BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

        Da sassarfa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa. Ya duba Anam dake barci hankalinta kwance harda naɗewa cikin lallausan duvet nashi dako shi bai taɓa lulluɓa da shi ba. Nufarta yay yakai hannu kamar zai tadata sai kuma ya fasa, ya ɗan furzar da huci tare da dafe goshinsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya tabbatar su Mommy suka ganta ya shiga uku, dan baima san kalar ƙurar da zata iya tashi a family ɗin MD Shareff ba yau. Jin horn ya sashi sake ambaton “Ya ALLAH”. Tare da fita a ɗakin domin buɗe musu tunda babu maigadi har yanzu sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu yake saran Fharhan zai kawo shi…..

         Tunda ya buɗe musu gate bakin Mommy da Gwaggo ya sake washewa. Suma dai su Mom fuskarsu da murmushin jin daɗin ganin yanda ɗansu ya gina wannan gida dako maƙiyi ya gani zai yaba ko’a zuciyane.
      “Kai-kai! Anya kuwa Alhaji ƙarami bazan dawo nan ba irin wannan gida haka?”.
    Gwaggo ta faɗa tana riƙe haɓa dabin ko’ina da kallo. Murmushi yay mata da shafa kansa. “Indai bazaki dinga damuna da kwakwazonki ba sai na dawo dake”. Dariya su Mom sukasa, yayinda Gwaggo tai masa daƙuwa. Nanma murmushi yayi kawai. Da kansa yay musu jagora suka shiga ko’ina suna mai yabawa da masa addu’a, bakin Gwaggo da baya iya yin shiru tace, “Toni abinda ban ganeba anan, Alhaji ƙarami yanaga sashe biyu, gidan kamar na zaman mace fiye da ɗaya! Kar dai kacemin kaima halin Kakanka da ubanka zakai tara mata?”.
      Ganin duk su Mom sun juyo suna kallonsa, har fuskar Mommy ta sauya ya sashi ɗan hararar Gwaggo ta ƙasan ido. “Kai tsohuwarnan kedai bakinki bai iya shiru, kawai dan mutum yayi wadataccen waje a gidansa sai yazam na aure? Nayine saboda ke in kinzo kwaɗayin jar miya”.
        Dariya su Aunty Amarya suka sanya. Mommy ma ta ɗan saki fuska tana murmushi dan tun farkon fara ginin gidan da tazo ta gani ta masa irin wannan maganar ganin sashe biyu da nasa na uku, amma sai yace yayine kawai saboda baƙi. Haka kawai zuciyarta taƙi aminta da shi taita masa bin…..
       “To shikenan muje ka kaimu naka sashen muga namai gida”.
   Gwaggo ta katse mata tunani. Gabansane ya faɗi, zaiyi magana Gwaggo ta nufi ƙofar sashen da basu shiganba wanda tabbacin nasan ne, itama Mommy saita take mata baya. Hakan yasa dole su Mom ma binsu. Da ƙarfi ya rumtse hanunsa da cije lip ɗinsa. Ganin har Gwaggo ta shige yay saurin bin bayansu shima dan ya tabbata target ɗinta na biyu shine bedroom ɗinsa. Kamar yanda yay hasashen kuwa hakane. Dan ko falo bama tagama nutsuwa ta ganiba ta nufi ƙofar bedroom acewarta da nan zata fara a sashen. Shigowarsa tayi dai-dai da ɗaura hanunta a handle ɗin ƙofar………….✍

    ????????Yau munga idi wagga tsohuwa babu man kai zata ɓaro aiki. Dangin Anam kuna ruwa, maganin masu bin mazan mutane kenan????????????????
     

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107

ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*.      *_Typing????_*




  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

09

………Murmushi Fadwa ta sakar masa, cikin narke murya taima hannunta kiss da hura masa .
      “I miss you my Soulmate”.
   Kansa kawai ya jinjina da wani ɗan guntun murmushinsa iya laɓɓa. Cikin iyayi da feleƙe ƙawayen nata ke gaishesa idanunsu kamar zasu faɗo a kallonsa. Ɗan tsuke fuska yay yana amsa musu sama-sama.
        “Baby am sorry na saka wahala”.
Fadwa ta sake faɗa tana sake narke masa har tana saka tsigar jikinsa tashi. Nanma murmushi kawai yay mata da kauda kansa daga gareta dan shi kaɗai yasan halin da dama yake ciki ita kuma tana son sake kunnashi da wani. Cikin motar yay ƙoƙarin komawa da nufin ɗakko mata saƙonta, ita kuma batare da tunanin tare yake da kowaba ta nufi ɗayan side ɗin a zatonta anan ya ajiye saƙon nata ne, tana kuma son ƙara birge ƙawayenta da akaikaice tasa ake musu hoto acan gefe batare daya sani ba….
        Sosai Anam ta cika tayi fam da takaici, tayi yunƙurin buɗe motar ta fita taji ya sakata a lock dan yasan dama abinda zata iyayi kenan tace zata fita kamar wancan ranar. Ya ɗakko ledar dake a back sit ɗin Fadwa ta buɗe ita kuma. Ido huɗu sukai da Anam, ta watsa mata wani kallon banza ta ɗauke kai dajan siririn tsaki da faɗin “Ballagaza” a hankali….
        A yau kam tayi laƙawarin bazata ƙyale ƴar iskar yarinyar nan ba. Cikin jin ɗacin (ballagaza) data kirata dashi tace, “Kin yima ubanki dan uwarki.”
    Duk da Anam bajin hausa take da ƙyau ba tasan zagi, amma sai tayi kamarma bataji Fadwa ɗin ba, taciro Bluetooth daga bag ɗinta ta fara ƙoƙarin maƙalawa a kunne Fadwa ta buge hanun Bluetooth ɗin ya faɗi ƙasa. Ƙafa tasa ta takesa da shegen takalminta mai tsananin tsini……
       “Fadwa!”.
    Shareff ya faɗa a ɗan kausashe…..
“……Amma dai Soulmate kanajin tsakin da taimin ai, ranar na ƙyaleta daboda darajarka, amma yau gaskiya bazan iyaba, ban son raini..!”
    Itama ta faɗa da sauri cikin tarar numfashinsa.
          Anam data sake cika tai fam tai yunƙurin hanɓarata baya ta futa. (Yo dama a gayama kura gayyar cin nama bayan bidirin nasu ne????. Ba’a takali Anam ba ma yaya aka ƙare balle anzo har gida da goron gayyata????).
      “Idan kika fita a motarnan sai ranki ya ɓaci!!”. Yay maganar a tsawace da fisgota ya maida ya zaunar. Kuka ta fashe masa da shi dan zuciyarta tazo wuya. Baibi takantaba yay yunƙurin fita a motar sai ya hango Fadwa can ta nufi motarta a fusace ƙawayenta na take mata baya. Idonsa ya rimtse da taune hakwaransa, sai kuma ya furzar da huci mai zafi yaja murfin a fusace ya rufe, na side ɗinta ma shine ya rufosa ya tada motar suka bar wajen dan tuni su Fadwa ma sun fice a wajen har tana bulama mutane ƙura.

         Cikin sake tunzurasa da kukanta keyi yaja birki da ƙarfi, firgita tai ta ɗago da sauri tana kallonsa. Harara ya watsa mata tare da gangarawa gefen titi ya kashe motar. “Nidai ka kaini gida, kuma saina sanarma Daddy mata na maka kiss a titi da rungumek….”
     Bamm ya bige bakin nata, kukan ƙarya ta sake fashe masa da shi dan ko hawaye babu yanzu sai dai taji zafi sosai. “Har Abba ma saina faɗawa da Abie da Mamie da Mom da aunty Amarya”. Ta sake faɗa da ɓalle murfin motar zata fice. Riƙota yay ya maida murfin ya rufe yasa lock. Takaicinsa da haushin abinda Fadwa ta masa yasa takejin zafinsa batare data san dalili ba, cizo tai ƙoƙarin kaima hanunsa dake riƙe da nata….
       “What!! Ni zaki ciza?”.
   Bata kulashi ba ta sake kaima hanun cizo. Babu shiri tilas ya saketa, yana mai girgiza kansa. A hankali yakai kwance jikin kujera bayan ya kwantar da ita, hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa ya lumshe idanu yana mata kallon ƙasan ido. Tunba yanzuba yasan Anam fitinanniya ce dama, sai dai yayi zaton tabar tsiwa zuwa yanzu, amma tun tana ƴar ƙaramarta boss ce daman. Yasha zuwa hutu ya samu an kawo ƙarar Anam daga school ta naɗi ƴaƴan mutane babu dalili, idan kuma gidansu akazo nanma ta jibga, idan gidansu taje yaran ba tsira sukeba. Ƴaƴan aunty Mimi ba ƙaranar wahalar Anam sukaci ba duk da wasu sun girmeta bata ɗaga musu ƙafa……..
       “Nidai ka buɗemin, bazan sake shiga wannan motar ba da akeyin wannan abun….”
      Duk yanda yaso danne murmushin dake son fita ya gaza hakan, gefe ya maida kansa yay murmushin kafin ya tashi zaune sosai fuska a haɗe ya riƙo hanunta dake jikin handle ɗin ƙofar, baki ta buɗe zata saƙi ƙara dan matse hanun yayi yasa yatsunsa biyu ya riƙe lips ɗin nata fuskarsa a tsananin haɗe. Sosai idanunta suka sake firfitowa, ga tsoro ga tsiwa……
       “Haɗiyemin wannan kukan, ki kuma faɗi miye abunda akeyin kona tattakaki”.
    Tsaf ta haɗiye kukan zuciyarta na bugawa da sauri dan kusancinsu yayi matuƙar yawa, kanta ta fara jujjuya masa a hankali. Idanu ya zare mata da sakin lips ɗin nata, “Ai saikin faɗa mara kunya”. A tsorace take amma bakin yaƙi mutuwa. Taja jikinta baya da maƙurewa a jikin ƙofa, “To ka bari muje gaban su Daddy ɗin basai na faɗa ɗin ba….”
     Bakin ya sake kaima ɗalli tai saurin duƙewa da cusa kanta a tsakanin cinyoyinta. Ƙwafa yay da komawa jikin kujerar ya lafe yana kallon waje,  kusan mintuna huɗu suna a haka ring ɗin wayarsa ya katse shirun nasu. Iska ya ɗan furzar da kallon wayar, ganin Daddy ya sashi ɗagawa yakai kunne a ladabce yay sallama.
       “Shareff kuna ina?”.
  Ɗan jimm yay saboda jin muryar Daddyn, sai kuma ya gyara zama da ƙoƙarin yima motar key yana bashi amsa. “Daddy gamu a hanyar tahowa gida”.  “To inna jiranku”. Kafin ya sake cewa wani abu ƙitt an yanke wayar. Shiru yay yana kallon wayar sai kuma ya sake furzar da numfashi. Ruwa ya ɗauka a baya ya miƙama Anam da itama ta ɗago tun ɗaga wayarsa. “Malama anshi ki wanke wannan banzan hawayen”. Baki taɗan tura gaba kafin ta amsa, ta buɗe murfin motar batare data fita gaba ɗaya ba ta wanke fuskar. Bag ɗinta dake kan cinyarta ya ɗauka ya buɗe, zatai magana ya harareta. Komai babu na kayan kwalliya da ƴammata kan ɗan fita da shi a bag sai lipsgloss kawai. Baice komai ba ya maida jakar ya rufe, tissue ya ɗiba guda uku ya miƙa mata sannan ya harba motar saman titi.
      Tafiyar mintuna ƙalilan ta kawosu gida, tunda aka buɗe musu gate ya sake tabbatar da babu lafiya, dan ganin masu baƙaƙen kayan nan yasan Aunty Halima ce a gidan. A karon farko yaji zafin hakan matuƙa, shikenan da abu ya faru tsakaninsa da Fadwa sai iyaye sun shiga ciki, to shikam idan anyi auren yaya kenan kuma?. Ita dai Anam ba fahimtar komai tai ba, dan tun kan ma ya gama kashe motar tai ficewarta sashen Mom a zatonta ma ko baƙi Abba ko Daddy wani yayi. Binta yay da kallo harta shige, ya sauke numfashi a hankali shima yana fitowa. Sashen Daddy ya nufa duk da yasan bai wuce ɓacin rai zai tarar ba.
      Tun kafin ya ƙaraso yake jin hargowar Gwaggo Halima daketa masifa, ya girgiza kansa kawai ya shiga falon da sallama. Da Fadwa dake faman rusar kuka suka haɗa ido, ya ɗauke idanunsa fuskarsa na sake tsukewa. Sosai Mommy ke antaya masa uwar harara, hakama Gwaggo. Daddy dai kallonsa kawai yakeyi cike da nazari. Shiko Abba murmushine ma akan fuskarsa yana sauraren ƴar uwar tasu kuma yayarsa. Ƙasa ya zauna ya shiga gaishesu. Abba ne kawai ya amsa da daɗin rai, sai Daddy daya sauke ajiyar zuciya. Mommy kam da Gwaggo hayayyaƙo masa sukai da masifa kamar yanda Gwaggo Halimar ta rufesa da tata. Shi dai babu wanda yacema uffan a cikinsu, kansa a ƙasa ma yake. Sai da sukai mai isarsu sukai shiru duk da Abbah nata son dakatar da su sunƙi saurarensa.
        “Ina ita mara kunyar dan ubanta? Kai yanzu Shareff ko kishinmu ma bakayi duk yawan ƴan uwanka da muka haifa karasa wadda zakai yawo da ita a motarka sai bare…..”
        Haka kawai maganar ta bashi dariya, amma sai baiyiba yay murmushi kawai da ɗagowa ya ɗan dubi Gwaggon tasa datai maganar.
    “Eh kalleni da ƙyau mara mutunci, ko kanada wata alaƙa da ita bayan ubanta dake matsayin ɗan uba a cikinmu da har kake wulaƙantamin yarinya akanta?”.
          “Dan ALLAH ya isa haka Halima, maganar yarinya ko matsayinta duk bashi bane ya taramu anan. Kai Shareff miya haɗaka da ƴar uwarka?”.
    Numfashi ya sauke a hankali da ɗagowa ya dubi Abbah da yay maganar ya sake sunkuyar da kansa. “Abbah ni bansan wani abu ya faruba. Ina office ta kirani tana buƙatar abu, duk da ina buƙatar zuwa na huta kuma tana ƙasa dani na ɗauka nakai mata har inda take badan ina jin tsoronta ba…….”
     “Amma daka tashi zuwa ai da wancan bakwainin yarinyar kazo. Dama ranar da ita kaje gidanmu taimin rashin kunya da marina ka hana na ɗauki mataki kace zaka ɗauka da kanka, yau kuma harda zagina tayi tanamun kallon banza irin like akwai wani abu tsakaninku. Ni gara idan sonta kake ka faɗamin na barmata kai kawai dan bazan iya shearing ɗinka da wancan jakar ba….”
       Idanunsa yay bala’in rumtsewa tare da dunƙule hanunsa da masifar ƙarfi. Daddy dake kallon hanun nasa ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, sai dai kamar yanda tun ɗazun baice komaiba yanzunma baice ba. Fadwa ta cigaba da sakin zance tana kuka har sai da Abbah ya ƙwaɓeta dan sai zagin Abie take da Anam….
      “You’re vary stupid. Baki san shi ɗin wanene ba a gareki? Ashe muma zaki iya zaginmu mara kunyar banza……”
     A zabure gwaggo ta tare numfashinsa da faɗin, “Yo Abubakar wane matsayi Usman kedashi a wajenku bayan ɗan uba da zaka balbaleta danta zagesa?”.
        “Haba Gwaggo wane irin magana ne wannan?”. Abba ya katseta ransa a ɓace. Gwaggo Halima zatai magana ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Bana sonji, daga yau kuma idan na sakeji a cikin ƴaƴanki wani ya zagi Usman to lallai ke kanki sai ranki ya ɓaci tunda akoda yaushe ke hankali baya isa miki cikin jiki. Wannan magana kuma na kasheta anan, sannan Mamana nine nace kullum Al-Mustapha ya sauketa a wajeb aikinta ya kuma ɗakkota tunda shine babba wataran sunan uba zai amsa a garesu. Bana son sake jin ƙananun maganganun nan daga yau, nakuma dawo da bikinsu baya zanje na samu Alhaji Sadiq ɗin, magana ya ƙare ok”.
       Babu wanda ya iya sake cewa komai, sai dai har cikin rai maganarsa ta farko ta zafi wasu a cikinsu, ta ƙarshe kuma ta musu daɗi kusan su duka idan ka cire uban gayya daya shaƙa yay fam. A wannan gaɓar yaji mugun haushin Gwaggo a ransa fiye da koyaushe, dan ya gama gane itace ke assasa tsanar juna a tsakanin iyayensu da ƴan uwansu guda biyu kacal dan kawai suna matsayin ba uwarsu ɗaya ba. Shi ya fara ficewa a falon batare da ko kallon wani ya sakeyi ba.
     Da sauri Fadwa ta mike tabi bayansa har tanayin tuntuɓe zata faɗi. Tana kiransa ko waugota baiyiba duk da sarai yajita. Duk da taji zafi haka ta cigaba da binsa har part ɗinsu, yana ƙoƙarin shiga ɗakinsa tai azamar shan gabansa ta tare ƙofar. Mugun kallo ya watsa mata, sosai hanjin cikinta suka kaɗa amma saita daure ta marairaice masa fuska.
      “Haba My Soulmate yanzu ɗinma wulaƙancin zakamin?”.
          “Bani hanya!!”.
    Yanda yay maganar a tsawace idanunsa har suna firfitowa yasata saurin matsawa. Hannu yasa ya ƙarasa ingijeta ya buɗe ɗakinsa ya shige tare da bugo ƙofar da ƙarfi har sai da ta sake zabura….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button