BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari monday Anam ta koma aiki, Abie da kansa ya kaita. Hakan ya mata daɗi, ya kuma sakata a farin ciki har fuskarta ta kasa ɓoyewa. Da Yaseer ta fara cin karo, wanda rabonsa da zuwa aiki tun randa ya kaita gida. Kallon kallo suka tsaya yima juna, farin cikin da take ciki ya sata fara sakin murmushi. Cikin harshen turanci da mutsukka idanunta take faɗin, “Ko aljani ne kemin gizo”.
Duk yanda ya so daurewa sai ya kasa. Ya saki murmushi yana gyara tsaiwarsa. “Ba aljani bane ifiriti ne”. Dariya maganar tasa ta bata. Ta ko ƙyalƙyalawa cike da nutsuwa tana kare bakinta da handkerchief. Jiyay gaba ɗaya ya narke a kallonta, harma zuciyarsa na jin anya kuwa zai iya kiyaye dalilin da ya sashi jin zai nisanceta kuwa?... Matsowarta kusa da shi ta katse masa tunani. Har yanzu fuskarta ɗauke da murmushi mai bayyana haƙwara. “ALLAH da gaske naji kewarka Friend. Wane laifi mukai haka ake fushi damu harda tafiya babu sallama?”.
Hannayensa ya haɗe alamar ban haƙuri????????, fuskarsa a marairaice sai dai baice komaiba. Cikin ƴar dariyar data ƙara zuwa mata tace, “Shikenan ya wuce muje ciki”.
Tare suka shiga, suka cigaba da hidimomin gabansu. Koda aka tashi aiki Maheer ne yazo ɗaukarta. Ta nuna farin ciki anan ma dan tunda yazo hidimar biki ta hana su zauna su gaisa da ƙyau. Maheer baida damuwa, yanada sauƙin kai sosai ga barkwanci, sai dai Shareff ya fisa haƙuri nesa ba kusa ba, kawai dai yafisa sakewa da mutanene shiyyasa ake ganin kirkin Maheer fiye da Shareff ɗin.
Bai wuce da ita gida kai tsaye ba. Sai da suka biya wani joint sukaci kayan kwaɗayi sukai hira sosai sannan. A hanya yake cemata yaushe zata rakasa gidan amarya yaga gida. Cikin taɓe baki ta bashi amsa da “Yah Maheer kaje abinka kai kaɗai kawai”.
“Miyasa bazakije ba ke?”.
“Ba komai, kuma ni nama riga naje ai”.
“Idan kin koma ma ai duk cikin zuminci ne”.
Maimakon ta amsa masa sai ta canja da wata hirar. Shima sai bai sake maganarba har suka isa gida.
A kwana a tashi ango da amarya sukaci kwanaki shidda da angwancewa. Soyayya ce ake zubawa tamkar babu gobe. Basu da matsalar abinci, dan kullum sai Mamie ta aika musu na safe na rana harda na dare ma, sai da Yah Shareff ɗin da kansa yace a daina kai na daren sannan Mamie ta hutar da kanta. A komai nane suke da juna tamkar su haɗiye kansu. Basu da wata damuwa sai suci suyi ƴar soyayyarsu. Babu inda yake zuwa dan ya ɗauka hutu na sati biyu dama, duk da sati ɗaya yay niyya Fharhan ya takura masa akan biyu dai sannan gajiyar biki ta sakeshi. Ya dauka sati biyun dai kawai badan yana tunanin zama har su cika baije office ba, dan yasan sunada ayyuka danƙam harma da wasu sabbin projects da yake fatan samu wanda zasu fito ne daga gwamnati.
Yakan je gidansu a kullum da yamma ya gaida iyayensa, sai dai koya shigo wajen su Mamie basa haɗuwa da Anam. Dan a mafi yawan lokuta yakan zone bata dawo aiki ba. Bakuma dan lokacin dawowar tata baiyiba. Kawai dai yanzu Maheer na matukar ɗauke mata hankaline, yama hana Abie kaita da safe shi ke kaita ya kuma je ya ɗakkota, bakuma su dawowa gida sai sun ɗan zaga gari wani lokacin ma sai bayan magrib. Wannan dalilin yasa duk sanda Yah Shareff yazo baya samunta a gidan. Bai dai taɓa magana ba, hasalima bai nuna ya san da wanzuwarta ko saɓanin haka ba. Itako dama ko'a jikinta harma mantawa take da shi yanzun, dan koba komai ta huta da harara da kallon dake matuƙar ƙona mata rai daga garesa.
Yau ta kasance juma'a. Da wuri Maheer ya ɗakkota a wajen aiki da jaddada mata ta shirya da wuri zatai masa rakkiya wani waje. Batare data tambayesa ba tace to. Ciki ta shige, bayan ta gaida Mamie da Abie ta wuce ɗakinta. Dan aunty Mimi da yaranta sunje Abuja gidan yayan mijinta, amma yau suke saran dawowarsu. Wanka tai ta shirya tsaf cikin kwalliyar doguwar rigar material dan Yah Maheer yace mata tasa kayan hausawa. A lokacin har tana ɓata fuskar cewar ita suna damunta bata son zafi, lallaɓata yay, dan yafi son ganinta a kayan saboda ƙyawun da suke mata. A bikin nan ba ƙaramin son ganin kwalliyarta ya dingayi ba. Koda Mamie tace ta zauna taci abinci catai a'a zasuci a wajen cin abinci Yah Maheer zata raka wani waje. Mamie ta ɗanyi jimm sai kuma ta sauke numfashi, gargaɗi tamata nata kama kanta tare da jin tsoron ALLAH.
“Insha ALLAHU Mamie bazaki taɓa yin kaico akaina ba, yanda nake a gaban idonki haka zan cigaba da kasancewa a bayan idonki. Domin UBANGIJIN dake azaba ga wanda ya saɓa masa, yake rahama ga wanda ya bisa yana kallona koda ke baƙya ganina”.
Murmushi Mamie tayi, cike da jin daɗi da alfaharin tarbiyyar da suka bama gudan jininsu tilo duk da suna rayuwa a inda kowa ke ganin dole ne yaro ya lalace, sai dai ba hakan baneba, kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi. “ALLAH yay miki albarka, ya kuma baki ikon tabbatarmin da hakan”.
“Amin Mamie na uwa ɗaya tilo”.
Ta faɗa tana sumbatar hanun Mamie sannan tai mata sallama ta fice.
Tun tafiyar tasu batai nisa ba sosai ta fara fahimtar inda suka dosa. Taso ta share amma saita kasa. ta dubesa a shagwaɓe “Yaya nifa....” Da sauri ya dakatar da ita ta hanyar fadin, “Ban son kice komai. Ai ni zaki raka ko”. Shiru tayi badan taso ba. Dan tana ganin girmansa da kima sosai a zuciya da ayyuka. Hira ya cigaba dayi mata, wani ta amsa wani tai murmushi har suka iso. Har ciki ya shiga da motar, kamar yanda ya saba mata a tsakanin nan shine ya fara fita sannan ya zagaya ya buɗe mata fuskarsa dauke da murmushi kamar yanda tata ma ke ɗauke da murmushin mai bayyana haƙora. Tace, “Kai Yaya Maheer shine har da wani ɗan respect?”.
Dariya ya sanya, idanunsa akan fuskarta yana ji kamar ya haɗiyeta dan murmushi na mata masifar ƙyau. Ƙara risinawa yay irin na respect ɗin yana nuna mata hanya alamar suje. Dariyar ta sake sanyawa da salute nashi itama....
A hankali ya lumshe idanunsa da ɗaukesu daga garesu yana sakin siririn tsaki dan komai yana faruwa ne akan idanunsa kasancewar yana daga barandar sashensa tare da Fharhan da Khaleel suna magana akan office. Tsakin nasa yasa Khaleel da Fharhan da suma ke kallon su Anam ɗin maido dubansu garesa. Sai dai kasancewar ya riga ya maida ga lap-top ɗin dake cinyarsa yasa basu fahimci da ainahin wa yake ba. Khaleel ya mike yana miƙama Maheer daya iso wajen hannu yana faɗin, “A'a Brother dama nan kawo ashe?”.
“Eh wlhy, ai ban san kaima nan din kayo ba damun haɗa tafiyar ma ai”.
“Ai babu damuwa tunda ga ƴar rakiya ka samo”.
Murmushi kawai Maheer ɗin yayi da maida hankalinsa ga Fharhan suka gaisa cikin mutunci dan duk abokan Shareff suna ɗaukarsu yayu suma.
“Babban Yaya barka da yammaci”.
Maheer ya faɗa idonsa akan Shareff. Sai lokacin ya ɗago, ya ɗan dubi Maheer ɗin fuska babu yabo babu fallasa. “Daga ina haka?”.
“Daga gida muke. Yau dai nace bara nazo na gaida amarya na huta da gorinta”.
“Hakan nada ƙyau”.
Ya faɗa a taƙaice hankalinsa nakan abinda yakeyi dan dama tuni ya maida kansa ga lap-top ɗin. Shima Maheer maida dubansa yay ga Anam data coge can taki karasowa. “Hajjaju ƙaraso mana ku gaisa da su Yaya”.
Baki ta tunzura, badan taso hakan ba ta nufesu tana ƙunƙuni. A jimlace ta gaishesu, batare data damu dawa ya amsa ba waye bai amsa mata ba tabar wajen. Shima Maheer bayanta yabi sai dai ganin ta sake cogewa alamar bazata shiga falon ba yaja hanunta. Ƙoƙarin amshewa take amma ya hana hakan sai da suka shige ya saketa. Kowa babu a falon sai uban ƙaurin abinci daya gaurayesa, ga falon a ɗan hargitse alamar dai yau bai samu gyara ba koma ba yau ɗin kawai ba. Anam ta yamutse fuska kamar mai tsantsami tana bi ko’ina da kallo a karo na farko dan waccan ranar batai ba.
“Ni kamar ƙaurin abinci nakeji fa?”.
Ya Maheer ya faɗa yana dubanta. Baki ta taɓe da kauda kanta batare data amsashi ba. Shima sai bai sake magana ba ya shiga ƙwala kiran sunan Fadwa a tunaninsa ko ta shiga wani uzirinne a ciki batasan abincin na ƙunewa ba. Kusan sau uku sannan ta fito daga hanyar bedroom hanunta rike da waya tana murmushi, da alama abu take dubawa da yake sakata nishaɗi………..✍
????????Wayyo Fady baby ya zaki bamu kunya haba selen mu so kike ƴan uba su sami na faɗa yau????. Koda yake munada bakin ramawa????
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
0913484810_ZAFAFA BIYAR_
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107 ko
ALLAH ya gafartama iyayenmu????????????
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
BABU SO.????????AREWABOOKS????????
15
……….Da kaurin abincin ta fara cin karo, dan haka ta kwasa da ɗan gudu zuwa kitchen tana faɗin, “Wayyo ni Fadwa yau ma yayi ƙauri”.
Daga Maheer har Anam da kallo kawai suka bita, Anam ta taɓe baki da neman kujera ta zauna. Ganin haka shima Maheer ɗin sai ya zauna yana ƴar dariya. “Tofa bama yau aka fara ƙonawaba kenan. Lallai Yaya an shigo abba tuwa ashe. Nikam gaskiya bazan iya haƙuri da mace bata kulamin da cikina ba”. Ya ƙare maganar yana tsare Anam da idanu.
Idanu ta ɗan waro da ɗage kafaɗarta baki a tabe alamar I don’t care, sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya. Ihun da Fadwa ta saki ya hanashi cewa komai ya mike da sauri ya nufi kitchen ɗin. Anam kam maimakon ta tashi sai ta ɗauka waya tana cigaba da dariyarta. A dai-dai nan shima ya shigo falon kasancewar Fharhan da Khaleel sun wuce office saboda sunada uziri. Buɗe ƙofar ta sakata rage dariyar da ɗan kallon ƙofar, sukaima juna kallon ido cikin ido. Nata ta fara janyewa saboda hango wani irin yanayi mai kama dajin zafinta a cikin nasa idanun, itakan ta rasa mitaima Yaya Shareff ya tsaneta a duniyar nan, idan dan tazo gidansa ne ya kwantar da hankalinsa wannan shine zai zame mata na ƙarshe insha ALLAH. Bata sake yarda ta kalla inda yake ba, sai dai har yanzu tanajin nasa idanun a kanta. Hakan ya sakata a matuƙar takura, sai dai kuma ta kasa motsawa balle ko yinƙurin barin wajen tayi….
Dariyar Maheer ta sakashi janye idanunsa a kanta ya juya garesa, sai yay karo da idanun Fadwa dake tsaye ƙyam a kansa tana masa kallo mai cike da tuhuma. Fuska ya sake tsukewa cikin basarwa ya maida hankalinsa wajen bin falon da kallo. Sosai ransa ya ƙara ɓaci fiye da wanda yake ciki tun ɗazun, duk gargaɗin da yay mata akan karya shigo ya sake ganin falon nan haka da datti batajiba kenan. Ya ɗan cije lip ɗinsa kawai batare da yace komaiba ya juya ya fita. Hakanne yasa Maheer bin bayansa shima. Anam ma mikewa tai, ta zabgama Fadwa dake binta da kallon wulaƙanci harara sannan ta fice tana jan ƙaramin tsaki.
Duk da kiran da Maheer yay mata batai niyyar binsu sashen Shareff ɗin ba. Sai dai ganin Fadwa na leƙenta ta window rai ɓace ya sata nufar can tana wani murmushi daya ƙawata fuskarta. A bakin ƙofa ta coge, Maheer ya juyo yana kallonta, cikin tsokana ya wulla mata ƙaramar harara. “Malama wa kikema aikin gadi zaki mana tsaye anan? Zoki zauna jareh”.
Murmushi kawai tayi itama, batare da tace komai ba ta zauna a kujerar kusa da shi tana satar kallon Shareff dake latsa waya kamar ma bai san da shigowar tata ba. Baki ta taɓe itama ta ɗauka tata wayar ta shiga latsawa. Ba’a rufa mintuna huɗu ba Fadwa ta shigo ɗauke da babban basket dake ɗauke da kuloli da duk abinda maicin abinci zai iya buƙata. Maheer ya miƙe ya karbeta yana dariya, cikin ƙasa da murya yace, “Badai mai ƙaurin zaki bamu ba?”. Harara ta ɗan sakar masa da kai masa ranƙwashi ya kauce, dining ya nufa domin ajiyewa, ita kuma ta nufi inda Shareff ke zaune har yanzu idonsa akan wayarsa. Zama tai kusa da shi tana mai rungumesa tare da manna masa kiss a kuncinsa. “I miss you my Soulmate”.
Maimakon amsa mata sai ya ɗago ya ɗan saci kallon Anam. A zahiri idonta akan waya yake, sai dai kunenta da hankalinta na tare da su….. “Wai har yanzu fushin kake?”. Fadwa ta faɗa cikin kunnensa hanunta ɗaya na cikin nasa ɗaya na shafo wuyansa zuwa gefen kunne. Hanunta dake kan wuyansa ya janye, a hankali yace, “Miye haka wai, muje ki bani abinci”. Bataso haka ba, sai taji inama ya biye mata kodan ta turama wannan yarinyar haushi. Amma ko yanzu ma bata ɓaci ba, tayi alwashin sai Anam ta daina zuwa mata gida har abada daga yau dalilin abinda ta shiryama ranta zatai mata. Cike da isa da yauƙi tabi bayan Shareff zuwa dining, dama shi Maheer tunda ya dire abinci yaja kujera ya zauna acan abinsa.
Cikin bada umarni Maheer yacema Anam ta taso suci abinci, ta ɗago tana girgiza masa kai alamar a’a. Hararta yayi, “Kinsan ALLAH idan na taso ɗaukarki zanyi kamar bab…..”
“You’re vary stupid!!”.
Ya faɗa cikin suɓutar baki idanunsa na wani irin ƙanƙancewa. Furucin da fusatar tasa ya saka Maheer haɗiye sauran abinda ke bakinsa. Anam da Fadwa kam gaba ɗayansu suka zuba masa ido dan yanda yay maganar a fusace duk sai da suka zabura. Waya yakeyi, wayar da kafin zancen Maheer yinta yake da murya can ƙasa dako Fadwa dake kusa da shi tana ƙoƙarin fara zuba masa abinci bajinsa take ba. Hannu takai da nufin taɓashi ya maka mata harara dole ta janye, sosai abun ya bama Anam dariya, tako yi gefe da kanta tanayi sai dai ƙasa-ƙasa. Maheer ya kalleta yana murmushi shima. Cokali ta ɗauka ta saka a cikin abincinsa babu ko ɗar ta kai baki, da sauri ta ɗiba tissue ta tufosa a ciki tana ambaton ya ALLAH. Shima dai Maheer yay cak ya kasa cigaba da tauna na bakinsa. Yayinda shima oga kwata-kwatan ya tufo nasa cikin tissue ɗin daya fisga yana kallon Fadwa rai a ɓace.
“Kinada hankali kuwa? Wannan gishirin fa!”.
Ɗan zabura Fadwa tai baya jikinta na tsuma. Ya sake jan tsaki da miƙewa zai bar wajen tai saurin riƙosa. A fusace ya juyo gareta sai dai saurin rungumesan da tayi ya sashi haɗiye kakkausan furucin da yay niyyar jifanta da shi. Jin bai tureta ba ta ɗago da sauri dan a gareta wannan damace da zata aiwatar da shirinta, babu zato kuwa babu tsammani ta haɗe bakinsa da nata. Da sauri Maheer yasa handkerchief ya rufe fuskarsa yana dariya…
Faɗuwar abu da tarwatsewarsa kan tiles tare da sakin siririyar ƙarar Anam ya sakashi saurin ture Fadwa yana jan numfashi da ƙarfi. Maheer ma da sauri ya janye handkerchief ɗin dake fuskarsa tare da haɗiye dariyarsa. Kusan a tare suka zabura kanta, sai dai Maheer ya rigashi kai hannu zai riƙo Anam, a ɗan fusace ya fisgo hanun Anam ɗin da Maheer ya kama ta dawo jikinsa, cak ya ɗagata daga dirƙuson da tai ya maida saman kujera, ƙafarta dake fidda jini ya ruƙo yana kaiwa tsugunne gaban kujerar, sai da ya rumtse ido sannan ya tsige yankin kwalbar cup data shigeta. Tako sake sakin ƙara jikinta na rawa dan har cikin ƙwaƙwalwarta taji cire glass ɗin. Handkerchief ɗin hanun Maheer ya fisga ya ɗaure mata ƙafar, sannan ya sake ɗaukarta cak yay waje da ita. Maheer da shima ke a rikice bin bayansu yay da sauri…..
Sosai zuciyar Fadwa ta kumburo cikin ƙirjinta tamkar zata fashe, itace ta tura kofin da hanunta ya faɗi lokacin da taga Anam zata miƙe a yanda ba kowa ya gani ba musamman ma Shareff data rungume. Tsabar yanayin da take ciki ko kwakwkwaran motsi ta gagarayi har tajiyo fitar motar mijinta. Hajijiyar da taji tana kwasartace ta sata saurin dafe kujerar dining…