BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

        WASHE GARI ta kama ranar ɗaurin aure, har sha biyu Anam na ɗakin Abie tana shaƙar barci. Dan tun bayan sallar asuba ta gudo daga ɗakinsu saboda hayaniya tafi ƙarfi acan downstairs. Duk tashin da Mamie ta mata taƙi, sai kawai ta shareta ta cigaba da hidimar baƙinta, dan nan ɗinma dai ya cika taf da dangin Mamie da ƴan uwa da abokan arziƙi kasancewar wannan shine karo na farko da zata fara aurarwa, duk da ba’ita ta haifi Shareff ba an mata karar riƙesa da tai tamkar ɗanta auren ya koma tamkar a hanunsu ne.
      Mutane sai tambayar ina Anam akeyi, sa’ointa ma na family ɗin sunata zuwa nemanta. Bata tashi ba sai kusan ƙarfe ɗaya, batare da tayi ko brush ba ta fito sanye cikin kayan barci fuska a kwaɓe dan yunwa takeji. Fitowar tata yayi dai-dai da shigowar ango da tawagar abokansa, yayi ƙyau har ya gaji cikin ɗanyer shadda fara tas sai baza ƙamshi yake yi. Ga wani kwarjini na musamman da kwalliyar ta basa tabbacin yau ɗin ta daban ce a garesa. Hakama abokansa kowa ya sha ƙyau.
     Anam ta kafesa da manyan idanunta da barci ya sa su yin wani luf-luf da sake girma, shima tunda ya shigo nasa idon a kanta suke, sai dai lokacin ɗaya ɗan murmushi dake a saman fuskarsa ya bace ɓat, ya ɗan harareta ya ɗauke kansa kasantuwar caa da ƴan uwan Mamie sukai masa kowa na faɗin albarkacin bakinsa cikin yabawa.
     Murmushi ya ƙaƙaro yana kaiwa rissine domin gaishe su kamar yanda abokansa sukayi suma, kafin ya miƙe zuwa gaban Mamie da tun shigowarsu idonta ke kansa tana murmushi. Gabanta ya durƙusa ciki sanyin murya mai nuna rauni yace, “Mamie zamu tafi masallaci”.
      Hannu ta ɗora saman hularsa, itama muryarta a raunane da sanyi  tace, “ALLAH yay maka albarka Al-Mustapha. ALLAH yasa a ɗaura a sa’a, kuma yasa abokiyar arziƙinka ce har a aljannah”.
    Gaba ɗaya falon aka amsa da amin. Shareff da kansa ke ƙasa ya kasa ɗagowa, hakan yasa Mamie kamo haɓarsa da yatsunta biyu ta ɗago fuskarsa. A hankali hawayen dake maƙale a idanunsa suka gangaro, murmushi ƙarfin hali tayi da ƙoƙarin son danne nata hawayen dake son zubowa amma hakan ya gagara. Itama sai kawai ta saki kuka mara sauti tana goge masa nasa hawayen da hanunta duka biyu. Sun birge kowa, sun kuma bama kowa tausayi, duk da wasu basu san dalilin kukan nasu ba kai tsaye.
    Mamie dake murmushi ga hawaye tace, “Tashi kuje karku makara su Abie ɗinku sun wuce tun ɗazun. Kai Shareff ya gyaɗa a hankali, sai kuma ya kai hannu shima ya share mata nata hawayen, ta saki murmushi da shafa kansa. “ALLAH yay maka albarka”.
      Da amin aka sake amsawa. Ya miƙe idonsa na kallon ɗan lungun da zai sadaka da hanyar upstairs inda Anam take. Har yanzu tana gurin, hasalima leƙensu take baki a taɓe dan ita bataga miye na kuka ba inba gulma ba. Harda faɗin, “Su Mamie an iya kalan dangi, Mommyn sa batako kallona da arziki amma ke kinama ɗanta wannan kulan”. Ganin ya miƙene yasata komawa ta maƙale, jin kamar sun nufi hanyar fita ta sake leƙowa. Ido suka haɗa dashi yana tsaye shi da Aunty Mimi suna magana. Fuska ta taɓe da murguɗa baki tabar wajen. Numfashi ya saki a ɗan fisge da lumshe idanunsa ya ɗauke kansa shima. Aunty Mimi da duk taga komai tai murmushi kawai tana kallonsa.
      Fuska ya ɗan kwaɓe. “Miye kuma small Mom?”.
   Dariya tayi da faɗin, “A’a babu komai My son. Kuje karku makara ALLAH yasa a ɗaura a sa’a.”
     “Humm”
kawai yace mata yay gaba abinsa. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya. “Ita dai wannan Humm ɗin bata magani Yarona”.
       Murmushi kawai yay batare daya juyo ba ya fice abinsa. Dr Jamal da Fharhan da suka rage na take masa baya………✍????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: _Typing????

  *_❤‍????BABU SO....!!❤‍????_*
             _(Miya kawo kishi?)_



          *_Bilyn Abdull ce????????_*

13

……….Gab da magrib aka kawo amarya Fadwa, kamar yanda Daddy ya bada umarni nan gidan aka kawota wajen Mamie. Hakan ba ƙaramin zafar Mommy da su Gwaggo Halima da aka kira aka sanarwa abun yayi ba. Gwaggo kuwa kasa shiru tai sai da ta tanka, Daddyn yace ya gama yanke hukunci, miye ma abin magana bayan gobe idan ALLAH ya kaimu za’a maidata gidanta. Badan rigimar ta kwantaba akai daiyi shiru kowa yaje ya fara shirin tafiya dinner.
     Bayan sallar isha’i aka fara kwasar mutane inda za’a gudanar da dinner, sai dai har aka gama kwashe kowa babu Anam babu alamarta. Hasalima tuni taje tai kwanciyarta a falon Abie batare da kowa ya sani ba. Wajen dinner ya ƙayatar matuƙa. Amarya da ango sunyi ƙyau har sun gaji. Anci ansha ƙawayen amarya sun sami yanda sukeso suda amarya wajen daukar hotuna da videos wasu har live suke ɗauka ana kaiwa tiktok. Nera tayi kuka kamar yanda aka zubar da mutunci galan-galan dan anci rawa casss da warrr ƙawayen amarya ta rashin mutunci, amaryar kanta ta cashe kamar babu gobe, sai dai rashin yin rawar ango ta jawo cece kuce sosai dan wasu na ganin amarya Fadwa ta zaƙe da yawa. (Komadai miye ni ina ganin ranar farin cikin tace a barta ta shana????). Ƙarfe sha biyu taro ya tashi lafiya aka kwaso jama’a aka dawo gida.

    WASHE GARI aka gudanar da walima tare da yinin biki anan gidan, yini guda babu wanda zaice yaga Anam sai Mamie kawai da aunty Mimi, dan tana falon Abie kwance babu lafiya zazzaɓi ta kwana da shi har sai da doctor yazo ya dubata da safe ma, dan haka yau ko kwalliyar bikin ma batai ba abinta. Lokacin da taji sallamar Shareff zai shigo falon wajen Abie tashi tai ta gudu bedroom ɗin Abie ɗin, tanaji yana faɗama Abie baida kafiya shima da ciwon kai ya kwana kuma har yinin yau ɗin bai sakesa ba yana ganin hayaniyar nan ce. Baki ta taɓe cikin rashin damuwa tai kwanciyarta har sai da taji ya fita. Har dare bata sauka ƙasa ba dan bata buƙatar ganin Fadwa har tabar gidan. Hakan kuwa akayi, dan washeri lahadi akai buɗan kai bayan sallar azhar. Anayin la’asar aka ɗunguma raka amarya Fadwa gidanta, yayinda a bangaren ango yaketa ƙoƙarin sallamar abokansa na nesa da zasu wuce gida yau. Hakama baƙin nan gidan wasu daga rakkiyar amarya bazasu dawo nan ɗin ba…
       Gidan amarya kam sai sambarka. Komai yaji zam masha ALLAH. Har kusan bayan magrib sannan mutane suka gama watsewa aka barta ita da ƙawayenta kawai dake jiran abokan ango…..

      ★★

  “Wai nikam wane irin ango ne kai Al-Mustapha? A irin wannan ranar irinka ɗoki da zumuɗi baya barinsu amma kai tun ɗazun sai fama ake da kai ka shirya a rakaka kanata jamana aji”.
        Duk da sarai abinda Dr Jamil ɗin ke faɗa yana shiga kunnensa tunda a kusa da shi yake amma babu alamar zai motsa. Sai cigaba da danne-dannen tab ɗinsa yake hankali kwance. Fharhan dake faman musu dariya ya miƙe ya fige tab ɗin. Ɗagowa yay yana harararsa da miƙa hannu, Isma’il ya amshe tab ɗin daga hanun Fharhan shima yana dariya. “ALLAH baza’a baka ba. Garama ka tashi kaje ka shirya mu miƙaka muma muje musa haƙarƙarinmu a katifa matanmu na jiranmu.”
       Isma’il ɗin ya kafe da idanu kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kai kawai. Dr jamil ya dafa shi, “Wai nikam Musty ko tsoron amaryar kake ne? Idan akwai matsala inada kayan gyara masu inganci wlhy da zaka baje kolinka babu ragi babu ragowa”.
      Naushi ya kaima Dr Jamil, da sauri ya duƙe yana dariya su Fharhan na tayasu. Hararsu yay da miƙewa ya shige bedroom. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button