BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

★★★★
A kallo ɗaya zaka fahimci tsananin ɓacin ran dake tattare da ita. Tunda Gwaggo Halima ta kirata ta sanar mata abinda ya faru take kiran wayarsa amma yaƙi shiga. Kasa daurewa tai ta dawo falo tare da tura Hussaina gate zaman jiran shigowarsa. Mintuna goma kuwa ba’aiba cikakku da zaman Hussaina a gate sai ga motarsa ta shigo. Anam ce ta fara fitowa, Hussaina ta bita da kallo harta shige sashen Mom. Shima dake binta da kallon fitowa yay hanunsa ɗauke da ledar takeaway. Hussaina ta taso da sauri tana washe baki dai-dai yana sama motar lock da key ta waje.
“Yaya sannu da zuwa”.
Batare daya kalleta ba ya amsa mata. Idonta akan ledar hannunsa ta kuma faɗin, “Yaya Dama Mommy ce tace kaje tana nemanka”. A yanzu kam idanunsa ya ɗago yana kallonta. Sai dai baice komaiba tsahon sakkani ya janye. Ganin zai bar wajen takai hannu ga ledar. “Bara na ɗauka maka to”. Harararta yay, babu shiri taja baya tana tura baki gaba. Baibi takantaba ya nufi sashen Mom. Fawwaz kawai ya samu a falon zaune yana kallon cartoon. Yaron ya taso da gudu ya nufosa. Ledar ya ajiye gefe fuskarsa ɗauke da murmushi ya ɗagashi sama. “Oh my Friend ya kake?”.
“Lafiya lau Yayanmu. Good morning”.
Kumatunsa ya ɗan ja yana murmushi. Kafin ya ɗan kalla falon. “Gentlemen ina Mom ne?”.
“Tana ɗaki da aunty Rahma tazo”.
“Okay! To kace ina gaisheta.”
Kai ya jinjina masa. Sai kuma ya kai bakinsa kusa da kunnen Shareef ɗin, cikin raɗa yace, “Aunty Anam kuma yanzu ta dawo sai fushi takeyi”.
Idanu ya ɗan waro waje kamar yanda yaron yayi, “Haba dai?”.
“ALLAH kuwa. Ko kulani ma batayiba ina gaisheta da nuna mata Cartoon ɗina”. “Ayya am sorry my dear, maybe bata da lafiyane. Amsa wannan ka kai mata sai kuci tare”. Duk da ledar ta masa nauyi da ɗan gudunsa ya nufa ɗakin cike da murna yana ƙwala kiran “Aunty Anam! Aunty Anam!!”.
Idanu yaɗan lumshe a hankali da harɗe hannayensa duk biyu a ƙirji yana murmushi har yaron ya shige ciki. Haka yake shi mutum ne mai tsananin son yara. Bai shirya aure yanzu ba, amma saboda son da yakema yara ya sashi amsar tayin su Mommy dan ta matsu taga yay aure ya rasa dalili?.
Shigowarsa falon yasa Hussaina saurin yin shiru ta haɗiye sauran gulmar da take faɗama Mommy. Sai dai kuma yama riga yajita, kallon daya watsa mata yasa tai saurin barin falon tana tura baki gaba.
“Shareff kai dawa kaje gidan Halima!!”. Mommy ta faɗa a fusace tunkan yace mata komai. Ɗan jimm yayi na wasu sakanni, sai kuma ya ɗago yaɗan dubeta. “Mommy ni ban shiga gidanba ma balle naje da wani”. Harara ta watsa masa. “Wlhy Al-Mustapha ka kiyayeni a gidannan. Idan kace zamu saka ƙafar wando ɗaya da kai bazakajita da daɗi ba! Yanzu na kiraka nace kasata a napep ta dawo shine danka rainani ka ɗauketa kukaje wajen wadda ke shirin zama matarka har kana mata walaƙanci a gabanta ko?! Ita kuma shegiyan yarinyar mai kama da ifiritin aljanu haihuwar bakwaini tana mata rashin kunya, to idanma wani abune a ranta tun wuri ta fiddashi dan har abada bazan haɗa zuri’a da Usman ba, sunga ta rasa miji a can shine zasu kwasota su kawo nan talla……”. Murmushin yay da tasowa ya dawo kusa da ita, sai dai a ƙasan carpet ya zauna ya ɗora kansa jikin ƙafarta, hanunta ya riƙo cikin nasa murya a sanyaye, “First-luv Please cool down, yaronki bashi da wata mata bayan zaɓinki, idan ma hakane a ransu ai bani kaɗai bane ɗa a gidan ko?!…..”
“Ko kai kaɗaine bazaka aureta ba, kuma ko yanzu dan kayi aure idanma hakane a ransu Maheer ma yafi ƙarfin nan sai dai suje can su nema mata miji dan ko Khaleel saina hana uwarsa yarda”.
Murmushi ya saki mai faɗi da lumshe idanunsa. Yayinda kunensa ke cigaba da sauraren banbamin masifar Mommy. A haka su Aysha suka shigo suka samesu. Gaisuwar da suke masa ce ta sashi buɗe ido da tashi daga jikin Mommy yana kallonsu. Kafinma yace wani abu Hassan yay saurin faɗin, “Yaya daga aikan Gwaggo muke fa”. Komai baiceba ya miƙe ya fita a falon.
A yau da Anam ke cika kwanaki biyar a gidan ya kamata ta fara shirin fita aiki, amma mutuniyarku barcinta take sharɓa saboda jin daɗin ɗan sanyi-sanyin safiyar dan bata isashen barcin dare daboda zafi. Da zarar an ɗauke wuta bazata sake rintsawaba. Dan ƴar fan ɗin da Mom ta bata Fawwaz ya joganeta jiya taƙi ɗaukar caji. Gaba ɗaya Mom ta shafa’a da batun fara fitar Anam ɗin yau itama, shiyyasa batai tunanin tadata ba tanata ƙoƙarin shirya su Fawwaz karsu makara tafiya makaranta suma. Sai daga baya ta tuna taje ta kakkaɓeta da ƙyar..
Kamar kullum cikin shirin fita office ya fito. Shareff mutum ne mai himma, bashi da wasa akan aikinsa shiyyasa a kullum cikin haɓaka kamfani yake. Zamansa tsayayyen mutum yasa ma’aikatan ke tsananin shakkarsa da kiyaye dokokin kamfani, dan shi babu ruwansa yana ganin baka serious zai sallameka ne acewarsa a kwai dubu masu buƙatar gurbinka zaune a gida. Sashen Mommy ya fara shiga, ƙanensa nata ƙoƙarin karyawa suma. Cikin girmamawa duk suka gaidashi. Amsawa yay yana ƙoƙarin kaiwa zaune a ɗaya daga kujerun falon dan bazaka taɓa ganinsa cikinsu yana cin abinciba. Mommy dake tsaye itama a dining ɗin tana haɗa masa tea ta ƙaraso garesa. Tunkan ta ƙaraso ya miƙe fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mug ɗin. “Good morning First-luv”.
“Morning dear, how are you?”.
“Alhamdulillahi”.
“Haka ake so ai. A saka maka Irish ɗin?”.
“No Mommy wannan ɗin ma is ok for me. Yau na makara gashi inada meeting eight thirty”.
“To aiko gara ka hanzarta tunda gashi eight ɗin gab yake dayi”.
Koda ya fito sashen Mommy wajen aunty Amarya ya shiga suka gaisa kamar yanda ya saba duk safiyar duniya zai shiga ya gaida kowa na gidan. Daga nan kuma babu mai sake ganinsa sai wata safiyar, sai dai duk ranakun juma’a da laraba zai sayo fruit bayan ya tashi aiki ya shiga kowane sashe yakai musu, hakama duk ƙarshen wata zai sayi kayan tea dasu sabulai omo MacLean kayan dai buƙata kananu yakai kowane sashe. Tun Mommy najin haushi da masa faɗa har dai ta tattara ta zuba masa ido amma hakan na damunta da ɓata ranta saboda zugar Gwaggo. Sashen Gwaggo ya nufa itama ya gaisheta dan itace a tsakiyar Mom da aunty amarya. Yasanta da son su zauna hira dan haka ya maƙale daga ƙofa suka gaisa duk da tayin kunun gyaɗa da take masa kuma ransa naso.
“Gwaggo na makara, amma zubamin zanje da shi office nasha. Bara na gaida Mom a kaimin mota”.
Kafinma tace wani abu ya fice da sauri zuwa sashen Mom idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Gaisuwar su Fawwaz ya fara amsawa dake fita da gudu zuwa school bus ɗinsu. Kafin ya ƙarasa cikin falon su gaisa da Mom. Itama nan koda tai masa tayin abinci cayay Alhmdllhi ya fito da hanzari. A jikin motarsa ya samu Ladi mai aikin Gwaggo ɗauke da ƙaramin basket. Tunkafin ya ƙaraso ya buɗe motar da key tai ƴar ƙara. “Ranka ya daɗe gashi inji Gwaggo”. Baice komaiba ya amsa basket ya ajiye a gefen mai zaman banza, fitowar Daddy ta dakatar da shi daga yunƙurin shiga motar da yay niyya ya nufi Daddyn ɗin duk da sun gaisa bayan fitowarsu massalaci da asuba, tare kuma suka fita motsa jiki….
“Babana har an fito?”.
“Eh Daddy nama so makara dan inada meeting”.
“To ai yau da gobe sai ALLAH ko”. Daddy ya faɗa dai-dai da fitowar Anam daga sashen Mom. Tsaf take shirya cikin kayan NYSE da sukaima jikinta cif kamar ka saceta ka gudu. Ta naɗa yololon veil ɗinta tare da ɗora p-cap ɗin samansa, saita goya bag ɗinta mai suffar teddy data zuba komai a ciki. Tayi ƙyau sosai sai zuba ƙamshi take mai daɗi. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufo inda suke, sai da ta sauke hular daga kanta tace, “Good Morning Daddy”.
“Good Morning Maman Daddy. how are you?”.
“I’m fine Daddy, sai dai zafi da dare barci babu daɗi”.
“Ayya mamana ba’akwai fan a ɗakin naku ba?”.
“Akwai Daddy, idan suka ɗauke nepa ɗinne fa, fan ɗin da Mom ta bani yaƙi ɗaukan cagi jiya”.
Kanta ya ɗan shafa da faɗin, “Am sorry insha ALLAH za’a saya miki wata to koda an ɗauke wutan, koma ac za’a sayo dai?”.
Ƴar dariya tayi da satar kallon Shareff da tun zuwanta wajen ya haɗe fuska yana danna waya kamar bai san da zuwan nata ba. Shima Daddyn dariya yay da duban Shareff ɗin, “Kun gaisa da Yayan naki ko?”.
Baki taɗan tura gaba da ɓata fuska, sannan tace, “Good morning”.
Duk da sarai yajita bai amsaba, sai duban Daddy yay yana tura wayarsa a aljihu da faɗin, “Daddy bara na wuce ina ƙara makara”.
Daddy yace, “Ato shikenan sai kije ya saukeki tunda hanyarsa ce”.
Idanu ta waro da ƙyau tana ƙyaƙyƙyafta su. “Daddy Abie yace driver zai dinga kaini”.
“No na dakatar da shi ai. Duk motocin gidan nan ace sai an ɗauka miki wani driver. Idan Shareff zai fita sai ya dinga tafiya dake, idan ya tashi aiki kuma ya ɗakkoki ba shike nan ba”.
Zatai magana ya girgiza mata kai alamar kartace komai. Shirun kuwa tai, sai dai kamar zatai kuka takeji. Sam bata buƙatar haɗa sabgarta da shi. Duk miskilancin Khaleel tafi jin daɗin zama da shi, shiko Maheer dama mutum ne mai sauƙin kai da faran-faran, shiyyasa da akace mata bayanan taji duk babu daɗi.
Ganin shima baice komai ba Daddy ya dubesa “To ALLAH ya bada sa’a. Sai ka wuce da Mamana ko”. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan rissinar da kansa ƙasa da fadin. “Mu yini lafiya”. Jinjina masa kai shima Daddyn yayi. “ALLAH yasa. Mamana bishi ALLAH ya bada sa’a”. “Amin Daddy” ta faɗa dabin bayan Shareff da tuni yay gaba abinsa kamar ta make masa ƙeya……….✍