BABU SO COMPLETE HAUSA NOVEL

Koda suka koma ɗaki Anam kwanciyarta tai tunda yau babu fita aiki, Aysha kam tai zaman lissafa kuɗinta dayin budget ɗinsu cike da farin ciki duk da dubu goma ne kawai. Barcinta da yay nisa ya saka har Yaya Shareff yabar gidan bata sani ba, koda Aysha ta fito masa rakkiya wajen mota dan da Fadwa zaije har airport cike da makirci Fadwan ke tambayar ina Anam. Aysha tace, “Barci take aunty ko’a taso ta?”. “A’a ki barta kawai kar’a tadata kanta yazo yana ciwo ko”. Duk yana jinsu, sai dai baice komai ba. Sai da Aysha taga fitar motar tasu sannan ta dawo itama ta kwanta dan barcinne a idonta.
A gidan su yaja kusan awa biyu, yay sallama da kowa sannan Khaleel ya ɗaukesa shi da Fadwa zuwa airport, basu wani jima suna jiraba jirgin da zai kaisa abuja ya keta hazo. Khaleel ya ɗakko Fadwa dake hawaye yana mata ƴar dariyar tsonar shagwaɓar tata. Ganin ya nufi hanyar maidata gidanta tace ita dai ya kaita can gidan zata ɗauka abu wajen Mommy, idan ma yanada wani uzirinne ya barta zata maida kanta gida kawai. Bai ƙiba ya canja hanaya.
Duk yanda Mommy da Fadwa suka so ayi maganar zaman Anam ɗin Gwaggo tace ba yau ba, ransu yaso fara ɓaci, sai dai Gwaggo ta nusar da su gaggawa ba tasu bace. Ita dai ta koma gidanta koda wasa karta nuna rashin son zaman Anam ɗin a gidan daga nan har zuwa sanda zata sanar musu abinda ta ƙulla. Fadwa bawani ta gamsu bane, dan haka batama gama sauraren Gwaggon ba ta figi handbag nata tai ficewarta. Duk da kallo suka bita, Gwaggo ta taɓe baki tana duban Mommy.
“Idan baki tashi tsaye akan wannan surukar taki ba to lallai ina tabbatar miki nan gaba kaɗan sai tasha kanki. Dan hatsabibiyar yarinyace da kanta kawai ta sani, halinta dana uwarta bashi da banbanci”.
Wani bahagon numfashi Mommy taja da ƙarfi tana duban Gwaggo tamkar mai son samo ƙarin bayani akan fuskarta, Gwaggo ta taɓe baki tana miƙewa. “Kinga ni jeki kafin mijinki da shi bai rabo da zargi yasan kina nan, nima kwanciya zan ɗanyi barci bai isheni ba jiya da dare”. Da kallo kawai Mommy ke binta hartai shigewarta bedroom. Itama tashin tai cike da rashin zaɓi ta fito dan tasan Gwaggon tayi hakane dan gujema kowace irin tambaya daga gareta.
Gwaggo dake laɓe jikin ƙofa tana leƙen Mommy ta taɓe baki, cikin ƙara yamutse fuskarta da tsufa ya gama nuna kansa tai murmushi mai cike da ma’anoni masu yawa da fahimtarta sai dai ALLAH.
(Mi tsohuwar ga ke ƙullawa ne?????????)
★ A ɓangaren Fadwa kam maimakon gidanta sai ta nufi gidansu, dan ranta gaba ɗaya a mugun ɓace yake, ta tabbatar idan ta koma gidanta a haka tofa tanayin sallama jibgar Anam ce zata biyo bayanta. Mamah (Gwaggo Halima) batai mamakin ganinta ba, saboda babu jimawa suka gama magana da Gwaggo a waya, sai dai su dukansu babu wanda yay tunanin nan Fadwa ɗin ta taho. Hasalima kiranta take son yi sai gata. Kuka ta fashema Mamah da shi, dan haka ta tsaya tana kallonta kawai.
“Wlhy Mamah sai dai na dawo nan da zama inhar akace sai ta zauna min gida. Ai dama tun farko haka mukai da shi zan zo nan na zauna har sai ya dawo, amma yana zuwa can gidan aka canja masa tunani, ni na gane Mommy da Gwaggo duk bakinsu ɗay…..”
“K bana son shashanci, ke ko Fadwa wai sai yaushe ne zakiyi hankali ne? Idan an faɗa miki ki dinga saurara..”
“Mamah dan baki san abinda ke faruwa bane fa, baƙar yarinyar can ɗiyar wancan mutumin na Malaysia fa aka kawo wai su tayani zama gida ita da Aysha. Na nuna masa ban yarda ba yana neman min azaba da masifarsa. Na faɗama Mommy amma Gwaggo ta nuna wai tanada shiri. Wane shiri gareta? Na fahimci tsohuwar nan bata sona kawai yanzun…”
“Fadwa!!”
Mamah ta katseta a tsawace. …….✍????
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS????????????????????????
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA????
09134848107
[11/25, 10:30 AM] Hajiya Qarama: Typing????
*_❤????BABU SO....!!❤????_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
BABU SO????????AREWABOOKS
24
……….Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu mintuna kamar kowa bazaice komai ba, kusan mintuna uku Amal ta nisa. Cikin ɗan ɗari-ɗari ta fara magana. “Ni dai a nawa nazarin da hange sai naga kamar cikin nan shine matsalarki. Kin san fa wasu mazan basu son da anyi aure ace ciki ɗin nan. Kigafa yanda Shareff ke sonki amma ace haka na faruwa tsakaninku wata baifi uku ba da aure, amma dai bamu san zuciyarsa ba kuma”.
Ta ƙare maganar da ɗan shafo gefen wuyanta ganin yanda suka tsura mata idanu su duka. Yanzu ma kamar bazasu ce komai ba, harta fara tsarguwa sai Siyyah ta katse fargabarta.
“Kuma fa maganar Amal kamar tana a kan hanya. Musamman idan mukai dubi da yanayin mijinki. Anya kuwa cikin nan bashine matsalar ba…”
Nufashi Fadwa taja da ƙarfi, zuciyarta babu abinda take hasaso mata sai yanayin Shareff a randa Dr Jamal ya tabbatar musu tana da ciki, ƙanensa da iyayensu kowa na murna amma shi bataga ko murmushinsa ba, da suka dawo gida ma baice mata komai game da cikin ba amma yana bata kulawa da duk take buƙata. Kenan in dai maganar ƙawayenta gaskiya ne kulawar yana bata ne kawai domin kar ace baya farin ciki? Ya ALLAH itako yaya akai ta kasa ganewa sai yanz………
Sima ce ta katse tunaninta da faɗin, “Fady nima dai ina ganin maganar su Amal nakan hanya gaskiya, dan na tabbatar badan cikin nan ba maybe ma tare da ke zai wuce ku ɗanyi honeymoon ɗinku. Amma gashi ciki ya muku cikas dole yayta maida allura galma a tsakaninku, ta hakanne kuma wannan yarinyar zata samu damar cika burinta akansa. A yanzu ma ɗaukar ciki duk ta wajigaki miji na gudunki inaga kin haihu, wlhy yara haukataki zasuyi ki fita hayyacinki. Baki ga miji hatta da followers naki sai sun gudu, dama kece mai kankaro mana mutunci saboda a yanzu kina cikin manyan tiktokers dake lokaci da kuma tarin followers a arewacin Nigeria, sunanki ya riga yayi zarra, da kin saki video tamkar wuta jaje haka yake danne duk wani posting, kiyi tunani”.
Da ƙyar ta iya haɗiye hawayen da suka ciko mata ido saboda maganganunsu sun matuƙar shigarta. Ta sake nisawa cikin ɗacin zuciya batare data kallesu ba. “Naji duk bayanan ku, sai dai ban san yaya kuke so nayi da cikin ba tunda ya riga ya shiga jikina, tun kafin faruwar haka ya kamata na ɗau mataki, amma a yanzu na riga nayi latti..”
“Bakiyi latti ba Fady, har yanzu kina da sauran dama”.
Ido ta tsirawa Bibah da tai maganar. Bibah ta jin jina mata kai da cigaba da faɗin, “Da gaske bakiyi latti ba, kwata-kwata cikin ana maganar ko wata biyu bai cika ba, ki zubar da shi kawai, hakan zai baki damar sasantawa da mijinki tare da fatattakar shegiyar yarinyar can a rayuwarsa. Idan ya fara nuna son ƴaƴan da kansa sai ki bama cikin damar shiga hankalinki kwance”.
Sosai maganar ta doki ƙirjin Anam dake saurarensu ta jikin window, dan a inda take zaune windown ɗakin Fadwa ne, tun kuma shigarsu ɗakin tana iya jiyo tattaunawarsu, sai dai da farko bata maida hankali ba sai da Amal ta fara danganta ciki da matsalar Fadwa. Duk da bata son Fadwa addu’a take a ranta kada ta ɗauki shawarar su Sima…….. Ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunani, Mamie ce, hakan ya sata mikewa a wajen tilas tana amsa kiran dan video call ne…..