BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

      Batafi awa uku da fita ba sai gata ta dawo, ta kara wani irin ƙyau da kwarjini tabbacin taci gyara tako ina. Dan babu abinda fuskarta keyi sai shining da glowing, ga wani uban ƙamshi mai saka nutsuwar mai shaƙa. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufi ƙyaƙyƙyawan dattijon dake tsananin kama da ita dan shima black beauty ɗinne, amma kasancewar akwai jin daɗin rayuwa baka ganin komai tare da shi sai ƙwarjini da ƙyawun haiba. Ga baƙin sajen fuskarsa daya ƙara ƙawata ƙyawun nasa. Shima dai bashi da wani jiki, dan komai na Anam bashi da maraba da nashi, hakan na nufin dai kamaninta ɗaya da mahaifinta.
      Zuwa tai ta rungumesa ta gefe tana dariyar farin cikin ganinsa. Shima fuskar tasa da murmushi ya riƙo hanunta cikin nasa. “Uhhm Mamana irin wannan ƙamshi haka kamar amarya”. Fuskarta ta ɓoye a kafaɗarsa tana dariya. “Nidai Abie ba wani amarya”. Dariya kawai yayi baice komai ba. A haka Mamie ta fito daga kitchen ta samesu. Fuskarta ɗauke da murmushi take kallon mijin nata abin sonta da ƴar tasu tilo ɗaya a duniya. Anam ta zame veil ɗin kanta tana nunama iyayen nata kanta daya sha gyara masha ALLAH, sai sheƙi yake da ƙamshi gashi da tsaho sosai. Gaba ɗaya kamaninta irin na Abie, gashin kai da gira zuwa gashi ido ne kawai irin na Mamie, sai ko maganarsu dake kama itama.
    Sosai suka shiga yaba ƙyawun da gyaran nata yayi, cikin tsokana Abie ke faɗin, “Mamana kin zama kamar wata amarya da gaske, kodai kawai idan munje na aurar dake ma?”.
    Idanu tai mugun zarowa, sai kuma ta kwaɓe fuska har hawaye na cikon mata ido. Lips ɗinta sai rawa suke tama rasa mizatace. Dariya Mamie da Abie suka shiga yimata, hakan yasata tashi da gudu ta haura sama. “Kin gani kin kunnata”.
     “Na kunnata ko ka kunna abarka”.
Cewar Mamie tana murmushi. “To aini abin na damuna, idan na tuna wataran aure zatai ta barmu hankalina na matuƙar tashi, gashi shekaru sunyi nisa, kamata yay ma data gama saves ɗin nan kawai a wuce wajen Humairah”.
     Ajiyar zuciya mai nauyi Mamie ta sauke. Murya a raunane tace, “Hakane ya dace, sai dai kuma a kullum cikin korar samarin take ai taƙi bama kowa dama anan ɗin balle Nigeria. A kullum kallon kanta take a yarinya”.
     “To ai yarinyarce, duka yaushe kika haifamin ita. Ni badan auren ya zama doleba dana bar abuta naita kallo kawai”.
      Sosai Mamie ke dariya, cikin riƙe baki tace, “Lallai ashe mu iyayenmu basa sammu kenan da aka ɗakko aka baku. Lallai ashe lokacin auren munada kallo kenan dan za’a sha show rabuwar ƴa da uba”.
     “A zakusha kam. Dan mijin nan zai sha gargaɗi, shiyyasa nafi son ma ta auri ɗan Nigeria dan ƙasar nan ta isheni haka”.
        “To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Ya kawo nagari”.
  Da amin Abie ya amsa cikin jimami da damuwar rabuwa da tilon ƴarsa.

Washe gari kamar yanda Mamie ta faɗa hakance ta kasance. Dan kuwa dai Abie da Anam sun wuce ƙasar haihuwarsu Nigeria. Tasha kukan rabuwa da Mamie duk da tasan bazatai shekaran Mamie bataje ba tunda ita sunce bazata zo ba har saita kammala. A jirgi barci ta dinga ramuwa wanda ta gagara yi a daren jiya saboda alhinin yin nisa da iyayenta datai matuƙar shaƙuwa da su take mu’amula da su tamkar ƙawayenta. Sune abokan shawararta, sune abokan kukanta, sune abokan dariyarta, sune abokan rayuwarta. Bata da kamarsu dan su tafi sani fiye da kowa a duniya………..✍

Hummm tofa masu karatu, ni kaina wannan littafi banma san mizance ba. Kawai kumuje zuwa muji yaya za’a ƙare da Anam ƴar Malaysia mai gudun Nigeria. (Kai nimafa da za’a kaini Malaysia ɗin nan ba dawowa 9ja ɗin nan zanso yiba. Idan baku yarda ba ku haɗan kuɗin jirgi kuga aiki????????????????‍????).

Ku kasance da Zafafa biyar dan da gaske wannan karon tafiyar tasu ta musamman ce insha ALLAH. Kowanne littafi yazo muku da salonsa na dabban daya dace da buƙatar ku. Sai da ku Zafafa biyar ke amsa sunan Zafafa biyar, dan haka kuɗin na musamman ne a garemu masoya. Idan muka ce na musamman da gaske muna nufin na musamman????????????????????????

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107

KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!????????????????????????

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

03

……….Tuni sun tattare kansu a sashen aunty amarya idan ka cire ƴan manya-manyan yaran gidan samari da basu gama dawowa da ga wajen aiki ba da kuma masu shiga school lectures ɗin yamma. Zagaye suke da Anam suna kwasar dariyar hausarta da bata nuna da ƙyau ba. Dan cike take gwamutse da yaren malay da turanci, wai a hakanma Abie na matuƙar ƙoƙarin mata hausar ne shi da aunty Mimi dan Mamie ma ba wani iyawa tai sosai ba harma gara Anam ɗin, tunda dama acan itama ta tashi, ko Nigeria tazo tafi yin turanci da jama’ar gidan. Aysha dake naniƙe da Anam ɗin da suke sa’annin juna dan dama idan tazo bata da ƙawar data wuceta a Nigeria, cike da kulawa take tambayarta dalilin matsar ciki da take famanyi.
       A yatsine Anam ta sanar mata tana jin yunwa ne, dan ta kasa cin duk abincin da aka shirya musu a gidan. Dama can idan sunzo Mamie ce ke musu girki shiyyasa Anam bata da matsala tunda abinda ta saba ci ne, a yanzu ko babu Mamie dole sai abincin Nigeria da har yanzu ta kasa iya ci, ƴan abubuwan da take iya cin ƙalilanne kuma babu su.
      Idanu Aysha ta ɗan waro, cikin harshen turanci take cemata miyasa zata zauna da yunwa bayan abinci da akai domin su tunda sun iske tarin kwanika a sashen Daddy lokacin da sukaje gaida Abie. Sunada tabbacin kuma an shiryasune dan zuwan su Anam ɗin. Fuska a marairaice ta sanarma Ayshan ita bata iyacin duk abincin ba ai. Ba Aysha kaɗaiba duk yaran sai da suka dara, dan sosai ragwantakar Anam ke basu dariya, kodan tana ganinta da ƙaramin jiki ƴar ficika da ita yasa a kullum bata sanin ta girma? Sosai Aysha ta fita girman jiki, sai ma ta saɓeta ta goya dan ita ta kwaso tsayi da garin jikin Mommy mahaifiyarsu.
    Sake ɓata fuska Anam tai kamarzatai kuka, sai faman matse ciki take da cizar lips dan da gaske yunwar takeji, shi kansa Abie yana canne amma hankalinsa na kanta dan yasan bazata iyacin kowanne abinciba da ya gani an tara masa.
      “Am so sorry sweetheart. Kar kiyi kuka faɗi abinda kike so sai a samo miki, ko a kira Yaya ya sayo miki tunda shi yasan inda yake samo abincin naku, dan shima dai ya jima yana wahala kafin ya saba da abincin Nigeria, ko yanzu ma ba komai yake iya ci ba”.
      Fahintar wa Aysha ke nufin za’ama magana ya samo mata abinci ya sakata girgiza kanta, a langwaɓe ta kamo hanun Ayshan cikin nata. “No don’t worry rakani wajen Abie na nidai kawai”.
    Batama bari Aysha tace wani abuba ta miƙe har lokacin hanunsu cikin na juna, ɗayan hanunta kuma nakan cikinta. Wando da rigane a jikinta marasa nauyi, wandon irin mai faɗin nan sosai da ƴan Nigeria ke kira a fantama????, sai fingilar top da tabi jikinta ɗas kamar dan ita aka halicceta, sai siririn veil data sakaya gashinta a ciki sai dai hakan bai hanashi bayyana ta gaba ba saboda veil ɗin daya zama baya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button