BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

     Sun sami Fadwa harta kammala shirya abinci, a cikinsu babu wadda ta kalli ƴar uwarta, kuma kowacce ta tsuke fuska babu sauƙi. Shi dai ya cigaba da shan alawarsa yana ƙumshe dariya, a zahiri kam shima tashi fuskar a tsuken take. Fadwa dake zuba masa abinci ta ɗago tana kallonsa, da ido yay mata alamar thanks. Ta ɗan saki murmushi, sai dai ta tsurama sweet ɗin bakinsa ido. Fahimtar hakan da yayne ya sashi zarota ya miƙa mata, ƴar kaɗan ta rage a jiki yama kusa shanyewa, hannu ta kawo zata amsa fuskarta da murmushi itama Anaam dake ɗayan gefensa tai kamar zata ɗauka kofi ta tanƙwaɓe hanunsa sweet ɗin ta faɗa cikin miya. Fiskewa tai kamar bataga abinda tai ba, hasalima taƙi kallonsu. Wani irin takaici da baƙin ciki ya turnuƙe zuciyar Fadwa, amma sai batace komaiba.
      Kallonta yay ta gefe ido shikam dai, sai kuma ya maida ga abincinsa guntun murmushi na suɓuce masa. Ganin har sun fara cin abincin bata da alamar zubawa ya sake ɗagowa ya kalleta. “K bazaki ci abincin ba?”.
Fuska ta ɗan yatsina da taɓe baki, “Ni ban iya cinshi ba”. Karon farko Fadwa ta kalleta, itama fuskar ta yamutse baki a taɓe. Cikin gatse da jin bazata iya shiru ba tace,
“Sai ki fara koya ai”.
Itama a gatsen da taɓe baki tace, “Ba buƙatar hakan”.
Baki Fadwa ta sake laɓewa da ɗauke kai abinta. Itama sai ta harareta ta cigaba da buga game ɗinta.
     Duk yana jinsu amma yay shiru bai sake yin magana ba, sai ma hankalinsa daya maida ga abincinsa hankali a kwance kamar bai san sunai ba. Har suka kammala dai Anaam bata ci ba, shine ya fara barin dining ɗin ya koma falo ya zauna. Fadwa dake shan lemo a hankali ta saki murmushi, dan da farko tayi zaton zai kama lallashi Anaam ɗinne kamar yanda ta san itama Anaam ɗin tayi ne dan ya lallasheta. Amma sai gashi yay biris. Mikewa tai tana tattare kayan da sakin ƴar karamar dariya. “To mudai wannan amarya ta gidanmu uhumm babu alamar ta cika amarya, hausawa na cewa amarya kota buzuzu ce ɗokinta ake, sai dai mu gata mutum a namu gidan bata da wani fawa”.
     Da gaske saƙon na Fadwa yana isa har tsakkiyar kan Anaam. Dan kuwa da turanci take maganar hakan yasa komai ta jisa. Zuciyarta ta fara luguden dakan fusata da sukar da kalaman ke mata amma sai ta saki murmushi a zahiri. Babu burin zamanta a wannan gidan hakan yasa bata fatan Shareff ya nema wani abu a gareta, dan hatta kissing ɗinta da yakeyi tayi alƙawarin baza’a sake na huɗu ba. Sai dai tabbas saita shayar da Fadwa mamaki cikin sauƙi batare da ta rasa mutuncin nata da take tattali ba… A yanzu dai batace komai ba har Fadwa na koƙarin barin wajen fuskarta ƙawace da murmushi. cigaba da zama a dining ɗin tai kamar mai latsa waya, a zahiri kam komai ta kasayi tsabar raɗaɗin da ƙirjinta ke mata…..
      “Amarsu mu kuna lafiya”..
Fadwa ta faɗa tana ɗaga mata yatsu biyu da ɗan ranƙwafawa ta sumbaci gefen fuskar Shareff. Fuskar tata ya shafo shima yana murmushi. Idanunta da suka ciko da ƙwalla ta kauda daga kansu, dama ta gefen ido take kallonsu. Jitai bazata iya barmata ba, dan haka ta miƙe tasha gaban Fadwa dake gab da fita…
Cike da salon ƙularwa fuskarta ƙawace da murmushi take kallon Fadwa da mamakin yanda ta tareta ya sata diriricewa, to amma a gareta hakan zai zama riba tunda tasan Shareff bazai ragawa Anaam ɗin ba.
Anaam data gama fahimtarta ta ƙara sakin murmushi da naɗe hannayenta a ƙirji “Amaryar data kai mace ba’a samunta ta sauƙi ai, saboda tsadarta tafi tsada tsada madam, ki rubuta ki aje a duk lokacin dana sallama wlhy sai kin zama ƴar kallo a wajen mijin naki, idan kin isa mu ƙulla”. Ta ƙare maganar ƙasa-ƙasa tana kashema Fadwa ido.
Yawu mai kauri Fadwa ta haɗiya saboda ganin alwashi cikin idanun Anaam, ta saci kallon gefen Shareff sai taga su yake kallo. Murmushi ta saki cike da kirsa. “Ayya Anaam miya faru da wannan magana haka?, ai shi ɗin mijinmu ne mu duka ba nawa kawaiba, kinga kuwa basai mun ƙulla wata yarjejeniya a kansa ba, kuma indai nice wlhy nama ƙara muku sati biyu akan ɗayan”.
Anaam dako kallon inda Shareff yake batayi ta saki wata siririyar dariya data ƙona ran Fadwa da tafa hannayenta. “Woow! kai kai kai Uwargida abun birgewa. Muna godiya da wannan ƙyauta mai tsada”. Sai kuma ta kashe mata ido da maida muryarta can ƙasa kamar mai raɗa. “Karki damu kinada kaso, za’a samo miki tukuycin baby da zaina tayaki hira tunda kin hana masa zuwan abokin wasansa yayansa duniya”.
Duk da a hankali sosai Anaam ta faɗi furucin ƙarshe kaɗan ya rage zuciyar Fadwa ta wantsalo waje. “Sautin bai miki ba na ƙara n…..” Da sauri Fadwa ta fice cikin sassarfa daga falon, wani irin zufa na tsatstsafowa ta illahirin ƙofofin jikinta har tana kifawa kamar zata faɗi. Anaam ta danne dariyarta da ƙyar, da binta da kallo harta fice. Sai da Fadwan ta fita da kusan mintuna biyu sannan tabi bayanta zuciyarta fes tunda ta rama.
Da kallo ya bita ta gefen ido, ya jinjina kansa da sakin murmushi dan duk abinda ya faru a tsakaninsu yaji. Hatta maganar farko da Fadwa tai a dining, yayi shirune dama dan yaga wane mataki ita kuma Anaam ɗin zata ɗauka. Wato Fadwa a gabansa ne take nuna ita ɗin mutuniyar kirkice, ita kuma Anaam bata iya ɓoye-ɓoye ba sai take nuna nata babu wani munafurci a ciki. idan ya auna da kallonsa da Fadwa takeyi tana magana cikin canja yanayi danta kunnasa ne ya hau kan Anaam kenan kamar yanda taga yanayi a kwana biyun nan idan tai makirci. Lallai mata sai ka barsu, idan kai wasa sai su kaika wuta da sheɗana, dolene ya nutsu wajen ƙara fahimtar halayen kowacce kuwa.
Duk yanda yaso cigaba dayin kallon kasa hakan yay, dan kalaman Anaam babu abinda suke sai tsikarar zuciyarsa, dole ya miƙe ya kashe komai ya shiga bedroom ɗinsa. Sabon shirin barci ya sabunta da mulke jikinsa da turarurrukansa masu ƙamshi har kusan kala biyar, haka kawai yake jin saka ɗaya bai gamsar da shi ba. Bakinsa kansa yasha Mouth fresheners kusan kala uku, ya sake duban kansa a mirror ya saki murmushi da kashema kansa ido ɗaya… “Dole ne yau a tabbatar min da wannan tsadar da tafi tsadar tsada my girl”.
     
       ★Ransa fes ya fito hanunsa ɗauke da fresh milk. Kansa tsaye sashen Anaam ɗin ya nufa, baiyi mamakin rashin ganinta a falo ba. Sai da ya fara shiga kitchen ya ɗauka ruwa da glass cup sannan ya nufi bedroom ɗinta bayan ya kashe komai ya rufe ko ina.
     Tunda ta fito a sashensa da murmushi ta iso nata sashen, ya kuma gagara barin fuskarta har tai shirin barci dan dama tayi wankanta, brush kawai tayi ta haye gado batare data ɗaura jacket ɗin rigar barcin ba a kan ta cikin data kasance ƴar fingila iyakar cinyoyinta, sannan hanunta siriri ne. Rufda ciki ta kwanta da jan bargo ta lulluɓe har kanta tana cigaba da sakin murmushi………✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button