BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

        Shawarar fita neman abinci ya yanke a ransa, sai dai kuma wata zuciya ta ƙwaɓesa dayin hakan dan ba mutuncinsa bane yana da mata har biyu ace yana fita yawon gidajen abinci siyowa. Sai dai kuma ko yunwa zata hakalashi yayi alƙawarin a yanzu dai bazaici abincin na Fadwa ba. Sashensa ya koma, ya zube a kujera hanunsa dafe da kansa. Kusan mintuna uku ya samu zaune shiru, sai da ya tabbatar zuciyarsa ta ɗan nutsu sannan ya ɗauka waya yay kiran Anaam.
      Kammala wankin toilet ɗinta kenan kiran nasa ya shigo mata. Batai saving number ɗin ba duk da ranar ya kirata da ita. Tai ɗan jimm kafin ta ɗaga da tunanin wanene. Shiru babu wanda keda alamar magana a tsakanin ita da shi. Ganin haka a ɗan harzuƙe tace, “Nikam idan mai kiran nan baida abinyi ni ina da”.
       Guntun murmushi yayi. Har cikin rai yake jinjina tsiwar yarinyar nan, ita kowa bata jin shakka na waya ma da batasan ko wanene ba bazata raga masa ba. Ya ɗan girgiza kansa da furzar da numfashi. “Ki samo min tea da wani abu ki kawo min”.
   Kafin ta samu damar tofa tata ya yanke wayar. Tai takwa-takwa na takaici sai kuma ta tsuke baki da buge wayar………✍

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

BABU SO????????AREWABOOKS

https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718

51

………Kwance ta kai tana faman tuttura lips gaba, a zuciyarya kam babu abinda take sai masifa, sai dai babu damar yi a fili. Tashi tai zaune zaram kamar wadda aka tsikara tana kallonsa, ganin ya koma ya zauna gaban laptop ɗinsa.
     “Yaya MM?”.
Shiru ya mata yaƙi ya amsawa, amma tsabar bazata iya haƙuri ba saita cigaba da maganarta kamar sharetan da yay bai zafeta ba.
           “Amma dai can ɗakin zaka koma ka kwana kamar ranar idan ka kammala aikin ko?”.
      Banza yay mata nanma, takaicinta ya bayyana har tana jin tuƙuƙimsa a maƙoshi, harara ta dallama bayansa, cikin jin zafi ta fara ɗaukar pillows ɗin gadon ɗaya bayan ɗaya ta jera a tsakkiyar gadon tun daga farko har ƙarshe tana muy-muy da baki alamar magana take. Ƙarshen gadon ta koma da salon kwanciyar kai da ƙafa ta kwanta badan zuciyarta ta bata nutsuwar haƙurin sake kwanciya ɗaki ɗaya, gado ɗaya da shi ba. Dan tayi alƙawarin kafin cikar wata ukunnan bazata taɓa bari ya samu nasara a kanta ba.
    Duk abinda take yana jin motse-motsenta sai dai bai juyi ba, aikinsa kawai yake badan yana fahimtar wasu abubuwan ba. Bayan shuɗewar kusan mintuna arba’in da biyar yaji shiru ta daina sukur-sukur da motse-motsen da takeyi, kaɗan ya juyo ya kalleta, a can ƙarshen gado take ƙudindine da bargo ta juya masa baya. Ya maida kallonsa akan pillows ɗin data jera, kansa ya girgiza kaɗan wani ɗan guntun murmushi na suɓuce masa. Hankalimsa ya maida ga aikinsa, wanda ya sake jansa kusan awa guda, ganin two ta kusa ya ga hamma yanata jerawa ya sashi tattara komai ya ajiye. Alwala yayo, ya shimfiɗa abin salla, sallar nafila ya gabatar raka’a biyu, yay addu’oi dan barci sai faman rinjayar idonsa yakeyi. Bai cire shingen datai musu ba yay kwanciyarsa bayan yayi addu’oi. Babu jimawa barci yay awan gaba da shi shima.
     Duk da ta rigashi kwanciya shine ya rigata farkawa, ya yunƙura da ƙyar ya tashi bayan karanta addu’ar barci, shanyayyun idanunsa da har yanzu barci ke cike a cikinsu ya zuba mata ta ɗan hasken lamp dake a ɗakin kaɗai. Yanzu kam ta juyo fuskarta, sai dai tana a inda take kwance tun jiya. Sai da yayo alwala sannan ya tasheta, a ranta ALLAH-ALLAH take ya fice ta sama ƙofarta key, sai da yaga ta shiga toilet sannan ya fice zuwa sashen Fadwa itama ya tashesu. Koda ta fito kai tsaye ƙofar ta nufa, amma wayam babu keys ɗin alamar ya zare. Ta dallama ƙofar harara da murguɗa baki.
       Sai da gari ya ɗanyi sha ya shigo, har sannan tana zaune tana azkar. Batare da ta yarda ta kallesa ba tace masa ina kwana. A taƙaice ya amsa yana kaiwa kwance dan barci ne fal idanunsa. Jin ya fara sauke numfashi ta ɗan juya ta kallesa, ya juya mata baya, amma ta fahimci barci ne ya ɗauke sa. Itama dai ƙarasa azkar ɗin tai ta koma ta kwanta tunda ba wani aikine da ita ba…..

       ★★★★

  Tsabar yanda ta kwana da abubuwa masu yawan gaske a ranta tana idar da salla sashen Gwaggo ta nufa. Burinta kafin su Daddy daga massallaci su shigo ta shige, dan ita yanzu ko ɗakinsa bata zuwa, shi kuma yaƙi ce mata komai akan hakan. Gwaggo na zaune tana lazimi Mommy ta shigo, kallonta kawai take baki a sage, sai dai kuma batai mamaki ba musamman akan sanin halin rashin haƙuri irin nata. Mommy ta gaisheta kamar yanda ta saba, damuwa ƙarara akan fuskarta.
        “Wai Nafisa kuwa anya hankalinki na jikinki? Wace irin rayuwace wannan duk kin firgita kanki akan abinda bai taka kara ya karya ba. Da alama yau ko barcin kirki ma bakiyi ba ko?”.
    “Humm Gwaggo ina naga ta barci nikam, kema kin san babu wani barci dazan iya a wannan halin. Ki duba fa kiga Shareff ya ɗauke ƙafa gaba ɗaya a gidan nan tamkar ya manta dani a raye, ko’a waya baya kirana tumma yanzu kenan za’a rabani da yarona. Maheer ma yaƙi zuwa duk da shi nasa bai cika damuna ba nasan fushin banza da wofi ya sakama ransa bayan ni gata naima rayuwarsa. Gwaggo taya zanyi barci a wannan yanayin to? Na kasa gane kan Shareff sam. Son yarinyar nan yake da yake gudun haɗuwarmu ko yaya ne?”.
        Ƴar dariya Gwaggo tai. “Banda abin Nafisa halin namiji kuma kika manta! Shi yanzu Mustapha a wannan gaɓar bake kaɗai ba kowama zai iya rasa gane kansa ai…..”
    “Gwaggo to saboda mi? Ni wlhy kaina duk ya kulle”.
       “Uhhm haka dai, tunda kin ruɗa kanki ba dole kanki ya kulle ba. Kina tunanin duk ƙin da yakema yarinyar zai kawo ido ya saka mata ne a gidansa”.
    Kaɗan ya rage Mommy ta haɗiye harshenta. Cikin in ina da shiga ruɗani take magana. “Gwaggo wai kina nufin ya kwanta da yarinyar nan?”.
          “Har kuwa ki ganta da ciki nan da watanni kaɗan”.
“Aiki dana tsine masa”.
    “Ki tsine masa! Kinga Usman da Ai’sha sunci riba a kammu kenan. Ki kiyayi harshenki da ambaton tsinuwa ya ƴaƴanki saboda kawai ranki ya ɓaci. Ki koyi nutsuwa a duk lokacin da kikaci karo da abinda bai miki ba. Nafisa idan kikai sakaci k da kanki zaki tabbatar da nasarar maƙiyanki akan ƴaƴanki. Yanzu dakin kwantar da hankalinki tun bayan da akai rikicin farko akan auren nan da yanzu mun kai ga mafita. Mustapha da kike gani hatsabibin yaro ne mai shegen zurfin cikin tsiya da wayo. Gaggawa a al’amarinsa ba shi bane mafita, kuma tsananinki ba shi bane zaisa muci nasarar rabashi da yarinyar cikin sauƙi, musamman da matarsa dama ta kasance shashasha, dan nikam sai yanzu nake dana sanin yin wannan haɗin nasu”.
       Da mamaki Mommy tace, “Wani abun ya faru ne Gwaggo?”.
    “Nafisa ai shiyyasa nace ke ɗin ruɗaɗɗiyar mutum ce, yo banda haka halin Fadwa har wani ɓoyayye ne da zaki kasa ganewa. Duk wani baƙin halin Halima shine tare da ƴarta, kodan shi Mustaphan bamai yawan magana bane da kullum zai zauna faɗa miki matsalarta shiyyasa kike kasa fahimtar halinta?”
           “Gwaggo bawai ban fahimci wasu abubuwa bane, dan ni kaina yawan kirana da takeyi kullum tana kawomin ƙararsa ya mata kaza ya mata kaza yana cimun rai, sannan Aysha ta faɗa min ko abinci sai ta gadama takeyi a gidan sai dai mai-aiki, Shareff da ko’a gidan nan baicin abincin masu aiki”.
      “Humm zatayi abinda yafi haka ni na sani. Amma karki damu zamu fara gyara mata zama. Yanzu abinda nake so da ke ki sassautama zuciyarki komai, ki nunama su Muhammadu komai ya wuce kin ajiye makamanki, shima ɗin Mustapha ki kirashi a waya ya sameki ki nuna masa komai ya wuce. Mu kuma daga nan zamu fara namu yaƙin, badai wata uku shi Ibrahim ya bata ba, to duk yanda zamuyi sai munyi nanda wata ukun tabar gidan, babban fata na dai ace bai taɓata ba. Kai koda ya taɓatan ma ba komai”.
     “Gara dai karya taɓatan Gwaggo, danni bana fatan haɗa kowace sabga da Usman balle shegiyar matarsa”.
    Ƴar dariya kawai Gwaggo tayi da faɗin, “To ALLAH yasa haka. Yanzu dai inaga kima Sakina magana yau taje mana gidan taga yaya zaman nasu yake”.
      “Wannan shawaran yayi gwaggo, bara na sanar mata yanzun nan kuwa”.
     Daga haka suka cigaba da tattaunawa kuma har gari yay haske sannan Mommy ta koma sashenta zuciyarta na ɗan sassauta nauyin da tai kwana biyu. Masu aikinta ta bama umarnin haɗa abincin Daddy. Duk da sun ɗanji mamaki babu wanda yace komai tunda ba huruminsu bane, itako ta shige domin shiryawa tunda dama girkin tane…..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button