BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

     Bayan duk wucewarsu ya dawo ciki, kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa, key ɗin daya cire yasa ya buɗe babu zato ko tunanin ta tashi a ransa…. Kusan a tare ƙofofin guda biyu suka buɗe. Shi yana shigowa ita tana fitowa daga bathroom. Wata irin ƙara ta fasa da ƙanƙame guntun towel ɗin data ɗauro a jikinta dake ɗigar ruwa tareda faɗawa saman gado ta cukuykuye zanin gado da duvet ɗin gaba ɗaya a jikinta….
        “you are vary stupid!!”.
Ya daka mata tsawa jin tana barazanar fasa masa dodon kunne.
     “Na shiga uku ni dai ka fita, dan ALLAH ka fita, Yaya wlhy babu ƙyau ganin tsiraicin wani. Wayyo ALLAH Mamie banji maganarkiba nashiga halaka…….
    “Shut up! Stupid!”.
Ya sake faɗa da matuƙar takaicinta. Bedsheet ɗin ta tusa cikin baki tana gyaɗa masa kai ga hawaye na faman mata gudu a fuska kai kace wani abu yace zai mata. Shiko gaba ɗaya idanunsa sun birkice dan takaici, ya ƙarasa takowa gaban gadon yana watsa mata mugun kallo. “Ubanwa ya saki yin wanka anan ɗin? Ko an faɗa miki nan gidan wanka ne?”. Kanta take girgiza masa tana ƙara maƙurewa waje guda, dan ita a yanzu ba faɗan nasa take tsoro ba a yanda ya ganta da a yanda take. “Dan ALLAH kayi haƙuri Yaya. ALLAH zafine ya dameni kamar fatana zai ɗaye zufa ya jiƙani ina ƙyanƙyami shiyyasa nayi”. Rasama mizai ce mata yay, ga jikinta sai rawa yake matuƙa. Tsaki yaja ya juya ya fita kawai. “Mintuna biyar na baki”. Ya faɗa dai-dai yana jan ƙofar har saida ta zabura saboda bugata da yay.
      Kanta ta cusa tsakanin ƙafafunta ta ta sake sakin wani kukan na baƙin cikin ya ganar mata jiki abinda wani mahaluki bai taɓayiba bayan Aunty Mimi da Mamie. Duk da bawai tsirara ya ganta ba a ganinta ƙanƙantar towel ɗin baida maraba da hakan ita kam. Tuna abinda ya faɗa na karshe da yay yasata zabura. Durowa tai a gadon ta nufi ƙofar ta saka sakata, da sauri ta kwashi kayanta duk da ɗunbin ƙyanƙyamin da take musu ta shiga maidawa a jikinta da sauri-sauri. Bata kammala ɗaure igiyar abayar jikinta ba ta fito. A falo ta samesa tsaye sai faman kai da kawo yake tamkar mai safa da marwa. Tai ƙasa da kai dan a yanzu kam babu abinda take gudu kamar su haɗa ido, wani irin matsanancin kunyarsa takeji har ƙarƙashin zuciyarta. Shima bai dubi inda takenba ya nufi bedroom ɗin nasa, bai koyi mintuna biyu ba ya fito da kayansa da sukazo gidan suna jikinsa. Magungunanta da lap-top ɗinsa ya ɗauka yay waje. Da sauri tabi bayansa dan dama kamar jira take ace ar ta kwasa ana kare.
        A motar ma hankalinta ta maida gaba ɗaya waje badan tana fahimtar abinda take kallo ba, sai dan bata buƙatar koda kallonsa. Shima ɗin dai aikin tuƙinsa yake kawai lokaci-lokaci yakan amsa waya har suka iso gida. Yana gama parking ta fice. “Waye zai biki da wannan?!”. Baya ta dawo kanta a ƙasa ta ɗauka ledar magungunanta daya ɗaura saman mota ta wuce har tana harɗewa saboda yanda take tafiya da sassarfa.
     
     ★★★★

   Shirye-shiryen biki ya ƙara kankama, yayinda Anam ke faman wasan ɓuya da Shareff. Sam ta daina yarda su fita aiki tare, kafin ya fito ta shirya tabi bus ɗin su Fawwaz da ake kaisu school. Data tashi aiki kuma zata saka wani abokan aikinta ya tare mata Napep ta dawo gida. Bata yarda dai ta faɗama kowa abinda ya faru ba, sai dai tun ranar har yanzu bata sake ganin Yaseer ba. Ya daina shigowa aiki ta daina samun number ɗinsa kuma. Ta tambaya iya wanda suke mu’amula a wajen aikin nasu duk sun sanar mata suma basu san miya hanashi zuwa aiki ba. Amma dai ance ya kawo reason nashi wajen oga. Haƙura tai tabar bin kowa, sai ma haushinsa ya kamata. A yanda suke tana ganin ya dace ace ya sanar mata idan zaiyi tafiyane kokuma wani abu ya samesa ai.
        Ranar laraba gidan aka tashi da shirin isowar su Abie. Wannan ne ya ɗauke mata dukkan hankali ta manta da batun Yaseer. Taso ace da ita za’aje tarbo iyayenta airport sai dai batasan waye zaije ɗakkosu ba, dan haka ta haƙura kawai tai zaman jiransu a gida. Aiko ƙarfe huɗu da rabi na yammaci sai ga Shareff da Dr Jamal abokinsa ɗauke dasu a motocinsu ashe sune sukaje tarbosu. Cikin ƙanƙanin lokaci gida ya hautsine da murna dan harda aunty Mimi da yaranta itama. Duk da an share musu nasu gida an gyara komai tsaf anan suka fara sauka. Anam ta rungume iyayenta harda kukan daɗi su Mubarak na mata dariyar ta girma batasan ta girma ba. Duk wannan kaikawo da ihun yara da hayaniya Mommy da Gwaggo ko leƙe basu leƙo ba duk da kuwa sun san su Mamie sunzo ne domin bikin ɗansu. Hasalima duk wani ɗawainiyar biki Abie da Mami suka ɗauka. Acewarsu Shareff ɗansu ne, sune suka cancanci yimasa aure ba kowa ba. Hatta lefe da duk abinda aka kai gidansu Fadwa sai da Abie ya dawowa Daddy da Abba abunsu. Mommy taita masifa amma Daddy ya taka mata burki tun wancan lokacin dan a sanda Abie ya rako Anam ne. Sai da sukaci suka sha sannan suka shiga suka gaida Gwaggo. Mommy kuwa basu nuna sun san da zamanta a gidan ba Gwaggon ma dan uwa ce shiyyasa suka bata girmanta. Ai tuni Anam tabi su Mamie can gidan, dan taci alwashin bazatai zaman gidan nan ba dan bata ra’ayin ayi bikin nan da ita, duk da kuwa katanga ɗayace tasan wasuma zasu shigo gidansu a ƴan bikin, amma dai ko yayane bazai kai nan gidan ba ai. Sai dai kuma batasan tayi gudun gara bane ta faɗa gidan zago????.

          ★★★

    Acan gidan su amarya Fadwa kam wannan rana itace ranar ƙunshi, suna can ita da taren ƙawayenta wayayyu da gayyar media an ware musu part guda sunata shagalinsu harda su shisha. Ga hotunan amarya sun baje media musamman tiktok da istagram da amaryar ta tara ɗunbin followers da suka sakata yin ƙaurin suna cikin jerin celebrities da akeji dasu. Amarya tasha ƙyau da gyara harta gaji, sai dai ba’ai mata nata ƙunshin bama sai gobe idan ALLAH ya kaimu alhamis.

      ★★★

    Bayan sallar isha’i Mom ta aiko kiran Anam data maƙale taƙi bin su Aysha can gidan yin ƙunshi. Amma hatta da Amrah ɗiyar Aunty Mimi dake kusan sa’anni dasu Anam ɗin tana can itama za’ai mata. Cewa tai bataso itakam, dan ko wankin kai da sukaje yau ita ƙin zuwa tayi. Sai da Mamie tamata jan ido ta biyo ƴar aikin Mom. Amma da ta langaɓe wai kanta ke ciwo. Koda tazo anan ɗin ma faɗa Mom tai mata akan batun ƙunshin. Amma saita hau hawaye wai ita bata da lafiya. Kowa kallonta kawai yake da mamaki a falon, dan kuwa dai ko awanni huɗu bata cikaba da gama murnar isowar su Mamie ai. Ganin yanda take kuka Mom tace mata taje ta kwanta ayi mata gobe idan ALLAH ya kaimu. Ai kafinma ta rufe baki tayo waje. Maimakon taje ta kwanta ɗin can ta samu inda babu wadataccen haske ta zauna taci kukanta da batasan daliliba itama sannan ta koma gidansu tai kwanciyarta.
       Washe gari wajen sha biyu yaran gidan kowa da ƙunshi abin sha’awa amma banda Anam dako wanke kai bataiba balle maganar kitso. Tana gani suka shirya suka fita hausa day itako tace bazataje ba. Sai faman baƙin rai takeyi na babu gaira babu sabar. Mamie dai tunda taimata tambaya ɗaya tace bakomai bata sakebi takanta ba. Sai aunty Mimi ce ke faman lallaɓata da lallashinta. Sai tace kawai ita bata da lafiya ne.
       A wannan lokacin Shareff dake gidan batare da Anam ta sani ba ya shigo. Gabantane yay masifar faɗuwa. Ta miƙe zaram da nufin guduwa aunty Mimi ta dakatar da ita cewar ta kawo masa breakfast ɗinsa dake kitchen wanda Mamie dakanta da girka abinta kuma irin abincin ƙasar Malaysia ne. Jitai kamar ta fashe da kuka dan takaici, koda ta kawo ta ajiye masa ƙoƙarin juya tai zata bar wajen ya watsa mata mugun kallo saboda ido da suka haɗa by mistake. Baki ta murguɗa masa itama ta haura sama da gudu.
      “Kai kaji shasha lafiyarki kuwa Mamana?”. Aunty Mimi da bata lura da abinda ya faru ba ta faɗa da mamaki tana kallon hanyar da Anam ɗin tabi. “Babana wai kaga mi yarinyarnan tayi kuwa? Sai kace mai tsoron wani anan?”. Murmushi kawai yay baice komaiba. Ta hararesa. “Kaifa tsiyarka kenan ai magana ka bama mutum amsa da murmushi”.
     “Oh ALLAH small Mom rigima. Ni yanzu mikike so nace anan kuma? Ina ruwana da shirmenta”.
         Hararsa ta ƙarayi ta ɗauke kai. Yay dariya da shafa kansa yana buɗe kwanikan. Ƙamshin ya sashi lumshe ido murmushinsa na ƙara faɗaɗa. “Lallai na shaida Mamie na kusa dani”.
     Dariya aunty Mimi ta sanya masa da faɗin, “Makwaɗaicin banza”. Dariyar yayi shima da faɗin “Naji ɗin”. Haka ya fara cin abincin cike da nishaɗi suna hirarsu har Mamie ma ta fito daga sashen Abie ta samesu. Zama tai itama suka ɗora, daka gansu kasan akwai shaƙuwa mai faɗi a tsakaninsa tun ba yanzu ba. Anam na jiyo dariyarsu daga sama taƙi sakkowa har saida ya wuce massalaci sallar azhur. Aunty Mimi kuma ta fita zuwa can cikin gida ita da Mamie.
     Ta idar da salla tana shirin sakkowa ƙasa ta samu abinda zataci suka kusa cin karo da Fawwaz.
    “A’a autan Mom daga ina haka da gudu?”.
         “Yaya ne yace na kiraki”.
Kafin tace da shi wane yaya ya kwasa da gudu ya fice. Ta girgiza kai tana murmushi. Ɗaki ta koma ta ɗauka abaya kasancewar kayan jikinta wando da rigane marasa nauyi. Duk zatonta Khaleel yake nufi, shiyyasa ta fito hankalinta kwance. Harta nufi gate ɗin shiga cikin gida motar dake fake a tsakanin gidansu da cikin gida tai mata horn. Kamar bazata juyaba sai kuma ta dubi motar ganin an sakeyi alamar da ita ake, tunanin ko Yah Khaleel ɗin ne a ciki ya sata nufar can duk da tasan ba motarsa bace, bama tasan motar ba dan kamar ma sabuwa.
       “Tofa, wai su Yah Khaleel sabuwar mota akayine halan?”. Tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi tana shafa motar har side ɗin mazaunin driver. Kanta tsaye ta buɗe murfin. Duk abinda take dama idonsa a kanta, kuma yana jinta dan ya ɗanyi ƙasa da glass kaɗan. Da sauri ta saki murfin tana ambaton ALLAH tamkar wadda taga wani shaiɗan ko aljani. Ɗaga kafa tai da nufin juyawa ya dakatar da ita.
      “Idan kika bar wajen nan sai na mareki”.
   Tsayawar tayi, sai dai taƙi ta juyo. Hasali ma auna yanda zata arta da gudu takeyi…..
            “Zagaya ki shiga”
     Ta tsinkayi muryarsa a dake. Shiɗin ba abun wasanta bane, musamman a yanda yay maganar babu alamar wasa a cikinta. Ta haɗiye ƙwallar da suka taru mata a ido cikin cije lip tabi umarninsa. Sanyin ac da kamshi na musamman suka ratsata a cikin sabuwar motar da ko leda ba’a cirema kujerunta ba. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke da lafewa cikin kujerar ranta fal tunanin ina zai kaita? Bata da mai bata amsa dan haka taja bakinta ta tsuke ta zubama sarautar UBANGIJI idanu……….✍

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button