BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

     Zuwansu ya matuƙar ɗauke mata hankali, da taimakonsu ta gyara ko’ina duk da babu wani datti, zuwa la’asar wasu daga cikin ƴan uwa danginsu Abie ɓangaren mahaifiya sukazo. kayan gara na fulawane da ƴan abubuwan daba’a rasaba suka kawo mata saboda baƙi da zasu ɗan ringa shigowa ganin ɗakin amarya, harda drinks mai ɗan yawa da ruwan roba. Sai lokacin sukaji sautin kiɗan dake tashi a sashen Fadwa ya tsaya, babu wanda yay magana suka cigaba da harkokin gabansu…….✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

44

………..Banza yay mata kamar baiji ba, sai ma ƙoƙarin mikewa yake bayan ya latse remote tv ya mutu. Ganin zai bar wajen tai saurin riƙo hanunsa dan in har ta bari ya wuce bazata iya kai kanta ko nan da ƙofar fita ba saboda da gaske bata gani da ƙyau a cikin duhu sai da taimakon glass ɗin.
    “Yaya Please ka bani”.
Hanun nata ya kalla tare da ƙoƙarin juyowa, da sauri ta janye nata a yanayin jin kunyar aikatawa. Kafeta yay da idanu yana ƙarema fuskarta kallo kai tsaye, yayinda ita kuma ta kasa ɗagowa ta kallesan. A cikin ransa  yake faɗin, (Fitsararriya ashe kinada kunya?). A zahiri kam babu alamar wasa tare da shi yace, “Muje ki kwanta”.
      “Ina ɗin?”.
Ta faɗa cikin waro makantattun idanunta da mai kallo a haka bazai taɓa tunanin rauninsu ba saboda girma da hasken dake cikinsu tamkar wadda ke iya hango abinda ke faruwa a kilomita huɗu na gabanta. Gab da ita ya matso har tana iya jin saukar numfashinsa a fuskarta. Cikin magana tamkar mai raɗa “A inda kike?”.
       Baya taso jan jikinta bugun ƙirjinta na daɗuwa amma sai ya hana hakan ta hanyar tokare hanun kujerar da take jiki da hanunsa. Duk sai ta daburce. Ture hanunsa tai da ƙarfi, tai gaba da nufin guduwa ƙafarsa ta nema taɗeta tai gaba zata faɗi ya riƙota, ɗan fisgota yay ta faɗo jikinsa, baima jira tako maida numfashi ba ya ɗauketa cakk ɗinta yay hanyar bedroom ɗinsa dan ya gaji shima kwanciya yake buƙata. Inko ya biye mata sai dai su raba hali. Watsal-watsal take da son ƙwace jikinta tana faɗin, “Ni wlhy ka saukeni bana so, bana son haka Yaya MM, ALLAH zan cijekaaa!!”. Ta ƙare faɗa da ɗan ƙarfin sautin daya sakashi direta a saman gadonsa da sauri.
      “Kina da hankali kuwa? Fasan kunne zakiyi?”.
   Mikewa tai cikin sauri da nufin barin masa ɗakin dan ita kam dai bazata taɓa yarda ta kwana a ɗakinsa ba, gidan nasa ma domin yin biyayya da iyayenta ne da son cimma burinta cikin sauƙi zaisa ta zauna har zuwa lokacin data ƙayyadewa shirinta. Bai hanata ba dan tuni ya zare keys ɗin ɗakin, sai ma toilet daya nufa cikin halin ko’in kula. Jin ƙofar a kulle ya sata juyowa da sauri duk da ba fes take iya ganin komai ba amma kasancewar da fitila tana gani fiye da acikin duhu. Sosai hankalinta fa ya tashi, dan abu ɗaya zuciyarta ta iya bijiro mata zaisa yay mata hakan, a gareta kuma shine abu na ƙarshe da bazata iya mallaka masa ba koda a yau zaice zai mata dukan da shine kawai abinda take shakka da tsoro tattare da shi. Haɗiye duk wani fargabanta tai tai tsayuwar sojan badakkare a jikin ƙofar tana dakon fitowarsa. Tsahon mintuna 6 sannan ya fito duk tana lissafa ta hanyar kallon agogon dake bangon ɗakin. Yi yay tamkar bai ganta ba ya hau zame jallabiyar jikinsa. Bayyanarsa a zahirinsa da ga shi sai boxer ya sata juya masa baya da sauri tana ambaton sunan ALLAH. Kayan barci ya ɗakko a wadrobe ya saka harda fesa turare kamarma bai ganta ba. Ya haye gadonsa yana faɗin, “Baƙya buƙatar kwanciyar ne?”.
      Maimakon amsa sai ta fashe masa da kukan ƙarya. “Yaya dan ALLAH ka bani key da glass ɗina na wuce barci nake ji, ALLAH haka babu ƙyau, kuma kaina zai iya yin ciwo”.
    “Idan kin so hakan kenan”.
Ya amsata yana jan bargo cikin halin ko’in kula. Kukan ƙaryar tata ta dakatar zuciyarta na mata zafi, sai dai hango keys ɗin a bedside drawer ɗin inda yake ya saka mata jin sauƙi, cigaba tai da tsaiwa a wajen har kusan minti ɗaya kafin ta nufi wajen cikin sanɗa da tunanin yayi shammatarsa ta warto. Tana gab da isa ya fiddo hanunsa dake cikin duvet ya ɗauke, rigarsa ya ɗaga ya ɗaura saman cikinsa ya maida bargon ya rufe. Ganin ta dakata daga yunƙurin tahowar ya ɗan buɗe ido yana kallonta a sigar da ita bata fahimci haka ba musamman saboda matsalar nata ido.
     “Gashi anan ki ɗauka”
  Kanta ta ɗauke idonta na ciko da ƙwalla na gaske a yanzun. Dan tsaf ta fahimci tarko ne ya kafa mata. Hannu tasa ta share hawayenta, sai kuma ta taka da baya-baya ta koma saman kujerar dake a bedroom ɗin ta zauna……….

        ★Tun barowarta sashen nasa ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai faman kaikawo take hawaye masu zafi na kishin mijinta na ragargazar zuciyarta tamka irin kowacce macen da aka kawowa abokiyar zama, ba ita kaɗai ba, irinta da yawa sukan azaftu matuƙa da rashin barci da ƙunci a irin waɗan nan kwanakin bakwai da amarya takan samu matsayin na amarcinta. Kai wasu ma borinsu har yakan zarta natan, ga masu ƙarancin imani ma kwana suke shiryama zukatansu munanan abubuwa harma da masu aikatawa. To ita dai Fadwa saita kasance a jerin masu azaftuwar ƙuntatama kai da ƙiyasta abubuwa da dama da bai dace zuciya ta ƙiyasta ɗin ba ta kasance duk da su Aunty Wasila sun bata tabbacin hakan bamai faruwa bane ta kasa nutsuwa, sai dai babu tunanin mugunta ko shirka a ciki, ita dai kawai mijinta take hangowa da wata a yanayin da ita kaɗai ta sanshi.
     Tsahon lokaci ta ɓata tsaye jikin window tana kuka da dakon kallon hanyar tsumayen fitowar Anam da mijinta, amma sai saɓanin hakan ne ya biyo baya, domin kuwa shi kaɗai taga ya fito zuwa sashen Anam ɗin, bai kuma ɗauki tsahon lokaci ba ya fito ya sake komawa nasa sashen. Neman zubewa tai ƙasa kuka mai cin rai na kufce mata dajin tsananin tsanar su Daddy da take ganin sun ƙulla wannan aurenne saboda basa ƙaunarta ita da mahaifiyarta dalilin asiri da Abie da Mamie da aunty Mimi sukai na raba kansu tamkar yanda a koda yaushe Gwaggo ke faɗa. (karku ga laifin Fadwa, a haka aka raini zuciyarta, a haka ta girma da ƙiyayyar waɗanda bata da wani tabbataccen laifinsu a zahirin rayuwarta, da yawa iyaye na kuskuren wajen ƙoƙarin fidda matsalarsu da ƴan uwansu ga ƴaƴansu, sun kasa gane hakan yanada matuƙar tasiri ga zukatan ƴaƴan, dan in har akai wasa su ƴaƴan zasu tashine da ƙiyayya mafi muni da tsauri ta waɗan nan ƴan uwan nasu koda ace su daga baya sun haƙura sun yafema juna ne. Shiyyasa mafi yawan zuminci ke ƙara lalacewa da taɓarɓarewa a zukatan kowacce zuria fiye da ƙyamatar kafurci. Tasirinsa ne a tsakanin Anam da Fadwa duk da suna amsa sunan jini ɗaya, amma tunda ba uwa ɗaya ta haifi iyayensu ba, sun ɗauki hakan babbar tazara da bazata iya basu wata ƙyaƙyƙyawar jituwaba sai ƙyara da hantarar juna kawai. Sai kuma ga KISHI ya ratsa, wanda yake zamtowa linzami na rasa imanin MATA da yawa a dalilin zafafawa, ko da sunada tabbacin bazasu iya canja ƙaddara ba).
          A jiya kasancewar su Aunty Malika tattare da ita ya sama zuciyarta salama da ɗauke kaso mafi yawa na hankalinta, musamman da zuciyarta ta dinga ayyana mata Shareff a sashensa ya kwana. Amma yau ganin zahiri ya hanata nutsuwa balle fahimtar kanta da kanta a matsayin abinda bazai iya canjawa ba ko samuwar ikon hanawa tamkar kowacce mace irinta. Kuka taci bana wasa ba, wanda ya jata lokaci mai tsayi har kusan ƙarshen dare sannan barci ɓarawo ya fara rinjayarta. A hankali ta sulale akan gadon ƙirjinta cike da nauyi tamkar yanda idanunta ke tattare da nauyin barci. (Koma dai miye ta bani tausayi, mu ƙiyasta kammu a matsayinta bisa adalci na rayuwa. ALLAH ka bamu kishi mai sauƙi da bazai sakamu a nadama ba????????????).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button