BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

   Wani irin harziƙowa Hajiya Luba tayi, amma sai Baba Ibrahim ya dakata mata wata irin razananniyar tsawa. Komawa tai ta zauna daɓar. Anaam tai murmushi mai ciwo da dafe karfen benen takai zaune saboda jiri da take gani. Sai da ta ɗan dafe kanta na wasu sakkani sannan ta ɗago tana ɗan murmushi. “Kuyi haƙuri.” Batare data jira cewar wani ba ta cigaba da faɗin, “Ban faɗa muku wannan maganarba sai dana riƙe hujja, kuma dama irin wannan ranar nake jira dan nasa duk yanda Maman Bibah da Bibah zasuyi da Gwaggo sai sunyi domin Yaya MM ya auri Bibah, kuma Fadwa itace kawai makaminsu da Mommy”. Ta ƙara maganar da miƙa wayarta dan bazata iya tasowa ba saboda jiri. “Gashi komai na’a cikin nan. Ku kira Amrah ma kuji dan tasan abubuwa da yawa itama”.

   Aunty Bintu ce ta amso wayar, ta kaima Baba Ibrahim. Gwaggo ta miƙe a fusace sai dai jikinta rawa yake. Amma sai Gwaggo Halima tasa ƙafa ta taɗota ta koma zaune daɓar har tana sakin ƙarar azaba data ratsa ɗuwawunta. Sosai da mamaki mai cike da ɗunbin razani suka bayyana a fuskokinsu Baba Ibrahim. Dan kuwa dai ga muryar Gwaggo gata Hajiya Luba da Bibah. Su Mommy zasu fara hayaniya Baba Ibrahim ya hanasu, cikin matuƙar razanarwa Baba Ibrahim yace Hajiya Luba ta faɗa kokuma ya ɗauka mataki a kanta. Jikinta tsuma yakeyi, musamman da taga irin mugun kallon da Shareff ke jifanta da dashi, wanda ba ita kaɗai ba, hatta Gwaggo haɗiyar yawu take da ƙyar…

    “Wlhy Yaya mu ba laifinmu bane, kawai dai Bibah ce ke tsananin son Shareff, nayi-nayi Nafi ta fahimci abinda nake buƙata na mu haɗa aurensu taƙi, sai nunawa takeyi da Fadwa za’a haɗa. Har nayi zuciya da hakan sai dai Bibah ta shiga damuwa, shine nazoma Gwaggo da batun ko akwai yanda za’ayi, amma saita nunamin itama bata san zancenba. Ban gajiba muka cigaba da binta har akai auren Fadwa da Shareff, sai lokacinne ta fara saurarena, ta kuma tabbatar min idan har muka taimaka mata cikin Fadwa ya zube zatai duk yanda zatai dan auren Shareff da Bibah ya yuwu”.

   Salati falon ya ɗauka baki ɗaya, yayinda a lokaci guda Gwaggo Halima da Mommy suka kaima Gwaggo shaƙa, da ƙyar aka ɓanɓareta a hanunsu idanunta har sun firfito waje kamar na tsohon kwarto. Nan fa sabuwar hayaniya ta kaure har wani baijin zancen wani, dan Fadwa kam tuni ta turmushe Bibah tana jibga, itama uwarta Hajiya Luba ta turmushe Fadwan. Ƙurace sosai ta tashi a falon, wadda ta saka Anaam ji kamar duniyar na juya mata. Cikin sa’a Shareff ya hangota tana jujjuya kanta. Da sauri ya miƙe yay inda take, cak ya dauketa ya koma saman da ita tana faman jujjuya masa kanta, Mamie da itama ta hangosu tai saurin bin bayansa dan ita kam ma ba komai take fahimtaba a abinda ke faruwa a falon.

   Faɗa sosai ya kaure, duk yanda su Abba sukaso kwantar da abun ya gagara, dan tun anayi a falo har aka koma tsakar gida, kafin kice mi ƴan biki sun fara tururuwar shigowa bama idonsu abinci tunda dama akwai ƙofar dake a tsakanin gidajen wadda basai kaje gate ba. Cirko-cirko mutane sukai sunajin fallasa da tonon asirin da su Mommy sukema juna, yayinda Gwaggo ke neman naɗe tabarmar kunya da hauka. Sai dai fa ganin lamarin yafi ƙarfinta dan hatta Mommy yau la’antarta take ga ƴan biki sai ta nema fita a gidan tana kuka wai su Daddy sun shirya wulaƙantata. Nanfa wasu a munafukai masu son jin ba’asi suka take mata baya, sai dai taƙi sauraren kowa, tana gab da barin layin nasu wani mai mota ya shawo kwana, duk da horn da yakeyi sam Gwaggo daketa faman sambatu da surutai batajisa ba, shi kuma ALLAH ya hanashi damar taka birki, ya kwasheta sama ya direma kasa, yana son riƙe kan motar ina saida taya ɗaya ta dirza ƙafar Gwaggo har ana iya jin karar farfashewar ƙashi. Tun ƙarar azaba ta farko data saki bata sake fahimtar ina take ba ta suma. Dan danan aka rufu kanta, har su Daddy labari yazo musu sun fito, nan fa layin ya cika dankam. Matasa zasu rufu kan mai mota da ƴan biki yazo dauka baba Ibrahim ya dakatar da su. Kamalarsa da dattakon kasancewarsa tsohon arziƙi ya sakasu bin umarni, sai dai an kama Gwaggo da babu alamar numfashi a jikinta an saka a motar mutumin aka nufi asibiti.

    Babu ko tausayi a fuskar Gwaggo Halima, sai ma faffaɗar magana take wai ai ƙarshen Gwaggo kenan. ALLAH ma ya kara sakata a masifa fiye da hakan. Mafi yawan mutane maganganun Gwaggo haliman basu ɓata ransu ba, sai dai duk da mugun halinta baban Fadwa ya kasa haƙuri shima a wajen ya yanke igiyar auren Gwaggo halima biyu. Ai sai lokacin Fadwa da Mommy suka sake tunawa da mutuwar nasu auren fa suma. Nan guri ya kara daukar zafi faɗa ya dawo sabo fil da ƴar koke-koke abin zakkunya da takaici………..✍
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

79

……….Yanda Fadwa ke jigatuwa a gidansu haka Mommy ke jigatuwa a gidan Baba Ibrahim, dan kuwa matansa babu kanwar lasa a ciki. Basa raga mata koda da wasa. Abinci kuwa iya abinda suka bata shine zataci, bata isa cewa tak ba Baba Ibrahim zai silleta tass. Kaf ƴaƴanta an hanasu raɓarta har su Shareff kuwa. Itama duk ta fige ta ruɗe da damuwa mai tsanani, ga rashin aure, ga rashin ƴaƴa, ga dukiyar ɗan da take taƙama dashi ashe ta maƙiyintace. Kai ina itako zata saka kanta taji sanyi wannan rayuwa haka.

       Gwaggo Halima kam ai zamu iya cewa ta susuce a wannan gaɓar. Dan kuwa maganar auren mijin nata ya risketa dan abune da aketa faman watsasa a gidajen talabijin da rediyoyi. Bikine ake shiryawa na hamshaƙai biyu masu daidaiton ƙwarya tabi ƙwarya. Ga rashin ƴayanta tare da ita, dan kuwa itama dai su Abba sun ƙwace wayoyinta, sun kuma kafa mata sharadin inhar tana buƙatar zama da su sai ta nutsu, inba hakaba zata bar musu gida, dan yanda sukayi haƙuri da ita a baya a yanzu kam bazasuyi ba.

     Kwanan su Sima takwas a police station aka shiga kotu, dan duk magiya da roƙo da iyayensu ke ma Shareff ya rantse sai sunyi shari’a. Kasancewar laifinsu a bayyane yake ba’awani wahalar da shari’a ba a zama biyu kacal aka yanke musu hukuncin zama gidan yari na watanni goma shaɗa. Tare da tara mai tsoka. Kafin kace mi media ta ɗauka, babu abinda ke trending kamar labarinsu. Manyan yaran da akeji dasu a tiktok da istagram dama mafi yawan kafafen yanar ta gizo sunsha ɗauri a dalilin shugabarsu. Ga labarin mutuwar auren Fadwa ya zama kamar wani abin izgili a bakunan wanda suke jin haushinta. Sai dai wasu hakan ya sanyaya musu jiki matuka. Dan inhar haka zata kasance ga Fadwa suma ɗin basu tsiraba kenan tunda duk iri aiki guda sukeyi, wasu ma nasu yafi nata muni matuƙa. A take wasu suka fara goge wasu videos na rashin tarbiyya dake a shafukansu, wanda kuwa ke kai musu ji suke yanzu aka fara wasan ma. (Ya rabbi ka shirya mana zuriya damu baki ɗaya????????????)

Kwanan Anaam goma sha biyar a gidan Shareff ya dauka matarsa suka koma gidansu, dan ta ɗanji daɗin jikinta. Sai dai an sama mata mai aiki tare kuma da Aysha suka koma can dan itama tana cikin kunci da damuwa abin tausayi, dan ma Anaam ɗin na tsaye a kanta wajen ganin ta sakama ranta salama da daukar komai matsayin jarabawa.. Komawarsu gidansu da sati guda su Abie suka koma, dan Abie yayi iya koƙarinsa na ganin komai ya daidaita amma hakan yaci tura, ya zube kuɗi masu tsoka na kula da Gwaggo a asibiti ya tattara iyalansa da su Aunty Mimi suka koma Malaysia, inda suka bar Anaam na faman kuka sai da Shareff yayta lallashi…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button