BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

46

………Kaɗan ya rage ta hamɓarar da wayarta dake ajiye, Baki ta tura da sakin numfashi mai kauri tana kai hannu saman ƙirjinta dake bugawa da sauri-sauri. Har lokacin bai motsa daga tsaiwar da yay jingine da bango ba ƙafafunsa a harɗe cikin na juna hakama hannayensa, sai dai cike da basarwa ya kauda idanunsa da tun ɗazun suke ƙare mata kallo tamkar ya samu television.
       “Gaskiya irin haka babu ƙyau, a tsorata mutum idan zuciyarsa ta buga fa?”. Ƙasa-ƙasa take maganar da yaren Tamil (shima yana cikin yarukan ƙasar malaysia, kuma Anam ta iya sosai, sai dai bata san shima Shareff yana jin yaren ba, duk da a yanzu bazai iya magana mai tsaho da shi ba, sai dai komai ka faɗa zaiji zai kuma baka ƙananun amsoshi). Ta ɗan saci kallonsa, sai kuma ta juya cike da basarwa tana faɗin, “Good Morning”.
      Maimakon amsawarsa tsaiwarsa taji a bayanta, taso ta dake, amma kusancinsu yaƙi bata damar hakan. Sai ta kashe oven ɗin kawai ta juyo da nufin barin wajen, komawa tai da sauri ta lafe jikin kitchen cabinet ɗin tana marmar da idanu, abubuwa da yawa sai tsarga mata suke da ga tsakkiyar kai zuwa ƙafafu saboda tsaretan da yay da idanunsa masu matuƙar kaifi da saka mata shakkarsa a lokuta da dama. Rashin mafita ya sata sake cemasa “Good morning” a karo na biyu.
      Kansa ya jinjina mata idonsa akan fuskarta da babu kwalliya. Yana matuƙar son yaga mace da kwalliya, musamman jambaki, hakan yana ɗaya daga cikin abinda Fadwa ke tasirantarwa a zuciyarsa. “Mi kikeyi anan?”.
    Ya faɗa cikin dakewa idanunsa har yanzu na yawo a jikinta. Itama dakewar tai, cikin ƙin nuna fargabar kusancin nasu da pretending ɗin daren jiya ta bashi amsa. “Ina warming meat pie ne”.
     Komai bai ceba, sai dai ya kai hannu zai cire meatpie ɗin daga cikin oven data riga ta kashe, ƙwara uku ne kawai sai cinyar naman kaza ɗaya. Wani plate ɗin ya ɗauka ya rufe sannan ya dubeta.
      “Muje”.
  Mamaki bayyane a kan fuskarta tace, “Yaya ina kuma?”.
  “Inda ake saida mutane”.
Tasan baƙar magana ya gaya mata dan haka tai shiru. Har tayi gaba taji ya riƙota, idanu ta rumtse wani abu na tsarga mata, ta juyo a hankali ta kallesa da idanunta dake cikin glass, ganin ita yake kallo shima ɗin ya sata kauda kai bakinta a sama. Jawota yay gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa, tana yunƙurin ɗagawa ya saƙalo hanunsa a ƙugunta ya maidata ya manne. Kusancin fuskarsu ya basu damar shaƙar numfashin juna. Sosai ta ƙwaɓe fuska tana son janye jikinta amma yaƙi bata dama. Sai idanunsa dake yawo a fuskarsa ne ke neman dagula mata lissafi.
       “Yau ta zama ta ƙarshe da zaki sake tahowa bada izinina ba”. 
Kallonsa tai, sai kuma ta janye idanun da sauri. Shima janyeta yay a jikin nasa ya nuna mata hanya. Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa dan gaba ɗaya yaci dukkan ƙudirinta da yaƙi a halin yanzun. Kwarjini da kamewarsa ta saka mata jin kasa masa musu. Kusan a tare suke tafiya duk da yanda take takun a hankali duk dan ya wuceta….

 Sosai ta dinga ƙarema gadon kallo zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Ga wani irin zafi da zogin da ƙirjinta yake mata. Jitai bazata iya ƙarasa abinda tai niyya ba, tai saurin fita a ɗakin kanta na wani irin sara mata alamar ciwo. A falo ta zube ta shiga ƙoƙarin saita kanta tun kafin waninsu ya shigo. Sai dai kuma har tsahon mintunan data gaji da irgawa babu ko mai kamarsu, hakan ma ya ƙara sosa mata rai, tana shirin miƙewa ta tafi sai gasu sun shigo kowane da sallama ciki-ciki. Da ƙyar ta iya amsawa batare data kalli Anam ba.  

     Sai da duk suka zauna cikin son danne komai tacema Anam ɗin ina kwana. Anam da tun shigowarta itama bata dubi sashin da take ba tai mata banza kamar bataji ba. Haka dama Fadwa ke buƙata, dan haka tai murmushi tana satar kallon Shareff da yay kamar hankalinsa baya kansu.
      “Amarya nace an tashi lafiya?”.
  Ɗago ido tai a karan farko ta kalleta ta watsar, sake maida hankalinta ga wayarta dai-dai da ɗagowar Shareff ya dubi Anaam ɗin ransa a ɓace, sai dai kuma ya haɗiye fushin nasa da kai hannu kan bluetooth ɗin dake manne a kunenta a zatonsa shine ya hanata jin Fadwa ɗin kuma. Saurin dafe kunnen tayi da kallonsa dan tasan babu abinda take saurare a ciki kawai dai bazata amsawa Fadwa ɗin bane. Ta zareshi gaba ɗaya fuskarta da babu kwalliya na ƙara shagwaɓewa.
     Hannunsa ya miƙa mata alamar ta bashi, amma sai ta maƙe kafaɗa, cikin muy-muy da baki take faɗin, (Mazuran nan fa dai kowa ya iya ai, niba tsoro nake ba dan kayi), A fili kam sai cewa tai, “Yaya miya faru?”.
      Hararta ya ɗanyi da sake miƙa mata hanunsa. “Karna sake ganinki da wannan abun a lokacin da muke tare baki ɗaya. Ana magana ko jin mutane baƙyayi. Bani nace”.
     A marairaice tace, “Nafa cire”.
Matsowar da yay idonsa tamkar zai faɗo saboda kallon da yake watsa mata mai kama da harara ya sakata zabura tai ɗan baya kaɗan tare da tura bluetooth ɗin cikin rigarta saboda hango murmushin da Fadwa tai na alamar cin nasara, sai kuma tunawa da yanda yay mata da key jiya da dare ya sata ganin itama idan tai haka dole zai barta ai, dan hanunsa dai tasan bazai shiga nan ya ɗauka ba.
      Tsamm Fadwa ta miƙe ta nufi kicin ɗinsa ranta fes da ganin fushi a fuskarsa, ta tabbatar Anaam ta cigaba da jaa akanta zai saukesa. Laɓewa tai tana leƙensu da kasa kunne da ƙyau dan jin yaya za’a ƙare.
      Cikin bada umarni da ƙara tsuke fuska ya sake miƙa mata hanu “Ciro ki bani da arziƙi”.
     “To ni Yaya dan ALLAH mi zakayi da shi? Badai na cireba shike nan, kuma ai banji bane”.
   “Dama ba lallai sai kinji ba ai, bani”.
Kanta tai niyyar ɗaukewa taji ya damƙo hannayenta, zabura tai tana waro idanunta dake cikin gilashi gaba ɗaya waje saboda tsantsar firgicin jin ɗayan hanunsa cikin rigarta yana laluben bluetooth ɗin data tura a bra….
      Har taune harshe take wajen faɗin, “Yaya Please w…Wlhy zan baka, tsaya ka tsay…”
    Ko nuna alamar ya jita ma bai ba ya tura hanun nasa har cikin bra.. ɗin ya ɗakko bluetooth ɗin. Zuwa sannan gaba ɗaya jinin Anam ya tsaya cak da daina zagayawa tsabar firgita da abinda yay ɗin. Shiko ƙememe babu alamar kallon abinda yay ɗin da girma tattare da shi. Saina hararta da yayi ya ɗauke kansa.
      Fadwa dake yunƙurin fitowa tai mutuwar tsaye, dan jitai tamkar saukar aradu a tsakkiyar kai, a zatonta yanda ya harzuƙa da farko mari zai saukewa Anaam akan fuska. Jin hawaye na ciko mata ido tai yunƙurin komawa cikin kitchen ɗin
     “K kuma ina zaki?”.
Ya faɗa dai-dai yana saka bluetooth ɗin cikin aljihun wandonsa idanunsa akanta. Amsa ta bashi batare data yarda ta kallesa ba tana wucewa. “Ina zuwa nayi mantuwa ne.
    “Kin san dai yunwa nakeji”.
“Kayi haƙuri ina zuwa”.
Ta amsa masa hawaye na sakko mata. Da ƙyar ta iya kai kanta jikin kitchen cabinet ɗin ta jingina saboda jin hajijiya na neman zubdata. Tasan shi din mutum ne kai tsaye, amma batai zaton iya yin hakan a gabanta ba, koda yake ba’a gabanta bane tunda ta tashi, maybe kuma baiga sanda ta fito ba shiyyasa. Da wannan ta bama kanta ƙwarin gwiwar share hawayenta ta goge fuskarta ta sake fitowa.
      Kofuna da plates data ɗakko ta ajiye tana magana cikin ɗan murmushin yake. “Am sorry Soulmate, bismillah ku sakko”.
     Harta kammala zuba Irish ɗin ma kowa Anaam da har yanzu mamakin Shareff ya kasa barinta bata iya ta sakko ba. Sai da suka fara cin abincin ya ɗago ya harareta sannan. Bataci dankalin ba, meatpie ɗinta ta ɗakko. Yi yay kamar bai ganta ba, sai Fadwa ce tai magana cike da kulawa a gareta. Dan burinta bai wuce ta wanke zuciyar Shareff akanta ba ya tabbatar ta amshi nasiharsa a gabansa, ta hakane kawai za’a fara wasan da zataci nasara akan Anaam dake nuna ƙuru-ƙuru kishinta takeyi, ba kuma zata iya ɓoye abu ba, tabbas hakan nasararta ce ta yaƙarta cikin sauƙi a wajen mijinta. “A’a Amarya bara a haɗa miki tea ko, kamar zai fi ki haɗa da shi”.
       Anaam data kalli kamar rainin wayon Fadwa ya fara yawa a kanta ta ɗago tana mata kallon ido cikin ido. “Madam mind your business abeg. Shin dole ne sai kin sakani a sabgarki ne wai?”.
     Cikin sauƙaƙa murya da karyar da kai Fadwa tace, “Ayya I’m sorry dear ban…..”
   Ɗagowar Shareff dake hararar Anaam a fusace ta sakata haɗiye sauran maganar bata ƙarasa ba. “Ashe zan fasa bakinki yay jini idan wata maganar banza ta sake fitowa a cikinsa. Ya tana miki magana cikin lalama kina wani botsarewa dan walaƙanci!!”.
     Tuni ta daina tauna meatpie ɗin, babu abinda zuciyarta keyi sai tafasa da kumburowa cikin ƙirjinta, musamman da taga murmushin da Fadwa ta saki tana kallonta. Hawayen takaici suka ciko mata idanu, tsam ta miƙe dai-dai Fadwa na faɗin, “Lah babu damuwa wlhy Soulmate. Inaga bata fahimceni bane ba shiyyasa……”
    Bata gama jin ƙarshen zancen ba tai ficewarta……….✍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button