BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

39

………Alhmdllhi amarya ta iso gidanta lafiya, ta kuma samu tarba daga wajen dangin mahaifiyar su Daddy da suma sukazo suka taru anan domin nuna gata gasu daddy ɗin, duk da tun zuwan nasu ƙawayen aunty Halima dake gidan zagaye da Fadwa suka kirata suka sanar mata. Babu ko kara na tuna cewa dangin mahaifiyarta ne ta kirasu tai musu tas a waya da tabbatar musu zata iya da makircin kowa daya nuna goyon bayansa akan aima ƴarta Fadwa kishiya, kishiyarma ɗiyar ƴar uba. Inna Suwaiba! Wadda ta kasance ɗiyar wan maman su daddyn ce ta amshi waya tai mata tas itama dan in masifa ce ta fita iyawa, ai ko babu shiri ta yanke wayar tana zage-zage.

    Kowa ya yaba sashen amarya tare da jinjinama ƙoƙarin iyayenta, dan tabbas kam sun nunama duniya ita ɗin ɗaya ce tilo a garesu kuma ƴar gata. Cikin raɗa Mom da Hajiyar sudan suka sake yima Anam da keta sauke ajiyar zuciya nasiha. Rungume Mom tayi, muryarta a ɗashe alamar taci kuka mai yawan gaske tace, “Mom ni bana son sa dan ALLAH, Mom karku barni anan zan iya mutuwa”. Mom dake rungume da ita tana shafa kanta tai murmushi. “To kiyi haƙuri, zan samu Abbanku nai masa bayani yanda zai fahimceni, yanzu dai ki kwantarmin da hankalinki kinji”.
 Da sauri ta fiddo fuskarta dake cikin mayafi tana kallon Mom da jajayen idanunta da suka kumbura matuƙa saboda kuka. “Mom dan ALLAH da gaske?”. Hajiyar Sudan Da Mom suka haɗa ido, murmushi sukayi, kafin Mom ta jinjina mata kanta “Da gaske mana. ba Baba ibrahim ma yace nanda wata uku indai da wata matsala zai ɗauki mataki ba”. Sake rungumeta tai tana jinjina kanta fuskarta na bayyanar da murmushin da tunda aka fara badaƙalar auren nan ba'aga irinsaba a fuskarta. Cikin dabara hajiyar Sudan ta fita a ɗakin, dan dama su kaɗaine suka rage mutane duk sun fice kowa na tsoron ya rasa mota. Lallashinta Mom ta ƙarayi, kafin itama ta miƙe cikin dabara da plan ɗin da suka haɗa da hajiyar sudan.
  Hajiyar Sudan ɗin ce ta leƙo tai kiranta wai tazo taga wani abu, miƙewa Mom ɗin tai tana gyarama Anam zama. “Kinga zauna ina zuwa”. Ji Anam tai kamar dabara zasu mata, sai dai kafin tai wani yunƙuri Mom ɗin har ta fice a ɗakin, tun tana irga seconds harta koma minutes, ganinfa alamar mintuna kusan goma sun cika babu alamar motsi ma ya sakata miƙewa da sauri hawaye na ciko mata ido. Tabbas babu kowa a falon, hakama sauran ɗakunan zuwa kitchen, wasu irin zafafan hawaye ne suka silalo mata, ta dafe kujera saboda jiri dake neman ɗibarta, da ƙyar ta iya maida kanta bedroom ɗin da suka barta, ta zube a kan gadon hawayen na cigaba da sauka a guje dan bata da ƙarfin yin kuka mai sauti.....

  Gida ya koma tsitt, duk da sashen Fadwa har yanzu akwai wasu ƴan uwan babanta uku na hanun damar Gwaggo halima da su Mommy basu da alamar barin gidan, sun zagaye Fadwa dake kuka suna ƙara mata fanfo dan ba'ace nasiha ba. A kallo ɗaya zaka tabbatar da taci kuka itama har ta godema ALLAH, dan hatta da muryarta ma ta dishe. Gaba ɗaya ji take Shareff ɗin ma ta gama tsanarsa, ko ganinsa bata sonyi shi da duk wanda ya shafesa. Tsoron mahaifintane kawai ya taka mata birki akan ƙudirinta na barin gidan, amma batajin zata iya cigaba da rayuwa da Shareff ƙarƙashin inuwa guda da maƙiyarta, yarinyar datai matuƙar tsana a rayuwarta ace a yau itace kishiyarta, kishiyarta da zata iya shearing da mijinta abin sonta. Kai ina wannan ma maganar tatsuniyace, za kuma ta tabbatarma duniya cewar tatsuniyar ce...

 Duk wannan hidima da akeyi ango Shareff na can gidansu gurfane gaban su Daddy suna sake masa nasiha da jaddada amanar matan nasa a hanunsa domin a yanzu matsayi guda suke amsawa a wajensa. Kuma su dukansu ƴan uwansa ne na jini da basa fatan zuminci ya samu wani nakasu ko rauni a dalilin aurensu. Basu barsa ya baro gidan ba sai da ƴan rakiyar amarya suka koma. Yay musu sallama ya fito. Babu sashen daya shiga, dan shima yasan baida wannan damar a yanzu. Ga kuma kansa na masa matuƙar ciwo ma na hayaniyar da aka sha ga kuma jikinsa da bawai ya gama dawowa dai-dai bane shima dama. Dauriyace kawai da ƙarfin zuciya irin ta maza.
  Duk yanda abokansa suka so masa rakkiya kamar auren Fadwa ƙi yay, dole suka haƙura suka gudu sai Fharhan ne kawai dazai jasa a mota dan shi bama zai iya driving ɗin ba. Da farko tsokanarsa ya dingayi, sai da yaga baya cikin good mood ne ya koma nasiha a garesa, dan kuwa dai shi ɗin shaidane akan abinda Shareff yake ɓoyewa a zuciyarsa tsahon shekaru, sai dai ko'a yanzun ma bai nuna masa yama fahimcesa ba yadai bashi shawarwari kawai. Har suka iso bai dai ce komai ba, sai da zai fita ne yace masa “Thanks” a taƙaice. Da kallo kawai Fharhan ya bisa, sai kuma ya girgiza kansa yana murmushi.

    Kai tsaye sashensa ya wuce duk da yanada tabbacin zuwa yanzu babu kowa a gidan, ya zube cikin kujera yana furzar da huci mai zafi lokacin da yake kai bayansa ga kujerar. Ya lumshe idanunsa da yake jin sun masa matuƙar nauyi. Kusan mintuna goma ya ɗauka a wajen yana kokawa da abinda zuciyarsa ke saƙa masa, kafin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Wanka ne a ransa, dan haka bai zauna ba ya zame kayan jikinsa ya shige bathroom. Koda ya fito jikinsa kawai ya tsane ya zura jallabiya yasa turare kaɗan. Hakkinsa ne ya duba kowaccensu, duk da kuwa tunda Fadwa ta dawo gidan taƙi yarda su haɗu. Sashenta ya fara zuwa batare da tunanin zai samu kowa ba. Turus ya ɗanyi da mamaki, hatta fuskarsa sai da ta nuna dan bai zaton samun kowa ba. Fadwa da ke kwance ta ɗora kanta saman cinyar aunty Malika tai masa kallo ɗaya ta kauda kanta tana jan siririn tsaki ciki-ciki yanda bazaiji ba. Kallonta yake amma taƙi yarda su haɗa ido, ya ɗan girgiza kansa kawai. Komai baice ba ya fito a falon dan ko sallamarsa babu wanda ya amsa a cikinsu, sai kuma binsa suke da kallon banza....
   “Lallai wannan mijin naki ya cika ɗan iska Fadwa. Yanzu muna amtsayin ƴan uwan uwarsa amma yay mana wannan kallon banzar babu ko gaisuwa ya fice”.

“Ke ko ya zai gaishemu kansa na hayaƙin asiri Safarah. Ai bayin kansa bane, dole fa su Aunty Nafi (Mommy) sai sun tashi tsaye dan Shareff ya shiga kaidun waɗannan mutanen wlhy”.
Kuka Fadwa ta sake rushewa da shi tana kiran ta shiga uku. Cikin zafin rai wadda batace komaiba tun ɗazun ta daka mata tsawa. “A gidan ubanwa kika shiga ukun? Idan taƙamarsu asiri da tsubbu gaban iyayen gidansu sukazo. Har miye su? Mi akai akayi wannan ƴar yarinyar da bata wuce ki fetota a hancinki da makirci kawai ba. Danni banga abin ɓata lokaci agareta ba balle kuɗi na neman asiri. Wannan yaƙin da kanki zakiyisa in har kin cika ke ɗin jinin baba yalwa ce (Kakarsu data haifi mahaigiyar Mommy, Gwaggo, mahaifin Fadwa, mahaifiyar Bibah).
“Aunty Lawusa dolene nai kuka, wlhy shima na tsanesa, bana son ganinsa munafiki ne”.
Yanda take maganar tana kuka yasa Aunty Malika sake jawota jikinta ta rungumeta. Kuka ta sake fashewa da shi. “Aunty yanzu fa zuwa zai ya kwana da ita, shike nan sun rabani da mijina…..”
“Basu isa rabaki da mijinki ba, ki kuma kwantar da hankalinki shi bai isa kusantarta ba, bama a yau ba har abada, yanda ta shigo haka zata bar miki gida sai dai ta koma ta cigaba da rabama abokan shashancin nata a ƙasar data fito”.
Ɗagowa Fadwa tai tana girgiza kai, “Aunty baki san waye Shareff bane, wlhy sam baida haƙuri akan mace, ko faɗa yay da ita zai iya neman biyan buƙatarsa shi babu ruwansa”.
Dariya aunty Lawusa tayi sai kuma ta haɗe fuska. “Malama ki mana shiru haka, idan shi hrj ne ƙarshen dai maitar mace kenan ko? To bai isa tarayya da yarinyar can ba har abada tunda ya taka abun can da ƙafafunsa”.
Sosai Fadwa ta zaro idanu “Aunty wane abu wai?”. A tare suka sanya mata dariya, aunty Malika ta fiddo ƴar kwalba a jikkarta har guda 2. Ba kinga nayi turaren wannan ba ɗazun? Na kuma barbaɗe ƙofar falonki da wannan yanzun?”. Kanta ta jinjina mata. Ta dafa kafaɗarta tana murmushi, to wannan da kike gani sunansu ɗan kaɗafi da ni kaɗai ce mace mu dukanmu nan babu wacce bata aiki da shi a gidanta, kuma munga biyan buƙata shiyyasa kema muka amso miki, dan haka ki kwantar da hankalinki indai wannan yarinyar ce da ƙafafunta zata bar miki gidanki, ko zasu kwana manne da juna wani abu bazai taɓa shiga tsakaninsu ba”.
“Ni wlhy ko gadon ma bana ƙaunar su haɗa aunty, kai ko hanunta bana son ya taɓa riƙewa a gidan nan”.
“Wannan duk mai sauƙi ne, kedai kawai ki saki bakin aljihu, dan yanzu babu boka babu malam maganin mata sune ke ƙwatar mace, shiyyasa mukayo miki haɗinsu gasu nan na musamman yanzu haka ma Hajarah zata taho miki da wasu daga Niger, Fadwa sai kin koma juya Al-Mustapha inda kike so, balle ke ma da kika gama morewa da samun mabuƙaci, ta wannan hanyar zaki banbance masa tsakanin aya da tsakkuwa ki kuma damƙe abunki dan dama naki ne shi kaɗai. Tun farko su Aunty (gwagg halima da Mommy) sunyi sakaci ai da basu haɗaki da haɗi na musamman ba kafin aure da Shareff bai taɓa kallon wata mace ba, kai auren nan ma da bai sai sun wahal da kansu ba da kansa zai bijire wlhy. Amma ko yanzu bata ɓaci ba muna tsaye kanki”.
Fuskar Fadwa ta washe da murmushi, ta rungume auntys ɗin nata cike da farin ciki, jitai gaba ɗaya duk wata damuwarta tama gushe, dan tayi imani da duk abinda suka faɗa tunda ita ɗin shaidace akan yanda suke juya gidansu da mazajensu duk da sunada kishiya, aunty Malika ma su uku ne amma idan kaga yanda mijinsu ke rawar kai a kanta saika ɗauka ita ɗaya garesa ko kuma amarya, sai dai itace ta tsakkiya……..✍????

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

38

…………Duk da da sauran safiya hakan bai hana ta samu tarba daga mafi yawan jama’ar gidan ba. Musamman ma yaran dan suna shirin wucewa school ne suka iso. Duk sai da suka shiga sukai mata sannu da yaya jiki, bayan wucewarsu shima Shareff yay musu sallama ya fita dan wajen aiki zaije. Mamie da kanta ta taimaka mata tai wanka, bayan ta fito ta ƙara taimaka mata ta saka kaya sannan ta fiddota falo wajen su Daddy da suka shigo dubata.
Kanta a ƙasa ta gaishe su duk suka amsa mata da kulawa da tambayar jikinta. Abba ne yay ɗan gyaran murya idonsa a kanta. Ɗagiowa tai a hankali ta dubesu, ganin su duka ukun idonsu a kanta yake ta maida ta sake duƙarwa.
“Mamana!”.
Abba ya kirata cike da kulawa.
Cikin rawar murya ta amsa masa. Yay ɗan murmushi da sake gyara zamansa. “Kin yarda muɗin iyayenki ne bazamu taɓa cutar da ke ba?”.
Kanta ta jinjina masa tana haɗiye hawayenta. Ya cigaba da faɗin, “Alhmdllhi naji daɗi da kika fahimci haka, ina kuma fatan ki kasance mai biyayya tamkar yanda shima ɗan uwanki ya kasance amatsayinsa na namiji. Duk da nasan abinda mukayi munyisane akan gaɓar data dace akaran kanku bawai zumincinmu kawai ba. Ki ƙara daurewa ki zama mai haƙuri da biyayya, domin aure dai an riga an ɗaura, ba kuma yanzu aka ɗaurasaba ko jiya, an ɗaurashi rana ɗaya dana ƴar uwarki kamar yanda Yaya ya faɗa ranar a gaban kowa, sai da aka ɗaura naki da safe sannan aka ɗaura nata da azhur, hakan yasa ko shi Shareff bai sani ba, mun kuma ɓoye ne saboda wasu dalilai, hakama a yanzu mun bayyana a gareku da kowa ma saboda wasu dalilai. Dan haka zaki tare ranar juma’ar nan insha ALLAHU a ɗakin mijinki. ALLAH yay miku albarka, ya baku zaman lafiya da zuria masu albarka da MANZON ALLAH zai alfahari da su kamar yanda muke fatan yay alfahari da ku da mu baki ɗaya.”
Kuka takeyi sosai. Sai tausayinta ya kamasu, kiranta Daddy yay ta rarrafa zuwa gabansa. Hanunsa ya ɗaura saman kanta ya shiga saka mata albarka da mata nasiha mai ratsa jiki tamkar yanda Abbah yay mata. Shi dai Abie bai ce komai ba yana dai kallonta ne kawai. Hakama Mamie da aunty Mimi. Sai da suka tabbatar ta tsagaita da kukan da takeyi sannan suka fice su duka, Aunty Mimi ce ta dawo kusa da ita, jikinta ta jawota ta rungume tana lallashinta, a haka su Mom suka shigo suka samesu ita da aunty Amarya. Suma dai nasihar sukai mata da lallashi. Daga ƙarshe Mom tace hajiyar sudan zata zo ta ƙarasa aikinta tunda wancan yabi iska.
Ɗakinta ta koma ta cigaba da kuka har barci ya kwasheta, bata kuma farka ba sai kusan azhar da hayaniya ta isheta. Wanka tai cikin rashin ƙarfin jiki sannan ta fito, ganin akwatuna barbaje a tsakkiyar falonsu ga mutane cike anata kallo ya sata komawa da sauri tana faman tura baki. Amrah ta kira cikin roƙo tace ta kawo mata tea, babu jimawa kuwa ta kawo mata tana tsokanarta da fara bata labarin kayan lefen da aka kawo mata. Duk da bata da ƙarfin jiki haka ta kora Amrah waje ta sakama ɗakinta key dan bata buƙatar jin komai. Saboda ma ta kauda abun a ranta sai ta ɗauki lap-top ta kunna film abinta, tana shan tea tanayi, data gama shan tea ɗin sai ta kwanta ta cigaba da kallon a haka tana jiyo hayaniyar gidan har lokacin sama-sama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button