BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

★★★★★
Kwanaki sun cigaba da shurawa Anam na samun lafiyar ƙafarta. Tun daga ranar dai bata sake ganin Shareff a ƴan dubiya ba. Sai dai takanji maganarsa yazo gidan ko su Amrah suce mata yazo. Dan kamar da gayya sai ya daidaici lokacin da bata falon yake zuwa. Bata damu ba, dan a wannan gaɓar bama ta buƙatar ganin nasa sam. Tana son ƙara zama nesa da shi dan tunanin da aunty Mimi keyi a kanta ya gushe har abada. Kwanakinta biyar ta take ƙafarta sarai ta koma zuwa aiki. Kullum takan shiga gaida matan gidan cikin gida kamar yanda Mamie ke jaddada mata. Sai dai kuma iyakar Mom da Aunty Amarya kawai take zuwa ta gaida bata shiga sashen Mommy dana Gwaggo. Wajen aiki kam tare suke fita da Khaleel, wataran ya dawo da ita wataran Yaseer ya maidota dan yanzu ta ɗan fara sakin jiki da shi ganin bai nuna mata wata alama data danganci soyayya sai abota kawai. Muzzaffar ma yasha gwada zuwa ɗaukarta a office ɗin amma taƙi bashi fuska sam, hakan yasa ya fara zuwa gida kai tsaye dan shikam dai yaga matar aure. Tun tana noƙewa harta ɗan fara sakewa saboda huɗubar Aysha. Sai dai duk da hakan taƙi yarda ta amsa tayin son sa. Tana dai saurarensa darajar Abbansa abokin Abie ne kuma abota mai ƙarfi tun ƙuruciya dan tare sukai secondary school, a yanzu haka kuma suna ɗan huɗɗar kasuwanci tare.
A haka kwanakin hutun Shareff suka cika, Maheer ma ya koma katsina wajen nasa aikin tun satin daya shige. Da farko Shareff baya zuwa gidan da safe sai ya taso aiki yake shigowa ya gaidasu. Sai randa yazo sallama da su aunty Mimi da zasu koma Malaysia saboda yara makaranta ya samu Yaseer ya kawo Anam gida. Kuma har cikin gida Yaseer ɗin ya shigo gaishe da su Mamie, a yanda suka amshesa da alama ba wannan ne ma farko ba kamarma ya zama ɗan gida. Komai baice ba, sai dai koda Yaseer ya gaida shi hannu kawai ya ɗaga masa, daga karshe ma ya miƙe ya fice batare da an kammala sallamar ba. Da kallo kawai aunty Mimi ta bisa tana ƴar dariya, Anam kam ta taɓe baki da sake maida hankalinta ga Yaseer tana dariyar maganar Amrah kamar ma bata san da Shareff ɗin ba. Dan koda ta shigo ta gansa a taƙaice tace “Yaya good evening” tai wucewarta. Shi kuma bai amsa mata ba sai hararar da yabi ƙafafunta da su dan kansa a duƙe yake yana daƙilar waya.
Washe gari da shi akaima su aunty Mimi rakkiya airport, daga can kuma yay wucewarsa office. Anam kuma suka wuce tare da Khaleel daya buga mata warning ɗin kar ta sake tabi wata mota zai zo ya maidata gida da kansa koda bai tashi aiki ba. Badai tace masa komai ba, amma ta bisa da kallon mamaki. Hakan kuwa akai, tun kan ma a tashi aiki yazo yana zaman jiranta, washe gari ma haka sukai haka har kusan sati biyu da su Mamie suka fara shirin komawa suma. Nan fa hankalin Anam ya tashi, ta dinga kuka da magiyar zata bisu Mamie tace bata isa ba. Daga ƙarshe tai mata kaca-kaca sannan ta dawo lallashi da nasiha. Haka tanaji tana gani suka tafi suka sake barinta a Nigeria ita kaɗai. Cikin gida ta sake komawar dai sashen Mom dan nasu gidan an rufe kuma, ranar haka ta yini sukuku kamar mara lafiya, da ga ƙarshe ma har zazzaɓin sai da tayi. Sai da Khaleel ya samo mata magani.
Su Mamie juma’a suka wuce, dan haka bata fita ko’ina ba sai monday tai shirin zuwa wajen aiki. A cikin ɗaya a dogayen abaya da Mamie tazo mata da su tai shirin, bayan ta saka kayan hidimar ƙasa a ciki dan sanyi takeji yau. A hankali ƙamshinta ke fita, ga black skin nata na shining exactly cikakkiyar ƴar Africa. Bisa matsawar Mom ta zaman yin breakfast da abinda take iya ci da Mom ta jura girka mata batare da gajiyawa ba. Kaɗan ma taci ta miƙe tana faɗin, “Alhmdllhi”.
“Badai ƙoshi ba?”.
Mom ta faɗa tana kallonta. Murmushi tayi mai sanyi tana jinjina kanta, dan gaba ɗaya ta zama wata sukuku. “ALLAH Mom na ƙoshi, yau kwata-kwata banajin cin komai ne”.
“Anjima fa zaki iya jin yunwa”.
“To Mom bara naje da shi office ɗin”.
Babu musu Mom ta juye mata a kula mai ƙyau. Sai da ta jira Khaleel yasha shayi shima sannan, fita yay akan ta samesa waje zai shiga ya gaida jama’ar gidan. Saboda kar yasata binsa zuwa gaida su Mommy da tun kan su Mamie su wuce bata zuwa gaida su, shiyyasa ta noke akan zata samesa a mota. Sai da ya fita da kusan mintuna huɗu sannan ta fito. Waige-waige ta shigayi a harabar gidan babu alamar motarsa, tasan yakan kaita waje wani lokacin, dan haka ta nufi gate idan ya fito kawai sai su wuce.
A wajen gate ɗin kuwa ta samu motar Khaleel tare da makanike, ta ɗanyi tsai tana kallon motar da tai fakin a kusa da motar Khaleel ɗin. Kamar tasan motar, sai dai ta manta mai ita dama yaushe ta taɓa ganinta…. Horn ɗin da akai ya sata haɗiye sauran tunaninta. Makaniken dake duba motar Khaleel ya ɗago yana kallonta “Hajiya kamar dake ake fa”.
Ba laifi yanzu kanta ya ƙara buɗewa da jin hausa fiye da yanda tazo, ta jinjina masa kanta kawai batare da tace komai ba. Da farko bataji zataje ba, sai kuma ta canja shawara da tunanin ko Yaseer ne ya ɓadda kama. Murmushi ta saki akan wannan tunanin tana nufar motar.
Yanayin sanyinta a tafiyar ya sashi kafeta da ido cike da nazari, gashi bayan murmushin dake fuskarta babu wani alamun nishaɗi ko farin ciki a tattare da ita.
Zuciyarta ta gama yanke mata shawarar Yaseer ne, hakan yasata nufar ɗayan gefen batare da neman sanin waye ba ta buɗe ta shiga cikin ƴar dariya tana faɗin “Lallai ma Yaseer, kana tunanin ɓadda kama zata sa na gaza gane k…..” Sauran kalmomin suka kasa ƙarasa fita a bakinta saboda ƙamshin turaren da sai a yanzu ta samu nutsuwar banbancewa. Da sauri ta juyo batare data ƙarasa rufe motar datai yunƙurin yi ba. Har cikin rai ta tsorata da katoɓararta, amma sai ta dake cikin son kame kanta tace, “Oh Yaya yi haƙuri, ALLAH nama zata Yaseer ne ina kwana!”.
Shiru kamar bazai amsaba, dan tunda ta shigo bai kalleta ba ko sau ɗaya. Idanunsa da suka surku da ɗan ja ya ɗago ya zuba mata. Ƙoƙarin dannewa da ɓoye tsoranta take a fili, ta kai hannu kan ƙofar da nufin buɗewa ta fice ko zata samu damar shaƙar iska yasa lock.
(Ya ALLAH, wannan mutumin zai iya cinyeni fa a motar nan wlhy gara na lallaɓa) ta ayyana a zuciyarta. Idanu ta marairaice kamar gaske ta ɗago tana kallonsa, “Yaya kayi haƙuri ALLAH ban san kai bane”. Motar yayma key batare da yace mata komai ba ya fisgeta har yana bulama bakaniken dake duba motar Khaleel ƙasa.
Sunayen ALLAH kawai take ambata a ranta dan tasan itakan yau sai romanta za’a samu a hanun mugun nan……
“Mina faɗa miki akan yaron nan kwanaki?!”. Ya faɗa a kausashe dai-dai yana hawa kan babban titi. Kallonsa tai fuska a dake, ta kuma ɗauke da sauri saboda tasa fuskar ma tafi tata dakewar. Cikin ɓata fuska da tura baki tace, “Toni Yaya bamfa san wa kake nufi ba ai”.
Komai baice mata ba, ya cigaba da driving nasa, sai da suka iso dai-dai wajen nata aikin yay fakin daga ɗan nesa. Da mamaki ta kallesa, “Yaya yanaga ka tsaya na…..?”
Rinannun idanunsa daya dasa a kanta ya sata haɗiye sauran maganar muƙut, tai ƙoƙarin ɗauke idonta ya hana hakan cikin tsareta da nasa da duk suka firgitata. “Ni kike faɗama bakisan wa nake magana akai ba.”
Da ƙyar ta fisgi idanunta tai ƙasa da su zuciyarta na bugawa da sauri saboda yanayinsa ya masifar tsoratata. Da sauri ta rumtse idanunta saboda jin yatsun hanunsa a kan haɓarta, ya ɗago fuskarta sosai tare da matsota garesa har suna iya shaƙar numfashin juna. “Buɗesu kona mareki!!”.
Buɗewar tai da sauri saboda kusancinsu ba ƙaramar rikitata yay ba, hatta shi kansa yana iya jin sautin bugun zuciyarta ta hanyar ɗagawa da ƙirjinta ke ɗanyi da sauri-sauri……….✍