BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

Acan falo kuwa Daddy ne yay amfani da damar fitar su Shareff ya shiga yimusu nasiha musamman Gwaggo da Gwaggo Halima da Mommy da duk matsalar take daga garesu. Duk da a cikin lalama da son bada shawara yay maganar sai Gwaggo ta fashe da kuka tana matsar ido da fyatar majina wai ta fahimci laifinta suke gani dan bata haifesuba. “Shikenan Muhammadu nadai fahimci laifina kake gani, nidai ALLAH na gani ba inayi bane dan na rabaku da su kamar yanda kuke kallo sai dan kare martabarku da takaicin da uwarsu ta shaƙa mana a gidannan wajen mahaifinku. Babu annamimanci da kutungula da Zuwairah bataiba agaremu, akwai randa har sakinmu tasa mahaifinku yay a daren duk da ana ruwa yace mubar masa gidansa. Akwai randa ta ɗau hanun Halima ta turɓuɗa cikin murhu wuta naci wai dan ta zungurar mata icce. Kai har kusan jefa mahaifiyarku tai a rijiya lokacin tana goye da Umaru. Taya azzalumar mace irin wannan zanso ƴaƴanta kuma na baku goyon bayan kusota duk da abinda taima ƴar uwata. Ai shara’armu da Zuwairah sai dai a lahira, gashinan makirar jikarta ta gadota a komai na makirci. Dan haka bazaku taɓa samun nutsuwaba a gidannan tunda annamimiya tazo jinin munafukai…..” Fyaaaatttt. Ta face majina da ƙarfi da nufar hanyar ƙofa ta fita.
Mommy ma tashi tai a fusace tabi bayan Gwaggon tata. Cikin ɓacin Rai Gwaggo Halima ta dubi su Daddy. “Yaya kaji ko, duk da abinda uwarsa taima tamu uwar amma kuke nuna sonsa kamar…..”
“Halima!!”.
Daddy yay saurin dakatar da ita shima ransa a bace. “Amma Yaya itafa gaskiya ɗayace daga ƙinta sai ɓata. Wlhy wlhy kaji na rantse bazan taɓa son su Usman ba a gidannan. Har duniya ta tashi sunansu ƴan ubane a gareni, bawai ƴan uwa ba”. Fuuu ta figi jakarta ta fice. Duk da kallo suka bita. Abbah ya fara sauke ajiyar zuciya da maido kallonsa ga Daddy da ransa ke matuƙar ƙuna. Ya rasa mizai fassara Gwaggo da shi. Tun basu san kansu ba take ƙulla raba kansu, ALLAH gafurun kuma rahimun ya ganar dasu gaskiya hakan taƙi yuwuwa, amma bata barsun ba har saida haƙanta ya cimma ruwa. Sukazo babu dalili suka tsani ƴan uwansu da basu taɓa masu komaiba su da mahaifiyarsu sai alkairi, ALLAH ya ƙara taimakonsu suka gane suka canja. Gashi yanzu tana son saka ƙiyayya kuma a tsakanin ƴaƴansu, wace irin fitinace wannan, kenan itama data haihu a gidan basu isa su jitu da nata ƴaƴanba……”
Taɓashin da Abba yayne ya maidosa hankalinsa. Ya sauke numfashi a hankali da ɗago idanunsa irin na Shareff da sukai jajur yana kallon ɗan uwan nasa. Cikin ɗacin murya yace, “Abubakar itace silar komai. Duk wata ƙiyayya tsakanin Umma da Mama itace taita haɗata. Bata barsu sun zauna lafiya ba muma ta hanamu gashi zata hana ƴaƴanmu ma. Yanzu ƴar ɗaya tilo da ALLAH ya bama Usman ma bazata barta tasha iskar farin ciki a cikin namu ƴaƴan ba. Kana ganin Maryamu ta daina zuwa da ƴaƴanta ƙasar nan saboda Gwaggo. Haka kuma zamu cigaba da zuba idanu kenan Abubakar?!”.
“Bazai yuwu ba yaya. Dolene a wannan karon mu ɗauki mataki. Yaya Halima tafi kowa bani haushi. Sam ta kasa fahimtar halin Gwaggo tamkar ita ɗin ba mace bace ba. A zatona da ake cewa mata sunfi kowa zuminci ita ya kamata ta fara farga da son ganin mun dunƙule abu ɗaya amma da ita ake makamin rusamu. Bazan ɓoye makaba ina tausayin Shareff akan wannan auren. Bazasu barsa ya zauna lafiyaba dan itama yarinyar nan da kake gani shaiɗaniyar kantace Yaya”.
Sosai zuciyar Daddy ke ƙara tafasa dan yasan duk gaskiya ɗan uwan nasa ya faɗa. Shi kansa yana tausayama Shareff dan yana cikin kwatankwacin irin halin da suke neman jefasane akan mommy. Tunda ya aureta Gwaggo ta hanasu su zauna lafiya saboda kawai tana taƙama ɗiyar ƴar uwartace……
★★
Tunda ya shiga ɗakin bai sake fitowaba. Kwance kawai yake a gado ko takalmi bai cireba balle maganar wanka har aka kira magrib. Tashi yay ya nufi bayi yayo wankan a gurguje da alwala. Tsabar bai buƙatar haɗuwa da kowa ta baya yabi ya fita massallaci. Bai kuma dawo ba dan koda akai sallar isha’i can ya koma kan wani dakalin maƙwaftansu ya zauna…..
Tunda suka dawo gidan batabi takan kowaba. Tadai shiga ta gaida Mom sannan ta wuce ɗakinsu. Wanka tayi batare data ko shafa mai ba balle saka kaya ta kwanta da towel ɗin jikinta dan wani irin barci ke rinjayar idanunta kasancewar sanyin ruwan wankan dana jiƙar towel ɗin na ratsata. Barci sosai mai nauyi ya kwasheta, acikin barcin taji kamar abu na binta. A ɗan zabure ta farka ta hau dube-dube. Ganin jini ya sakata zaro idanu da dafe goshi. Shaf ta manta da batun zuwansa duk da sai jibi ya kamata ta gansa ma. Gadon ta ɗan dudduba, ganin bai ɓaciba ta nufi toilet da sauri, towel ɗin dai ya ɓaci kasancewarsa sky blue ya nuna sosai. Tasan yana mata zuba sosai shiyyasa bata wasa, gashi tanata son siyen audiga dama amma shiririta tasata mantawa dan ta saba sai da taga Mamie ta ajiye mata da lokacin yinsa yayi gareta. A gurguje ta gyara jikinta ta fito, baƙar abaya kawai tasa ta ɗauka atm ɗinta tayo waje. Ɗakin Mom ta leƙa ta samu tana salla, bazata iya jiraba dan akwai matsala zai iya sake ɓatata. Yanzunma handkerchief ɗinta sabo tai amfani da shi kafin. A falo ma duk sauran yaran sun fita massalaci kasancewar duk yaran Mom mazane aunty Rahma ce kawai mace, Husna ɗiyar ƙanwartace take riƙo bayan auren Rahama.
Su Daddy sun riga har sun shigo ciki, hakan yasa bata samu matsalar isa gate ɗin ba duk da batasan a ina zata samo audiga ɗin ba, kawai zatai dai tambaya ko gurin mai shagon layinne da sukan siyo ƙananan abubuwa wajensa koza’a samu kokuma ya faɗa mata inda zata samo….
Cak ta tsaya tare da saurin ja da baya saboda karo da sukaci, sosai gabanta ya faɗi, ta zabura da zummar komawa da baya tana kauda kai dan har yanzu haushinsa takeji akan abinda ya faru, Juyawa tai da sauri…..
“Idan kika ƙara stap ɗaya saina karya ƙafafunki”.
“Wayyo Anam kin mutu kawai”.
Ta faɗa tana rumtse ido da cije lip ɗinta kamar zata fasa ihu. Sai kuma ta juyo tana wani tamke fuska batare data yarda ta sake kallonsa ba, ita ala dole bata son yaga lagonta……….✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
11
…….Ɗin! Ɗinn!! Horn dake nuna alamar isowar dangin amarya Fadwa ya saka Gwaggo juyowa baki a washe tana faɗin, “A to ga masu ganin gidan nan ma sun iso ai? Kai Alhaji ƙarami muje ka buɗe musu ƙofa ɗin saina tarbesu ai ko”.
A hankali ya lumshe idanunsa da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Mommy ma bin bayan Gwaggo tayi, suma su Mom sai suka bisu kawai dan abu kaɗan zai iya jawo Gwaggo taita surutu. Har zai bisu ya dawo da baya, zuciyarsace ta bashi shawaran ya sakama ƙofar key, dan haka ya kulle da sauri ya fidda key ɗin ɗakin a cikin keys ya saka aljihu sannan yabi bayansu…
Mota uku ce a jere kai kace jeren kayan sukazo. Motar farko Fadwa ce ta fara fitowa a ciki, sai ƙawayenta uku. Ta biyu kuma ƙannen babanta ne su biyu da cousin ɗinta biyu suma dai duk masu aure ne. Sai aminiyar Gwaggo Haliman. Motar ƙarshe babban yayan Fadwa sauran kuma ƴan kamfanin da zasuyi aikinne dan motarma akwai tambarin kamfanin. Cikin mutunta juna aka gaisa tunda dama akwai alaƙa, kafin su ɗunguma gaba ɗaya zuwa can. Fadwa sai satar kallon Shareff take amma yayi kicin-kicin kamar ma bai ganta ba. Dama tun waccan ranar ko kiransa tai baya ɗagawa, idan tai masa magana koda yana a online kuwa ko buɗewama bayayi. Tabi duk hanyar daya dace su sasanta amma yaƙi kulata dan yayi alwashin koya mata hankali a wannan karon.
Ko’ina sai da suka shiga kowa na yabawa dan gida kam yayi sai dai maƙiyi. Ma’aikatan kamfanin da zasu saka kayan kuwa nata faman gwaje-gwajensu tunda dama amarya ta gama zaɓar wanda take buƙata tun a gida. Zare jikinsa yay ya koma sashensa batare daya amsa tambaya ko ɗaya ba akan ɗayan sashen dasu Gwaggo sukai magana suma. Shi dariya ma suke bashi da mamaki, ina ruwansu da sashen to tunda basu suka basa kuɗin ginin ba, sashen dama ko ƙarasa masa ayyuka ƙananu ba’aiba ya tsolema kowa ido.
Baifi mintuna biyar da shigowa ba Fadwa ta biyo bayansa. Bai nuna alamar yasan da shigowar tata ba. Duk da shariyar tasa ta sosa ranta sai ta shanye ta shiga yaba yanda sashen nasa yay matuƙar ƙyau shima. Yanda tsarin ya kasance na black and milk da ratsin ash ya matuƙar ƙayatarwa.
“Soulmate!”.
Ta kira sunansa a hankali tana kaiwa zaune kusa da shi. Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya dubeta ba yanata aikinsa kamar yanda ta samesa. Murmushin takaici ta ɗanyi tana kallonsa, ta lumshe ido ta buɗe akansa zuciyarta na raya mata abubuwa masu yawa dan ba ƙaramin haɗin kayan mata tasha ba. Sake matsawa tai jikinsa a kasalance ta ɗaura kanta a shoulder ɗinsa ta saki kuka.
Cak ya tsaya da aikin da yakeyi, yaja numfashi ya fesar yana mai rufe idonsa da buɗewa a lokaci guda…..
“Dan ALLAH kayi haƙuri ka daina fushi dani haka nan Yaya Al-Mustapha. Karka manta kwanaki takwas kacal ya rage mu zama abu guda, ina buƙatar ganin murmushi a fuskokinmu yayinda jama’a zasu fara taruwa dominmu daga gobe. Naji nayi laifi kuma na amsa na kuma bada haƙuri bazan sake ba mijina”.
Kalamanta sun ɗan saka masa sassauci, sai dai baida alamar cewa wani abu a zahiri. Kanta ta ɗago daga kafaɗarsa tana kallonsa idanunta na rige-rigen matso hawaye, ta riƙo hanunsa dake dafe da lap-top har yanzu sai dai ba aikin yake ba. “Baka haƙuraba ko My Soulmate? Shike nan na baka damar kaimin kowane irin hukunci amma dan ALLAH banda naƙin kulani na tuba”.
Karon farko ya ɗago idanu ya dubeta, kafin ya maida ga hanunsu dake cikin na juna. Nasa ya janye tare da ɗan bada tazara daga kusancinsu. “Naji ya wuce, sai dai ki tabbata kika sake hukuncin dazan ɗauka bazakiji da daɗi ba. Ni da ke zamu zauna bada iyayenmu ba, dan haka matsalarmu mune ya kamata mu fuskanceta basai wasu sunyi alƙalanci a ciki ba”.
“Insha ALLAHU zan kiyaye mijina”. Tai maganar tana faɗawa jikinsa ta rungumesa. Hannu yasa ya janyeta. “Nasha faɗa miki bana son ɗabi’ar nan sam. Domin babu wani hallaci daya halatta hakan garemu”.
“To kayi haƙuri, amma karka manta kwana takwas ya rage kacal mu zama ma’auratan ai ko, kaga kenan akwai banbanci da da yanzun”.
“Sai ki bari sai mun zama ɗin, a yanzu dai haramunne”.
“Hummm” kawai ta faɗa dan bata bukatar su sake wani rikicin kuma saboda kar yay amfani da damar yaƙi halartar duk events da suka shirya gara ta lallaɓasa ayi a tashi lafiya karya kunyatata ga ƙawayenta. “My Soulmate bara na ɗanyi using toilet Please”.
Ɗagowa yay ya ɗan dubeta dan harya sake maida kansa ga aikin gabansa. “Yanzu a barowanki gida har sai kinzo wani waje kin shiga toilet?”.
Murmushi tayi daya sake ƙawata ƙyawun fuskarta. “Oh My Soulmate nan ɗin aiba wani waje bane na daban, shine fa gidana nanda kwanaki kaɗan zan dawo rayuwar cikinsa. Bawani abu zanyiba part zan canja dan bana iya wuce awa ɗaya da shi a jikina”.
Idanunsa ya ɗauke daga kallonta, haka kawai yaji wani iri a ransa ganin babu ko ƴar kunya tattare da ita take faɗin part zata canja. Da hannu ya nuna mata toilet na falon.
“Ah-ah my Soulmate bara dai na shiga bedroom mana. Nan kuma idan cikin su Mommy wani ya shigo fa”. Komai baice mata ba, harta nufi hanyar bedroom ɗin Anam dake barci a ciki ta faɗo masa. Dakatar da ita yayi. “No ki shiga wannan ɗin can ƙofan nada matsala ne, sai angyarasa a rufe yake”.
“Okay! To bara naje naga bedroom ɗin namu ko?”. A ɗan kausashe yace, “Shi nake nufi”. Ɗan jimm tai tana kallonsa. Sai kuma tayi murmushi cikin rausaya kai ta nufi na falon kawai. Shima aikinsa ya cigaba dayi, a zuciyarsa yana ALLAH-ALLAH su kammala su tattara subar gidan.
Addu’arsa kam ta karbu, dan koda ta fito bata zauna ba kasancewar ƙanwar abbanta nata faman kiranta a waya akan ta fito zasu wuce.. Tare da shi suka fita, yaji daɗi sosai da su Mommy sukace suma zasu wuce ne magrib na gabatowa.