BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

        Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ƙaramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ruƙayya taita juriyar ganin ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman. Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira a waya ta musu ba akan su dawo mata da ɗanta idan sunji haushi su haifa nasu. Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da ɗan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ƙwacesa ba.
       A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ruƙonsa. Shaƙuwa kuma mai nagarta ta gama shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su’ad. Shareff nada shekara biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki. Zokaga murna da farin ciki wajensu, yayinda Mommy ta shiga baƙin ciki dan taso ace sun ƙare rayuwarsu ne babu haihuwa. Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata ɗanta. Sudai basa kulata, dan ko ƙasar zasuzo basa zuwa da shi ma.
       Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ƴarta mace. Mommy da Gwaggo sun ɗanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddarar bawa shi kaɗaine rabon dazai samu ai dama. Ita dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje Malaysia ganin gudan jinin ɗan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ƙwaf sukaƙi. Yarinya taci sunan Juwairiyya, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya da Anam (Blessings of GOD).

         Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buɗa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata. A koda yaushe tana maƙale da shi kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ƙiwa take masa sai shareef. Lokacin da take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami’a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia, dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na’a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa ɗaya, ko inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haɗasu ko hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.
       A haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama cikakken Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Maimakon ya nufi Malaysia kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waɗanda suke tsaye kan ɗawainiyar karatun nasa sai kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matuƙar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya ɓaci har suka sami saɓani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taɓa samu ba. Ya kuma fito fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haɗa kayanta tabar gidan, ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ƙarshe dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai ɗauka abinda Shareff ɗin yayi da wani ɓacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar mizai hana ya buɗe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.
     Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie haƙuri akan shima wani lokacin yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da fahimtar komai akan farraƙa yaron akai da su, bai kuma taɓa yunƙurin nuna ya sani ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take hanƙoro mizaisa ya damu tunda shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuɗin buɗe company, amma sai Abie ya bashi shawarar su haɗa gwiwa kawai…..
      A haɗin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuɗin da zata gina company ɗin, amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuɗin da ake buƙata aka kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, ya kuma gargaɗi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.
     Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan ɗanta yakai tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu ɗaukar Shareff ɗinne ya gina da kuɗinsa. Gwaggo ma ta ɗau abun da zafi, dan ita taita tunzura Mommy akan su ƙara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie yay tunanin haɗa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuɗance har yama fisa arziƙi. Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko’a mafarki bata fatar haɗa zuri’arta dasu Abie a duniya…..

       Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria ɗin ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-zafi. Anam yarinyace ƙyaƙyƙyawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai ƙiriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ƴar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka girmeta bata bari a cuceta balle sa’aninta, tanada baki sosai. A ɓangaren karatu kuwa sam bata da wani ƙoƙari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su Abie suka miƙe kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna’a nesa da ita bata ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ƙarfi bata ganin abu har saida lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai babu ɓata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin gani, amma zai ɗaurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya fisge yaje Malaysia ma bata barin su haɗu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su haɗu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haɗuwar tasu sai ya mata muguntar datake jin ƙarin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda tsiwarta da rashin kunya ido fiƙi-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga ɗaure-ɗauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ƙurar data kwasosa a duniya ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ƙwazon shugaba kwata-kwatansa wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da MM Shareff a taƙaice. Company ne da aka haɗa masu ƙwazo kuma ƙuraye, dan Ya Shareff bai yarda ya ɗauka ma’aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai bama ma’aikatansa damar yin wasan kuma.
     Jajircewar tasa tai matuƙar birge Abie, ya kuma ƙara tsayawa tsayin daka ta bayan fage yana bama Shareff ɗin gudunmawa dan yana matuƙar kaunar yaron har cikin ransa tamkar Anam ɗinsa ƴa ɗaya tilo.
        To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma ɓeranta da tuni yayi nauyi a Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ƙarfi a cikinsa da shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba………✍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button