da yasan sarai tana sane da komai na halin da yake a ciki dangane da aurenta. Yaja siririn tsaki a ƙasan zuciyarsa yana ayyana (Zanyi maganinki vary soon).
      Khaleel da tun shigowarsu yana wajen siya musu abinci ya dawo tare da waiter dake biye da shi. kujera yaja ya zauna. “Am sorry babban Yaya na daɗe”.
     “Don’t worry”.
Ya faɗa a taƙaice hankalinsa akan wayarsa. Sai da suka fara cin abincin a nutse Khaleel ya ƙara maida hankalinsa garesa. “Yaya nikam kuna waya da Yaya Maheer?”. Idanu ya ɗago ya zubama Khaleel ɗin, kafin kuma ya girgiza kansa alamar a’a. Khaleel yaja numfashi ya fesar. Ruwa ya ɗauka ya ɗan sha ya ajiye. “Naje gidansa jiya da yamma. Saboda su Abbah suna maganar ya daina zuwa gida gaba ɗaya sannan wayoyinsa duk a rufe. Yaya banji daɗin yanda na samesa ba shida matarsa. Gaba ɗaya Yaya Maheer ya canja tamkar bashi ba. Sam babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninsa da matarsa abin ya tsoratani wlhy”.
      Kasa magana yay ya kuma kasa cigaba da cin abinci har Khaleel yakai aya, sai dai idanunsa gaba ɗaya launinsu ya sake canjawa. “Mike faruwa?”.
     “Yaya komai ma na faruwa, a yanzu haka so take tabar gidan amma mahaifiyarta ta tabbatar mata zata tsine mata inhar ta bari Yaya Maheer ya saketa. Shi kuma yaƙi bata kowacce irin dama wlhy bakaga yanda yake treating nata ba like dai wadda suke rayuwa a…. Mtsoww oh my god babu dai daɗin faɗa kawai. Na fara masa nasiha amma yaƙi saurarena, daga ƙarshe ma a gabana ya mareta wai tana haɗashi da ƴan uwansa, so abin is to much wlhy”.
      Numfashi ya sauke zazzafa ransa duk a jagule. Still dai ya kasa cewa komai kallon Khaleel ɗin kawai yakeyi. A ƙasan zuciyarsa kam yana jin rauni matuƙa. Ya rasa miyyasa Mommy ta kasa fahimtar rayuwa irin ta yanzu ta aure tasha banban data zamanin baya, a da daga maza har mata kowa nada kawaicin iya karɓar aure a duk yanda yazo masa. Amma a yanzu ba haka baneba, auren soyayyar ma yaya aka ƙare balle na tilastawa. Shi kansa dabai jureba za’a samu irin wannan matsalar ne a lokacin data tilastashi auren Fadwa. Amma daya jure yayta gayama ALLAH da tilastama kansa tanada mahimmancin amsar ko minene daga umarninta sai gashi ALLAH ya saka masa son Fadwa ɗin. Sai dai Mommy ta kasa fahimtar shida Maheer za’a iya samun banbancin juriya akan wannan al’amarin. A ganinsa data barshi ya aura wadda yake so da an samu maslaha. Dan gashi abinda takema gudun bai tsallaketa ba tunda ga Anaam dai matsayin matar gudan jinin nata bisa ƙaddarar UBANGIJI da babu wani hannu daya isa gogewata….
     Numfashi ya sauke a hankali saboda taɓasan da Khaleel yayi. Abincin suka cigaba da ci batare da wani ya sake magana ba, sai dai Shareff tsakura kawai yakeyi. Baimaci na kirki ba ya ture gefe. Haka Khaleel ya biya kuɗin suka sake komawa wajen masu aikin. Har yamma yana a wajen, bai tafi ba sai da masu aikin suka tashi. Sai da ya sai kayan fruits ya bama Khaleel ya kai musu can gida shi kuma ya zuba na nasa gidan a mota shima ya wuce. Ana kiraye-kirayen sallar magrib ya shigo, dan haka bai nema kowaba a cikinsu ya wuce sashensa. Ruwa ya fara watsawa jikinsa na ɗumi a gaggauce, ya fito ya saka kaya nanma a gaggauce ya fice massallaci dan har an fara sallama……….✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

54

………Ƙara riƙo hanun yay da ƙyau idanunsa masu kaifi na saukar mata da kasalar data mantar da ita wanzuwar su aunty Sakina a falon. Dama haka yake buƙata, ta manta da wanzuwar tasu ya samu damar isar da gargaɗinsa garesu batare daya samu wani tangarda daga gareta ba.
     “Dama haka ake bama miji abu?”.
  Ya faɗi maganar a salon daya nema ɗauke numfashin Anaam na wucin gadi, dan muryar da yay mata magana da ita muryace da zata iya rantsuwa bata taɓa ji daga garesa ba. Da ƙyar ta iya ƙwato kanta, tai ƙoƙarin ajiye masa kayan a hanun kujerar da janye nata idanun daya sargafe a nasa dan ta gama yanke shawarar barin wajen kafin a samu matsala yaga rauninta. Tana daga kafa ya riƙo hanunta tare da jawota sai gata ɗaram a cinyarsa tamkar walƙiya. Kafin tunanin wani abu ya risketa har ya yimata zobe da hanunsa ta hanyar ɗorawa a saman cikinta ya manne bayanta da ƙirjinsa kansa bisa wuyanta yana shinshina da fara magana cikin kunenta da wani salon daya saka tsigar jikinta tashi.. “A haka ake bama miji abu ba’a tsaye ba”.
      Saukar wata mulmulalliyar ashariya cikin kunnuwansu ta tilastata ƙanƙamesa babu shiri dan da gaske ta tsorata dama gata a tsakkiyar wani firgicin. Harga ALLAH ta manta da su a falon, saɓanin shi da duk abinda yakeyi domin su ɗinne dama. A firgice ta ɗaga ido zata kallesu ya hana hakan, dan kuwa hanunsa ya tura cikin rigarta sai dai akan cikinta ya tsaya.. Ɗan matsawar da yay ta sata saki ƙarar ruɗewa dan a bazata abin yazo mata kuma taji zafi……
      Rige-rigen fita aka farayi tsakanin Hajiya Luba da Aunty Sakina, saboda ƙarar Anaam ɗin fassara daban suka bata. Aunty Sakina ma harda gwara kai a jikin garu lokacin da suke turereniyar ficewa.
          Hanunsa da taketa faman kaima mintsini ya janye, ta mike zumbur daga cinyar tasa idanunta taf kunya. Riƙota ya sake yi fuskarsa ɗauke da murmushin ƙeta. “Malama nace na gama n….”
    Hararar data wulla masa ce ta hanashi ƙarasa faɗa ya saki dariyar data ƙara ƙular da ita tana jin zafinsa har cikin maƙoshinta. Sake fisgota yay ta dawo saman cinyar tasa. Ya haɗe hannayenta duk biyu dake son turesa ya danne akan cikinta. “Idan idanunki suka cigaba da harararta daga yau sai na miki haɗiyar ɗan sululu a gidan nan fitsararriya”. Mutsu-mutsunta ta cigaba dayi na son ƙwacewa yaƙi bata dama. Saima lanƙwansota yay ta kwano jikinsa ya kai goshinsa kan nata ya haɗe. Yawu ta fara kokawar haɗiyewa da sauri-sauri ganin yana daidaita lips ɗinsu.
     “Please Yaya dan ALLAH kar kayi bana so”.
    Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya, “Fitinanniyar yarinya minace zanyi to?”.
  Bakinta da take faman karewa da hannu tatura gaba da ƙoƙarin kauda fuskarta ya tare da hannunsa, tare da janye nata hanun ya manne lips ɗinsu. So take ta turesa, amma tasirin abinda yake matan a cikin jini yana barazanar hanata kowanne irin yunƙuri, daɗin daɗawa ya riƙe hanunta ta yanda bazata iya ko motsashi ba. A karon farko ta fara maida masa murtani a yau dan tasirin salon nasa jinin jikinta ya fara amsarsa da ƙarfin gwiwa da wani sirrin ɓoye dake can ƙasan zuciyarta da ita kanta har yanzu bata san da zamansa ba tattare da ita. Hakan tamkar ƙara zugane a garesa da dukkan haƙurinsa, dan kai tsaye zuciyarsa ta fara ingizasa ga kaiwa inda bai gama shirya kai kansa ba. Ring na wayarsa ne ya dawo dasu duniyar da suka jima da yin nisan barin cikinta da lissafi irin na masu hankali. Sakinta yay, zaram ta miƙe kamar wadda take a tsinin allura. Da sassarfa ta bar falon ko waiwayensa taƙi tayi. Da kallo ya bita yana sakin kakkauran numfashi da murmushi, a hankali yakai bayansa jikin makarin kujera ya kwantar yana mai lumshe idanunsa da sake sakin ajiyar zuciya a jajjere yana kai hanunsa ya shapo lips  ɗinsa….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button