BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

  Idanu ya waro da sauri jin zatai masa fallasa, ya daura yatsansa akan lips ɗinsa alamar tai shiru, ta gefe kuma yana nuna mata aunty Mimi da ido. Sai dai kuma bai san sarai aunty mimin na kallonsu ba ita da doctor. Ta ƙunshe dariya da kyar, Dr Bilkisu dai kasa dannewa tai sai da tayi tata.

“Ayya karki damu insha ALLAHU zai daina, idan na sallameku zan baki dukkan dabarun da zasu taimaka miki har ki dawo normal a cigaba da amarci ko”.

   God forbid”.

Ta faɗa a hankali samman lips ɗinta. Da ɗan ɗagowa zata hararesa suka kuwa haɗa ido. Babu shiri ta mayar ta risinar. Har doctor ta gama ƙara duddubata bata sake yarda ta kalla sashen da yake ba dan tuni tace masa ta ƙoshi da abincin. Shima dai kunya ta hanashi sake wani motsi, dan ya san dai aunty mimi ta gama fahimtar komai kuma. Magungunnanta ya bata ta sha kamar yanda Doctor tace. Sai da ya tabbatar komai yayi normal sannan ya mike yana kallon agogon hanunsa. 

    “Small Mom ni zanje gida nai wanka bara na maidaki, inaga sai zuwa anjima zan dawo. Aysha ki kula da ita idan da buƙatar wani abu sai ki kirani a waya. Bana buƙatar wani yasan da zamanku anan, idan hakan ta faru ranki sai yafi nawa ɓaci”.

   Aysha ta amsa masa da to.

“Karka damu Babana jeka kawai harka dawo, bara naga likitar nan. Aunty Mimi ta faɗa kai tsaye tana miƙewa ta fita. (Shike nan na mutu) ya ayyana a ransa da bin aunty Mimin da kallo. Itako Anaam tuni tai kwanciyartama ta juya musu baya. Har tayi zaton ya fice sai ga saukar numfashinsa a cikin kunnenta, da sauri ta juyo dan ta tsorata, hakan ya bawa fuskarsu damar haɗuwa, ƙoƙarin jan tata tai baya ya hana hakan ta hanyar riƙota.

    “Ina alfahari da ke a wannan rana, alfahari irin wanda zuciya bazata iya ƙayyadewa ba, hannu bazai iya zanawa ba, ke ɗin zinariya ce, idan nace zinariya ina tabbatarwa duniya zinariya a tsakkiyar duhuwar jeji, amsar itace, Haskenki kaɗai za’a iya gani”. 

    Daburcewa tai, sakamakon saukar lips ɗinsa akan nata, ta shiga son ture masa fuska, amma yaƙi yarda da hakan har sai da yay yanda yake so da ita. Yana sakinta sashen da Aysha da aunty mimi suke ta fara kalla, sai dai wayam da alama ma duka basa a ɗakin. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke da saurin kauda kanta saboda ido da suka haɗa da shi. Murmushi ya saki mai faɗi da yalwa dan ya fahimci catake su Aysha na a ɗakin.

   Sake ranƙwafowa yay kanta har lokacin murmushi shimfiɗe a fuskar tasa. “A ƙara ko? Nima ban ƙoshiba”.

  Ture fuskarsa tai da sauri tana jan bedsheet ɗin dake a matsayin bargo ta ƙudundune kanta. Murmushinsa ne ya ƙara faɗaɗa, ya girgiza kansa kawai da juyawa ya fice a ɗakin.

   Sallamar Aysha ta sakata sakin ajiyar zuciya, sai da taji ta zauna a kusa da ita sannan ta buɗe kanta. “Da alama dai kin samu sauƙi tunda naga Yaya ya fita yana faman murmushi”.

  (Ba dole ya fita yana murmushi ba tunda ya gama yayyagani) a fili kam sai ta taɓe baki da yunƙurawa zata tashi zaune. Taimaka mata Ayshan tayi ta zauna cikin dauriya dan ƙasanta sosai yake mata zafi zamanma dai tayisane irin na kishingiɗa ɗin nan..

  Aysha ta sauke ajiyar zuya tana kallonta, “Dan ALLAH ki kwantar da hakainki na tabbatar zaki ji daɗin zama da Yaya Shareff insha ALLAHU Blood. Yanada ƙyawawan halaye da lokaci ne zai tabbatar miki da hakan kamar yanda nasan kema kina da su. Hatta Fadwa bana son ki biye mata dan ita kanta komai na ƙiyayyarki tanayine ba’a kan tunaninta ba, tunanin su Mommy shike sarrafata tun farko, amma wlhy inhar kika jajirce sai kin ƙwace komai kuma a hankali Mommy zata fahimceki halayen banzar da Gwaggo ta ɗorata a kai duk zata ajiyesu kodan son da takema Yaya”.

   A karan farko Anaam ta saki murmushi. “Blood wannan ba magana bace ta nan, Please share kawai yanzu dai ya mutanen gidan? Ina kewarsu ALLAH kamar nai tsuntsuwa na ganni ciki”.

   “Aiko bazaki ganki ɗin nan ba, dan a gabana su Abba sukace kar Yaya ya kawoki gida sai bikina”.

   Sosai ta waro idanu waje, “Bikinki fa? Hum’um ALLAH bazan iya ba. Dana koma aiki monday zaku ganni”.

   “Hhhhh ashe Yaya zai ɓalla miki ƙafar baya kuwa”.

  (Yanzu ma ai ya ɓalla min) Anaam ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai tayi murmushi kawai….

  ★★★★

Yanzun ma daya dawo gidan bayan la’asar yaso shareta, sai dai zuciyarsa ta gargaɗesa a kan hakan dan koba komai hakkintane a wuyansa. A falo ya sameta zaune ta ƙurama tv ido. Mmn Abu na daga kitchen tana aiki dafa mata indomie dan duk yau taƙi cin komai sai tea kawai. Sai yanzu da yunwar ta cita ne sosai bayan tayi wanka ta fito falo tasa mmn Abu din ta dafa mata. Kallo ɗaya tai masa ta kauda kanta, sai dai ta amsa masa sallamar da yay ciki-ciki itama akan lips. Motsin mmn Abu a kitchen ya sashi wucewa bedroom.

   “Ki sameni a ciki”.

Shiru kamar bazata bisaba, sai raka bayansa da tai da harara ƙasa-ƙasa. Sai da taja kusan mintuna biyu sannan ta miƙe ta bisa. Tsaye ta samesa ya jingina da mirror. Taima fuskarsa kallo ɗaya ta ɗauke kanta da kaiwa zaune bakin gado. 

  “Ɗazun ina tambayarki mike damunki kin tashi kin barni saboda raini. Ina gargaɗinki da karki tsiro da wata sabuwar ɗabi’ar banza, hakan zai sa mu sami matsala da kowaccenku idan tace zata dinga kawomin raini wlhy”.

     Tasan halinsa, dan haka a hankali tace, “Kayi haƙuri”. Batare data ɗago idanunta da suka cika da ƙwalla ba. 

  Duk girman laifin dakai masa idan ka bashi haƙuri yakan ɗanji sassauci ko yaya. Dan haka ya furzar da huci kawai. Sai kuma ya sake kafeta da idanun nasa. “Kina fushi da ni saboda na fita da ƴar uwarki, maimakon ki fara neman ba’asin mike faruwa kodan jimawar da kikaga munyi a waje batare da mun dawo ba. Sannan yanayin dana fita da ita a gidan nan yana nuna akwai matsala amma duk kika zaɓi ganin baƙina akan bincikawar!”.

    Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo mata. Tasa hannu ta sharesu. “Ni baca nai kayi laifi ba, amma ya kamata tunda ina a gidan na sani, a ƙalla dai an nuna inada daraja ko yayane, amma ta gabana ka wucefa Soulmate tamkar baka ganni ba saboda ka ɗauka mace a hanunka….”

   “Macen dana ɗauka matata ce, kinga hakan yana nufin babu haramci a ciki kenan, kema kuma nasha ɗaukar taki ai. Ki tsaya a laifin ba’a faɗa mikiba kawai bawai ɗaukarta ba. Sannan wannan ya zama na farko ya zama na ƙarshe da zanzo ina miki magana koda kuwa laifin na miki ki maimaita irin abinda kikaimin ɗazun, bazan ɗauki wannan salon ba ga kowace”.

   Duk da maganganunsa sun ƙona mata zuciya saita jinjina masa kai kawai. Shima bai sake cewa komaiba yay ficewarsa zuwa sashensa. Har yanzu ba’a kwashe kayan abincin safen ba. Dan haka yay kiranta a waya. Tana ɗagawa ya sanar mata tazo ta kwashesu ya yanke wayar.

    Wanka yay, koda ya fito sai ya ɗan kwanta duk da barci yake sonyiba yana son hutawa dan shi ɗin kansa jikinsa duk ciwo yake masa. Ga yunwa na cinsa kaɗan-kaɗan dan duk yau bai wani ci abincin kirki ba. Lokacin da sukaje salla da Dr Jamal bayan sun fito massallaci gidan abinci sukaje. Amma sai ya kasa nutsuwar cin komai sai doughnut kawai ya ɗanci da drink. Daga nan ya nufi gidansu sai dai bai shiga wajen su Mommy ba ya shiga nasu Anaam da niyyar ɗakko Amrah ta zauna da ita a asibiti sai ya iske bata nan. Mamie tayi masa tayin abinci amma sai yace ya ƙoshi yana sauri ne, amma baiwar ALLAHr sai gata da shi ta haɗo a basket saboda tasan abincin da yake matuƙar so ne. Harda plate da drink da alama tayi tunanin office zai koma dan yace mata yazo ɗaukar wasu takardune zai koma wajen aiki. A sirrance ya sanarma Aunty Mimi suka fito tare kamar zasu cikin gida, hakan yasa Mamie bata sani ba. Abincinne ya kaima Anaam taci shiko baima cin ba duk da yana so……….✍[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button