BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

      Sunbar airport ɗin kaɗan kiran Momy ya shigo masa. Idonsa ya ɗan rumtse kafin ya kai hannu ya ɗaga. “Kana ina?”. Ta faɗa tunkan yay sallama. “Mommy can gidan mana”. Ya faɗa a tausashe. “What! Al-Mustapha kana da hankali kuwa? Da wannan yarinyar kake nufin kaje?! To ina mai tabbatar maka maza ka sakota a napep ta dawo gidan ko ranka ya ɓaci bansan iskanci”. Ɗan jimm yay na sakanni biyu. Sai kuma ya ɗan saki murmushi. “Okay Mommy ba damuwa”. Numfashi ta sauke a hankali da faɗin, “Yauwa ko kaifa. Bana son wannan karon naji abinda bai minba kaga dai yanzu akwai banbanci da da. Ka kula ka bita a yanda take so dan ALLAH”. Nanma murmushin kawai yayi batare da yace komai ba, sai dai har cikin kunnenta tajisa dan haka tai masa sallama ta katse kiran. Wayar ya ajiye shima ya cigaba da tuƙinsa a nutse har suka iso.
       Da sauri ta waro idanu waje ganin inda suka zo, ta dubesa idanunta nayin ƙwal-ƙwal na tahowar kuka. “Yaya! nidai ka kaini gida bazanje wannan gidan ba”.
       Harara ya zuba mata, batare da yace komai ba yay parking a ƙofar gate ɗin. Sanin abinda zatai nan gaba shine roƙonsa ko guduwa ya sashi dubanta, “Haɗiyemin wannan silly hawayen banzan kafin nai miki dukan mutuwa a wajen nan”.
     Babu wasa a zancen nashi, dan haka ta haɗiye sautin kukan sai dai hawayen kam sun kasa tsayawa. Wayarsa data fara tsuwwa ya ɗauka, ganin mai kiran ya sashi ɗagawa da kaita kunne. “Ina waje”. Kawai ya faɗa tare da yanke wayar. Ko mintuna biyar basu gama cikaba Fadwa ta fito cikin yauƙi da yanga. Wando da riga ne a jikinta parkistan ƙirar Egypt. Sosai kalar kayan ya fidda mata ƙyawunta. Musamman yanda ƙaton gilashin data saka ya kusan mamaye rabin fuskar tata da haska farar fatarta. A hankali Anam taja guntun tsoki da ɗan laɓe baki. Sarai Shareff ya jita, sai dai komai baice mataba har Fadwa takusa ƙarasowa garesu.
     “Fita ki koma baya”.
Yanda yay maganar a dake batare da ya kalleta ba ya sata juyowa ta kallesa. “Are you daft?!”.
     Maganar tasa tayi dai-dai da isowar Fadwa jikin motar tana ƙoƙarin buɗe gaban ta shiga dan batai zaton ganinsa da wani ba ma balle wata.  Da sauri Fadwa taja baya saboda yanda Anam ta buɗe murfin a fusace. Saura kaɗan ta bugeta ma ALLAH dai ya taƙaita abun. Ko kallon inda take Anam bataiba tai ƙoƙarin barin wajen maimakon baya daya bata umarnin komawa. Sai dai kuma Fadwa tasha gabanta da sauri….
     “K! K! Dakata k! Ƴar uban wacece a motar mijina?”.
     Ba kowacce hausa Anam ke ganewa ba, dan haka a yanzun ma bata fahimci furucin farko ba hakan yasata kasa haɗa ma’anarsa dana ƙarshe da ƙyau. Amma a yanda Fadwa tai maganar ta tabbata ba’abune mai ƙyau ta faɗa ba. Wani banzan kallo ta watsa mata kawai dajan tsaki ta ratseta zata sake barin wajen. Hannu Fadwa tasa ta fisgota ta maidota baya a wani irin fusace, kasancewarta mutum mai saurin zuciya da son yanke hukunci sai kawai ta ɗaga hannu da nufin zabgama Anam ɗin mari………✍

Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja. Hajiya Fadwa daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi. To ku garzayo cikin tafiyar zafafa biyar domin ganin yaya wannan wasan zai kasance????. Dan tabbas akwai cakwakiya, idan nace cakwakiya ina nufin cakwakiya ƴar gaske. Yanda Fadwa take a tsaye Anam ɗin ma ba kanwar lasa bace. Littafine daya ƙunshi abubuwa da yawa. Rikicin zumunci, makirci, son zuciya, kishi, cin amana, kai harma da SARAN ƁOYE. Wasa ne kashi-kashi, dake da players daban-daban. Karku bari ayi babu ku, zafafa dabanne masoya, musamman na wannan ƙarnin da zasu zo muku a cikin zafi na musamman. Karna cikaku ku dai ku garzayo kawai.

_Dan girman ALLAH, dan girman ALLAH, dan girman ALLAH kizo ki mallaki halak ɗinki, idan baki da kuɗin saye ko baki da ra'ayin saye basai kin damu da karantawa ba dan baya cikin wajib. Mai tunanin siya ko mana mugunta ki fitar kiji tsoran ALLAH karki cutar damu bamu cutar dake ba, idan kinyi shirin haka da gayya ko izgilanci a garemu muna roƙon UBANGIJIN al'arshi mai rahama mai jin ƙai, mai sanya alkairi a zukatan dake ƙudurta sharri ya shiryeki ya ganar dake gaskiya ya kuma bamu kariya daga abinda zuciyarki ke ƙulla miki????????????._

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!????????????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*     

Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai. Ya rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al’ummarka. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar da ni da su. ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai. Ka ƙara mana lafiya da zaman lafiya a wannan ƙasa. Ka azurtamu da shugaba na gari mafi alkairi a garemu da ƙasarmu

06

………..Kafin ta sauke nata data ɗaga Anam ta sauke mata lafiyayyen mari daya saka Shareff ɗago idanu a karon farko ya kallesu. Fadwa tai saurin dafe kuncinta tana kallon Anam dake jifanta da wani shegen kallo na gargaɗi tana huci. Mamaki, al’ajab da tsantsar ruɗanin daya haɗu da azabar zafin mari take kallonta ƴar ficit a gabanta. Ba ita kaɗai ba, hatta Shareff wutar kansa ta ɗauke dan mamakinta da ƙarfin hali dama tsaurin idanu.
      A fusace Fadwa ta kai hannu da nufin shaƙota. Wani shegen kallo ta sake watsa mata da riƙe ƙugu, babu alamar tsoro kona sisi a idanunta cikin zafin rai da harshen nasara ta nunata da yatsa.
       “Niba takalmi bace, ballantana ƙafafunki suyi tunanin takawa a duk sanda sukaga dama. Respect your self ok? Shashasha”. Ta ƙare faɗa tana barin wajen cikin takun izza…
    Tamkar gunkin da aka dasa haka Fadwa ta kasance tsaye tana binta da kallo, dan da gaske wutar kanta ce ta ɗauke baki ɗaya har tama rasa hukuncin da zatai mata. Kusan taku biyar da barin Anam wajen Fadwa ta dawo hankalinta, zabura tayi zata bita  Shareff da mamaki ya hanashi motsin shima ya buɗe motar ya fito, cikin bada umarni yace, “Ƙyaleta”. Juyowa tai tana kallonsa idonta jajur, hakama fuskarta tayi ɗan ja abinka da fara. Tana bala’in jin shakkarsa, amma sai ta kasa daurewa cikin ɗaci tace, “Soulmate! Na ƙyaletafa kace?”.
      Kansa ya jinjina mata cikin ɗan lumshe idanu da jingina da motar, sosai take masa kallon tunzura, amma tai ƙoƙarin haɗiye dukkan abinda ke bakinta. Batare da tace komai ba ta juya da nufin komawa gida. Hanunta yay saurin riƙowa, tai ƙoƙarin fisgewa amma ya hanata damar hakan. A jikin mota ya jinginata idanunsa akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da hawaye ke sauka. Ba abinda Anam tai mata bane ya sata kuka, hanata ɗaukar matakin da yayi ne yafi ƙona mata rai.
    Handkerchief ya mika mata, idanunsa na mata kallo cikin lallashi “Nace miki bazan ɗauka mataki bane?”. Idanunta dake ƙara cikowa da hawaye ta ɗago ta kallesa. Ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. “Bana son ɗaukar mataki cikin fushi akan kowanne irin abu ki kiyaye wannan. Shiga muje”.
         Ƙara ƙuna zuciyarta tayi da kalamansa, kamar tace bazataje ba ta fasa sai kuma ta danne saboda shawaran su Mamanta akan ta danne komai dazai mata a yanzu har ta shiga gidansa. Sannan koba komai tana son sanin wacece yarinyar nan, amma cikin fushi tasan bazai sanar mata ba ɗin. Umarninsa tabi ta buɗe motar ta shiga, idanunsa da suka kaɗa sukai jaa ya ɗan bita da su, sai kuma ya janye dayima motar key yay reverse.
Kasancewar anguwace da kakan daɗe bakaga abin hawaba yasa har suka cimmata. Tafiya take tana sharar hawaye. Duk da horn da aketa faman mata baisa ta juya ba. Ransa ya ƙara ɓaci, a fusace yay parking tare da fitowa yasha gabanta, kanta ta ɗauke gefe kamar bata gansa ba zata raɓashi ta wuce.
      Hannayensa ya tura cikin aljihun wandon Jeans ɗinsa. “Idan kika ƙara step ɗaya a wajen nan sai jikinki ya faɗa miki!”. Cak ta tsaya iya taku biyun da tai, wasu irin hawaye masu zafi suka ƙara ciko mata idanu. Motar ya nufa idanunsa tamkar zasuyi aman wuta. Duka kawai take tsoro, dan haka ta share hawayenta dan bata bukatar da ga shi har budurwar tasa su gani, motar ta buɗe ta shiga. Yay ƙaramar ƙwafa da buɗewa shima ya shiga, ya fisgeta da gudu zuwa kan titi batare daya ƙara kallon kowaccensu ba. Sunyi tafiya kusan na minti biyar dai-dai gidan wani abinci Fadwa ta dubesa, “Please Soulmate banyi breakfast ba”. Shiru yay kamar bazai tanka ba, bai kuma da alamar tsayawa, itama kasa ƙara cemasa komai tayi saboda yanda ya haɗe fuska matuka. Harma ta haƙura sai taga ya gangara gefen titi dai-dai wani restaurant da bama tasan da shi ba. Buɗe motar yay ya fita batare da yace musu komaiba, itama Fadwa sai ta fita tana harar Anam data maida hankali ga latsa waya kamar bata a motar.
Suna ƙoƙarin barin wajen yakai dubansa gareta, dai-dai ta ɗago itama suka haɗa ido. Fuska ta sake ɗaurewa tamkar yanda shima ya sake tsuke tasa. A yanayin fusata ta janye nata da ɗan kallar gefen Fadwa. Har suna gab da shiga wajen bata da niyyar fitowa ita, sai da suka shige da kusan minti biyu sannan ta fito dan haka kawai zuciyarta ta raya mata ta bisu koba komai zata ragema Fadwa jin daɗi ai.
Cikin taku a hankali ta shigo wajen, dai-dai yana magana waiter idonsa ya sauka a kanta harta ƙaraso inda suke, kujera taja ta zauna. Idanun nasa ya ɗauke gefe, tare da yin kamar bai ganta ba ya ɗauka wayarsa ya hau dannawa. Kallonsa ta ɗanyi tana tura baki, batare data kalli inda Fadwa take ba itama ta hau latsa tata wayar cikin kwaikwayon salon da yayi.
      Ta gefen ido ya dubeta, numfashi ya ɗan ja a fisge tare da maida hankalinsa ga wayarsa a zuciyarsa yace (azababbiyar yarinya).
      Kamar tasan mi yake ayyanawar ta ƙara ɗaure fuska tana hararsa shi da Fadwa da hankalinta itama gaba ɗaya ke kan wayarta da alama akwai abinda takeyi mai muhimmanci. Isowar waiter ɗauke da tray ya sakasu ɗagowa su duka. Har waiter ɗin ta gama shirya musu abincin tabar wajen idon Anam nakan nasa. Ya ɗau cokali zai fara ci tace, “ALLAH Yaya abincinka yafi nawa nama”.
       Duk yanda yaso basar da ita ya kasa. Ya kafeta da idanu kamar mai harara “Kuɗinki ko kuɗina?”.
  Fuska ta taɓe “Naka ne. Amma kuma ai ina cikin masu cin gadonka idan ka mutu, kaga banda laifi idan nayi magana”.
Wani wawan tsaki Fadwa ta saki tsanar Anam na ƙara faɗi a ranta.
“Shiga shanu ba sharo”Anam ta fada cikin sakin siririyar dariyar data sake kular da Fadwa (Sharo ba shanu bahaushiyar malaysia????????)
     Tattausan murmushi kawai ya saki a karo na farko da cigaba da cin abincinsa. (Batun yanzuba ya fahimci bata da riƙo. Sai dai ya tabbatar wannan sauyawar tata lokaci guda ba’a banzaba akwai abinda ke ranta).
Fadwa ta kafesa da kallon mamaki, sai dai shi yaƙi yarda ya kalla inda take. Saurayin dake kusa da su da drama ɗin tasu taja hankalinsa tun ɗazun yay ƴar dariya idonsa akan Anam shi kuma. Juyawa tai taɗan kallesa. Ganin shima ita yake kallo ta ɗauke kanta tana harararsa, abincin Shareff ta ƙara kallo, burinta kawai ta yanda naman kan plate ɗin nasa zai dawo nata, ganin hankalinsa nakan wayarsa tace. “Yaya!”.
      “Uhhyim!”.
Ya amsata batare da ya daina abinda yake ba. “Na faɗa maka wani abu?”.
     “Uhhm”
Nanma ya sake faɗa batare daya ɗago ɗinba. Ɗan shiru tai tana nazari. Bayan kusan sakan talatin ta dubesa sai kuma ta ɗan harari Fadwa ta maida dubanta ga ƙofar shigowa. “Lah Yaya wannan ba Aunty bace?”.
     Kamar bazai ɗagoba sai kuma ya ɗago ɗin jin kamar tayi maganar a serious. Kallonsa ya kai ga ƙofar duk da bai san wace aunty take magana ba akai kamar yanda itama Fadwa da gaba ɗaya takaici ya turniƙe takai kallonta wajen. Wuff ta kwashi kusan rabin naman daya tsole mata ido ta maida a plate ɗinta. Lokacin da yake juyowa fuska a tsuke harta miƙe a table ɗin ta koma na kusa da su da guy ɗin da duk hankalinsa ke kansu yake.
     Plate ɗin abincin nasa ya kalla sai kuma ya kalleta. Kauda kansa yay gefe saboda murmushin dake neman suɓuce masa. Ya ɗan jinjina kansa dayin ƙwafa. Fadwa dai kallonsa kawai take mamakin tsaurin idon yarinyar nan na nema shaƙureta.
       Saurayin da gaba ɗaya komai na Anam ya gama tafiya da imaninsa shima fuskarsa ɗauke da mayataccen murmushi yake kallonta. Ya sake sakin murmushi ganin duk laumar abincin da zata kai sai da yankan nama. Cikin murya ƙasa-ƙasa yanda ita kaɗai zataji yace, “In ƙara siya miki wani gimbiya?”.
        Kai ta ɗago ta kallesa, sai kuma ta saci kallon Shareff. Ido suka haɗa, ya zuba mata hararar da hanjin cikinta suka kaɗa, amma saita fuske cikin dakewa. Ƙasa tai da idanunta Tana ƙoƙarin sake kai abincin bakinta kamar bata gansa ba, saurayin ya sake ɗan matsota cikin ranƙwafowa har tana jin hucin numfashinsa yace, “Queen Please”.
      Wani irin cije baki Shareff yayi da ƙarfi, sai kuma ya miƙe gaba ɗayansa. Gabansu ya iso ya ɗauka wayarta da saurayin ke ƙoƙarin ɗauka. A kausashe yace, “Tashi muje”.
     Kamar bazata ɗago ba sai kuma dai ta ɗago tana kallonsa. “Ni banfa gama ba, ba yanzu muka fara ba, ga budurwarka ma bataci nata ba”.
    “I will slap you in baki tashi ba”.
Miƙewar tayi fuska a kumbure. Ya nuna mata hanyar waje, ko kallon saurayin baiyi ba yayma waiter nuni tazo. Kuɗinsu ya bata, tareda wasu yace ta masa takeaway na naman rago. Fadwa da ko lauma ɗaya bataiba dama ta miƙe tsam da wayarta a hannu ta fice, bayansu yabi, sai dai kafin ya fito Fadwa ta tsaida napep ta shige abunta, Anam ko jikin mota ya sameta ta haɗe fuska tamau. komai baice mata ba ya buɗe ya shiga, a dai-dai nan aka kawo masa takeaway ɗin da ya saka akayo. Jin ya kunna motar tai saurin buɗewa itama ta shiga. Sai lokacin ya lura babu Fadwa, motar ya sake buɗewa ya fito yana dube-dube.
Wata shaƙiyyar dariya Anam ta ƙyalƙyale da ita harda kwanciya, tana ganin zai dawo ta haɗiye kayarta da gyara zama ta fuske…
A dake yace, “Malama dawo nan”.
Ido ta ɗan waro tamkar bata san mike faruwa ba. “Yaya Auntyn kuma fa, ba fitsari taje bane?”.
Kallon banzar daya watso mata ya sata buɗe murfin ta fita tana danne dariya da ƙyar, ƙasa-ƙasa take faɗin, “Ai daga yau daga kai har ita kun shiga uku da ni. Sai tasan ita ƙaramar ƴar iska ce”……

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button